← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 143

Sashe 108

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da a rufe take zai iya ballata. Hurriya dake tsaye a dinning rike da plate ta juyo cikin tsoro ta kalli kofar falon, domin yadda ya turo kofar falon ya shigo ya firgitata even though bata san waye ba har sai da ta kalli kofar. Kai tsaye ya nufeta daman zuwan domin ita ne! Waye Adam.....! Ta daga kai ta dubeshi gaba daya muryarsa ta cika dodon kunnenta ta cika falon tsayen da yayi a gabanta kuma ya cika duniyar idonta. Sai tsaya baya da sauri at that time ne ya fisge plate din hannunta ya bugashi a kasa. Waye Adam....!! Ta yunkura zata ranta ana kare, ya rikota kamar wata bulala haka ya jujjuyata ya jefar a gefen kujera ta fadi kasa tana kwala ihu. Subhanallahi? Captain Lafiya? Amadadin ya amsawa Momy dake saukowa tana tambayarsa tare da Namra sai ya nufi gurin da Hurriya take kwance ya mikar da ita tsaye ya dauketa mari. Waye Adam? Ta kai hannu zata taba fuskar ya wanke mata fuska ta dayan gefen sai ta fasa taba fuskar yawu da jini suka gangaro mata lokaci daya, yadda yake daka mata tsawa gurin tambayarta da kuma marin da yayi mata a yanzu ya mantar da ita Adam, domin ta dade ta tattara lamarinsa ta aje a gefe daya tun da dadewa. Momy ta iso da sauri ta rika Captain ta matsar da shi gefe ta kalli Hurriya. Me kika masa? Hurriya kallon Momy ta yi ta fashe da kuka domin ba zata iya fadar abun da ta yi ba, tambayarta yake wanda bata sani ba. At that time ne Captain ya samu damar runtse ido ya bude ya zauna a kujera ya kasa cewa komai, zuciyarsa na masa wani irin bala'in zafi. Wai me ya faru ne can anyone explain? Momy ta tambaya a tsawace tana kallon Captain kamin ta juyo gurin Hurriya. Me kika yi? Hurriya ta girgiza kai. Captain ya dago daker ta danna wutae da yake ji ya kalli Momy yana nuna Hurriya. Waye saurayin yarinyar nan Momy? Momy ta daga kafadunta. I don't know, waye saurayinki? Miye matsalarka da saurayinta? What's going on here? Ba ni da saurayi Wallahi Allah Hurriya ta amsa cikin kuka, Captain ya daka mata tsawa. Karya kike yi waye Adam? Namra dake saukowa stairs ta amsa masa. Adam Sarauta? Wanda yayi miki ruwan kudi a birthday Khairy ina tunanin shi yake nufi Captain ya kalli Namra yana kara tabbatar da zancen da Adam din ya fada masa cewar a birthday yayarta suka hadu. Ba sarauyina ba ne.... Ta amsa cikin kuka bakinta na mata mugun ciwo yana zubar da jini, kana ta kai hannu ta rike rigar Momy ganin Salim ya shigo cikin falon sai zuciyarta ta raya mata taruwa za su yi su duketa. Momy ta juyo ta kalli Salim Namra ma da mamaki take kallom yadda ya shigo falon dake bude babu sallama babu neman izini, hakan kuma yana karantar da ita akwai abun da yake faruwa. Ita ma ka fasa mata baki ko Captain? Wai duk na minene? My mind is telling me son yarinyar nan kake a boye Captain? Is that the reason da yasa idan na yi maka maganarta kake fushin dina away? Ba abun kunya ba ne a gareki ka yi soyayya da yarinyar da ni na fara? You betrayed me Captain.... Salim ya juya gurin Hurriya dake tsaye ya kalleta. Thank you da kika rufe kofafin soyayyarki a gareni, na gode da baki ba ni damar dandana bakinciki da yanzu ya zame min abun kunya ba, ashe kin san tarayya kike da cousin dina Adam shiyasa baki karbi soyayya ta ba, tir da ke babu uban da zai so mace mai two face irinki green snake under green grass, kowa ya san wacece ke yanzu Duk wata kalma da Salim ya fadawa Captain be dago ya kalleshi ba har sai da ya kai ga taba Hurriya. At that time Captain ya kalleshi sai kuma ya daga kansa sama ya kyalkyale da dariya ya daga kafarsa sama ya buga a kasa. Hahahahaha Salim.. Haba Salim.... Ya sauke kan ya kalli Salim kamar bakin maciji da ke shirin yin sara. In less than second Captain ya mike tsaye ya cire bindigar jikinsa ya taka ta isa gurin Salim ta dora masa bindigar a kasan makoshi ya daga kansa kasa. One bad word for her, sai na tashi kanka sai dai ni ma a kashe ni, and you know i can do it... Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Namra ta dora hannu akai, Momy kuma ta fashe da kuka ta nufi Captain ta rike shi ta ja shi baya, tsoro take ayi kisan kai a gidanta. Ba ni ba kai Jamal daga yau... Kuma duk wani abun da yake da alaka da kai na datseshi daga yau ba nan nigeria ba har wanda yake Ethiopia... What are you waiting for? Captain ya furta a kakkausar muryar as his responsed ga Salim. Salim ya kalli Namra ya kalli Captain yayi murmushi sannan ya fice daga falon. Na rasa gane me yake faruwa? Me kika aikata wai? Hurriya na jin tambayar da ta fito daga bakin Momy ta san fadan gurinta zai dawo, sai ta juya zata bar gurin Captain ya ware kafarsa yaja yayi hanzarin rikota ya jefar da ita kan kujera. Ban aikata komai ba Wallahi ni ban yi soyayya da Adam ba... Captain ya ciro wayarsa ya kunna data ta sauke hotunan da Salim ya turo masa ya jefawa Hurriya wayar. Hurriya ta dauki wayar da sauri ta duba, duban da take da ma ace idonta ya rufe gaba daya bata ga komai ba, wani tashin hankali da gurbacewar rayuwa a hango a cikin wayar, idanuwanta suka yi arba da makwafin mutuwarta, da gaske ita ce din ko mai kama da ita? Adam take gani Adam din da ya zame mata fitina a rayuwarta, yaushe ta dauki hoto da shi? A ina? Da yaushe? A lailai a yau ta gane wani garin ya fi gaban kuku, domin kuka ko kadan be kusanto idonta ba hawayen da yake ma a yanzu sai suka tsaya cak.... Tun tana ganin hotuna daidai har suka koma mata biyu ta gizon yayi yawa suka rabu gida uku, ta dago kai sai ido ya mamaye ilahirin idanuwanta bata iya jin sautin komai saboda an dauke jinta a lokacin, wayar dake hannunta ce ta fara faduwa kasa sannan jikinta ya bi baya, daga Momy har Namra da Captain suna kallonta har ta jikinta ya kai kasa kanta ya bugu numfashi yayo halinsa, aka rasa mai riketa. Momy ta karasa ta dauki wayar ta duba Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Shi ne abun da ya fito daga bakinta tana rufe ido, Namra ta karaso gurin da sauri ta karbi wayar ta duba, bata gama ta tantancewa ba Captain ya karbe wayar a hannun Namra, ya duka ya kai yatsansa biyu ya taba wuyan Huriyy, sannan ya dago I will be very happy idan na samu babu hannun kowa a cikin nan Momy ta dauke shi da wani kallo. Baka ma yarda ta aikata ba kenan? Kuma idan sheri aka yi mata mu kake zargin mun aikata mata right? Wutar data halba a zuciyata ba zata bar ni na yarda ta aikata hakan ba, kuma kowa abun zargi ne a gurina because kowa yana da target dinsa akan Hurriya, and the innocent soul a saw in her ba zata aikata ba, akwai wanda ya shirya wannan abun.. Kuma wani nan kanwar ubanka ce uwa daya uba daya ko? Ya dafe kansa. Momy please... Kamar wanda magana ta karewa a baki haka ya yanke kalamansa ya kasa kara wani furucin ya fice daga falon. Momy ta juyo ta kalli Namra cikin tsananin takaici da bacin. Wai ni Captain zai zarga? Namra ta duka ta taba Hurriya dake kwance a suma kamar gawa tana fadin. Kamin mu yi tunanin abun da Captain yayi mu kai yarinyar nan asibiti bata motsi fa Ke da kika ji zaki iya sai ki yi, ni ko mutuwa ta yi a yanzu Alhamdulillah, zamanta a nan be kara mjn komai ba sai bakinciki da damuwa, dramer queen Momy ta saka kafa ta take ta wuce Hurriya ta haye sama, Namra ta bita da kallo kamin ta kalli Hurriya hankalinta a tashe. Da gudu ta nufi kitchen ta kunna tap ta dauki roba ta zubo ruwa ta zo ta zubawa Hurriya ta girgiza ta amman shiru. Hurriya Hurriya... Ta kara mata ruwan ta sake girgiza ta nan ma shiru, tsoron kar ta mutu a gurin ya saka ta tashi da gudu ta fice daga bangaren Momy zuwa bangaren Hajiya Kaltume, and abun mamaki ta isa gurin a daidai lokacin da Khairy take nunawa Ruma hoton Hurriya. Ba sai kin fada mana ba, mu ma mun gani video ta is all over the internet... Ba wannan ya kawo ni ba Namra ta kawar ma Khairy kai ta nufi stairs tana kiran sunan Yasir domin ta san shi kadai zai iya taimaka mata a yanzu. Ya Yasir ya fita Yaya Namra Ta juyo ta sauko da sauri. Dan Allah zo ki kama min Hurriya mu kaita asibiti kar ta mutu, faduwa ta yi kuma bata motsi Ruma ta mikawa Khairy wayar da sauri ta bi bayan Namra suka fice a falon cikin tsananin tashin hankali. Khairy ta bi su da kallo then ta maida idonta kasa tana kallon wayarta dake hannunta. Contact dinta ta shiga ta yi dialing number Adam sai kuma ta yi saurin yanke kiran ta fadi zaune kan kujera kamar mai mamaki. CAPTAIN JAMAL POV. Wasu hotuna zan turo maka yanzu, ina son ka yi aiki mai kyau akansu ka gano min idan editing aka yi, kuma ina son ka bincika a ina aka dauki hoto nan kuma ka gano ne waya watsa hotunan a media Okay Sir Ya sauke wayar daga kunnensa ya shiga Whatsapp ya aika masa da hoton sannan ya goge su a wayarsa, ya saka wayar aljihu ya nufi gaban teburinsa ya dafa teburin ya rumtse ido.... Zuuuuuu zuuuuu wayarsa dake aljihunsa ta yi vibration alamar kira, ba tare da ya bude idon ba ya saka hannunsa aljihun ya ciro wayar, bude idonsa ya kalli wayar shi ne abu na biyu da yayi sannan ya
Chapter 108 · 0% Book details