Sashe 15
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ruwan hawayen da a da su kwana a idonta. Kanwarta Rukayya ta bata fuska sosai kamar ta fasa kuka. Amma da baki nan gidan babu dadi, kuma Appa ya kwashe kayanki daga gidan Na sani, ya aiko min da su nan ai, suna nan a zuba a gareji, wasu an saka a falon waje Hurriya ta dago tana kuka ta kalli Amma. Ba zaki dawo ba kenan? Khairi ta fada min Appa ya rabu dake? Na fada miki tun ranar ai, abincina ya kare a gidanku, ina Hamad Amma na rufe baki Hamad ya karaso gurin kofar sai ya tsaya yana kallonsu kamar wani bako. Hamad shigo mana ya ka tsaya a jikin kofa Rukayya ta fada, sai ya nufo cikin dakin yana jin wani irin tausayin mahaifiyarsa da ya kasa nunawa a fuskarsa, sai dai sanin halinsa da Amma ta yi ya saka ta fahimci akwai damuwa a tare da danta domin fuskarta babu walwala kuma ba hade rai yayi ba alamar fushi, yana a wani yanayi ne da ita kadai take gane damuwarsa. Hamad kuna nan kuna ta fadan ko? Ba mu yi fada ba, ba mu yi fada ba Amma, amman dai gidan babu dadi... Dorawa ta yi da labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan ciki har da komawarsu bangaren Momy da suka yi. Daman gidan ko da ina ciki ya kuke zaune balle bana nan, sai dai ku yi ta hakuri karku saka komai ranku Ni dai na ce Bappanku ya tafi gurinsa yayi magana da shi, yaran nan ya bar su zauna a gidan nan idan ba haka ba, wannan matan uban na su za su iya saka musu guba su mutu ma Cewar Gwaggo a lokacin da take kokarin shigowa dakin. Sai Amma ta amsa mata tana hawaye. Allah ya fi su Gwaggo, na san Allah baya bachi kuma baya son zalinci, zai kare su, amman abu ne mai wahala Alhaji ya yarda yaran nan su zauna a gidan nan Amma me yasa Appa ya sake ki? Hamad ya tambaya kai tsaye yana tsare ta da ido. Ban sani ba Hamad, Wallahi ban sani ba, da ace na san laifin da na yi masa wata kila da zan fi jin sanyi fiye da yadda nake ji a yanzu, shi kan shi ya ce ban masa laifin komai ba Saboda Hajiya ne? Ko Kuma Momy Amma ta kama hannunsa ta rike Ba saboda kowa ba ne, kar kaje ka yi ta fada da mutane wahala zaka sha a gidan nan, dan Allah ka zauna lafiya da kowa Hamad wannan fushin da saurin kai hannu ka daina, ku kenan Allah ya ba ni sai wannan idan na haifa, ban sani ba ko zan kara wani ko kuma iyaka kenan, dan Allah ku hada kanku ku zauna lafiya, ina gidan nan amman tunanina yana can tare da ku saboda na san yadda kuke yawan samu tsabani da juna, ba ku mai raba ku a yanzu idan kuka yi fada ma dadi za su ji Be ci abinci Amma tun da kika bar gidan nan, da safe ma tea kawai ya sha Amma ta dauke idonta daga barin kallon Hurriya dake fada mata ta kalli Hamad. Saboda me? So kake ka jawa kanka wani ciwo kuma? Kamar an zunguro idonsa haka ya fara hawaye yana kallon mahaifiyarsa, duk yadda ta so ta daure sai ta kasa ita sai da kukan ya ci karfinta balle Hurriya da ke da raunin zuciya. Rukaiyah ta share hawayenta. Kai Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Wallahi idan raba ku aka yi an ci amanarki an ci amanar yaran nan, mu ma kuma anci amanarmu an daga mana hankali Gwaggo ta girgiza kai cike da tausayawa. Toh Allah ya kyauta, arzikinsu ma suna da wayo da ace kanane ai da sai sun fi shan wahala, kuma ubansu yana sonsu za su samu sauki ta wani bangaren A gidan suka wuni har dare, abincin da Hamad ya kasa ci a gidan Ubansa sai gashi ya ci a gidan kakarsa kasancewar Amma ce ta dafa masa da kanta, kuma ta saka shi gaba ya zauna ta cinye abincin tass ya dora da lemu, tukuna hira ta biyo baya, sai da dare yayi misalin tara da rabi sannan Yasir ya zo daukarsu daman ya fada musu a lokacin da direba zai kawo su cewar shi zai dauko su. Nasiha sosai Amma ta yi musu sannan ta aika Hamad ya shigo da Yasir ya zauna saman kujerar karamin falon suka gaisa. Yasir ga kanenka nan, na san kana kokari amman Dan Allah a kara, a rika ja musu kunne idan suka yi ba daidai ba, kuma a rika duba su dan Allah Amma dan Allah ki daina wannan maganar, ko minene Allah ya kawar da shi ya kawo maslaha ki dawo gidan kamar yadda aka saba Toh Ameen, duk da haka dai a kula da su musamman Hamad In Shaa Allah Allah ya taimaka ko a kawo maka abinci Aa idan na koma gida zan ci, yau Rukayya bata gidan Tana ciki karatu take yi kasan idan suka samu littafan nan na hausa basa son tashi, yanzu haka bata ma