← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 143

Sashe 122

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yarinyar nan ta yi? Bata aikata ba sheri aka yi mata, kuma asiri zai tonu nan ba da jimawa ba, kowa be wuce kaddara ba hakan zai iya faruwa da ni, ko da wani a cikin jikokinki sheri ne aka yi mata saboda a lalata sunanta Haka ne, abun kam babu dadin ji babu dadin fadi, amman na tausaya mata matuka Captain ya daga hannayensa sama fafaren hakoransa na bayyana yayi ma Allah godiya. Allah ka ba ni ikon kyautata ma yarinyar da daukar nauyinta yadda ya dace, ka ba ni ikon faranta mata, ka taimaka min gurin tarbiyarta da na yaran da zamu haifa Allah, ya Allah ka karkato da zuciyar mahaifiyata da hankalinta ta fahimce kuma ta so abun da nake so, Allah ya ba mu zaman lafiya ka kawar da shaidan da mahassada a wannan aure Ameen Nene ta amsa masa tana kallonsa cike da burgewa. Kana da hankali matuka Jamal, ba dan kana jikana ba hakika wannan yarinyar ta yi dacen miji, matukar ba zata fusata ka ba to zaku zauna lafiya da ita In shaa Allah Nene Ya kara taka mata rawar sai a lokacin yake jin wani kalar farin ciki da be san a muhalin da zai aje shi ba, a lokacin ne wani shaukin auren da annashuwa da zumudi suka same shi. Hanyar da dakinsa yake ya nufa yana tafe yana gyara babbar rigar abun ka da wanda be saba saka manya kaya irin wannan ba. Agaban madubi ya zauna yana shafa fuskarsa ya dauki ragowar tutaren ya feshe a jikinsa, wani irin yanayi yake jin kansa da be taba samun kansa a ciki ba, yanayi ne dabam da yake zuwa sau daya a rayuwar ko wane saurayi fa budurwa, yanayin da kan canja yanayin ango da Amarya tun daga yanayin gari har zuwa na hallita da mu'amala da kuma na iskar da aka shaka. Hoton da ya dauka na Hurriya ya kama a wayarsa yana kallo yana shafa screen din da hannunsa. You're the only thing i want touch.... Kin kawo ni a wata duniya da ban yi mafarkin zuwanta a kusa ba, kin haska min abubuwa da yawa da duhun watan soyayyarki bata bari na gani ba, zan baki kyauta duniyar dake cike da haske da farinciki sai na dawo miki da abubuwan da kika rasa, bakinciki da kike ciki zan maye miki gurbinsa da farinciki, zan canja shafin rayuwarki har ki bata damuwa baya, zaki gode Allah ki yi alfahari da ya baki ni a matsayin miji.... QURRATUL AYN (meaning Delights Of The Eye, Darling, sanyin idaniya...) Ya sumbanci hoton sannan ya dorashi a kirjinsa ya rumgume ya lumshe ido yana murmushi, a zuciyarsa yake ayyana Hurriya tsaye a gabansa tana kallonsa da murmushi a fuskarsa fararen tufafi sanye a jikinta. Ya... Ya... Ya... Na.. Ya ji yana fitowa between her soft lips tana motsa halshenta a hankali. Uhmmm..... Ya bude ido yana amsawa, a nan ya gane imagination ne yake ba gaskiya ba, murmushi yayi mai sauti ya cige bakinsa ya maida idonsa ya rufe yana jin kamar