san ka shigo, bari a kirata ku gaisa No kyaleta Amma, a gaisheta dai, bamu mu tafi kar dare ya kara yi Yana rufe baki wayarsa ta bude nata ta fara kuka, hannu ya saka aljihu ya ciro wayar ya duba ganin mai kira ya saka ya amsa da sauri. Hello Appa Yasir Hurriya bata dawo ba? Gasu na zo dauko su Sai yanzu? Kasan bana son ana kaiwa dare a waje ko? Me yasa direba be je dauko su tun wuri ba? Affuwan Appa, laifina ne ni nace zan dauko su kuma yanzu haka ina gidan To ku dawo yanzu nan, karka sake yaran nan su ce zasu kwana a nan In Shaa Allah, yanzu zamu taso Sai kun iso.....ka gaishe da Mamansu Ya fada daga karshe bayan yaja dogon numfashi, da mamaki Yasir ya amsa masa da toh sannan ya sauke wayar. Appa ne, ya ce na gaishe ki Wani irin faduwa gaban Amma yayi, mutumen da ya sake ta ya kwaso kayanta ya yace a kawo mata kuma shi zai ce a gaisheta. Ina amsawa Mikewa yayi tsaye yayi mata sallama Hamad da Hurriya suka bi bayansa, Amma kasa raka su ta yi har suka fice daga gidan. Daga gidan Gwaggo Yasir be tsaya ko'ina ba sai gidansu ya faka a bangaren Hajiya Kaltume, Hamad ya riga fitowa motar s annan Hurriya, Yasir kuma ya tsaya gyara parking din. Me yasa baki fadawa Amma na fasa miki gilashi ba? A jere suke suna tafiya Hamad ya tambayeta domin abun da ya tsaya masa a rai kenan tun a lokacin da ta boyewa Amma cewar sun yi fada. Idan ta ji zata ji ba dadi ba, baka ji tana cewa mu zauna lafiya ba? Idan kana yin fada ran Amma zai bace Ni dai bana son Hajiya bana son Momy bana son kowa a gidan nan Yana fada yana wani cin magani kamar wani babban saurayi, Hurriya ta tsaya kallonsa da mamakin furunci, shi kam tuni ya juya ya fasa shiga bangaren Hajiya Kaltume ma ya nufi na su bangaren duk kuwa da ya san Amma bata gidan. Hurriya ta cigaba da tafiya har ta isa bakin kofar falom ta muda kofar ta shiga da sallama farin gilashin dake kara mata kyau yana fuskarta. Wa'alaikassalam Fadeel ya amsa mata yana zaune daga gefen kujera yana gwada kiran Hajiya Fatee. Ni yanzu hankalina ya tashi sosai, ace har karfe goma Hajiya bata dawo ba? Ga wayarta baya shiga, daman tun da Ruma ta dawo makaranta take ta damu na da ina Hajiya Cewar Maama tana gwada kiran Hajiya Kaltume. Amman fa ce mana ta yi gurin Hajiya Fatee zata je Fadeel ya ce Bata gidan, domin daga can na fito masu aikin suka ce min tare suka fita da Hajiya, shiyasa na zo nan ko tana nan domin wayarta har yanzu bata shiga Yasir ne ya shigo falon yana motsa keys din dake hannunsa. Hurriya ke da Hamad Appa yace na kira ku, Ina Hajiya? Ya karashe zancen yana kallon Maama da hankalinta ya tashi sosai kamin ya karasa ya mikawa Fadeel hannu su gaisa. Ita muke ta nema? Ban gane ita kuke nema ba? Tambayar Fadeel dake fadar haka yake da mamaki. Dazu na shiga na gaishe da Hajiya aka ce sun fita tare da Hajiyarka, yanzu kuma na dawo masu aikin suka ce min bata nan, na gwada kiran wayarta kuma ba a samu shiyasa na zo nan ko zan sameta sai kuma na tarar nan din ma kanenka neman Hajiyarka suke Wai tun fitar da ta yi da safe bata dawo ba? I thought ta dawo ba fa, yanzu ma Appa ne ya ce a kirata Maama da tuni ido ya raina fata ta fara kuka ta ce. Wallahi bata dawo ba har yanzu, ni hankalina ya tashi Subhanallahi, to ina ta ce zata je? Maama da Salma suka amsa masa, duk abun da ake Hurriya da ido kawai take binsu, Fadeel kuma yana jefa mata kallo time to time, farar fatarsa sai daukar masa hankali take kasancewarsa baki, ba shi kadai ba har Yasir da duka yan matan Hajiya Kaltume babu fari ko daya, sai wanda ya dara wani baki, domin an yi gadon bakar fata ta uwa ta uba, kamar yadda shi ma yake baki sai dai nasa bakin mai kyau ne irin mai shaike da ya dace da fatarsa ya karawa hancinsa fa fararen hakoransa da idanuwa kyau. Hurriya ta mike tsaye ta nufi kofa domin amsa kiran mahaifinta Fadeel ya bita da ido yana kallonta kasa kasa har ta fice, ba wannan ne karon farko da ya fara ganinta ba, amman a yau ta tafi da shi, domin ta kure iyakar ganinsa ta cika idonsa. *** *** *** Wasa-wasa aka nemi Hajiya Kaltume aka rasa babu amo babu labari, duk inda ake saka ran za'a gane an bincika bata nan, haka ma Aminiyarta Hajiya Fatee ita ta bangaren danta Fadeel babu inda be bincika ba amman be same ta ba, gashi be san direban da ya daukesu ba balle ya neme su, wayoyinsu kuma idan an kira ba mai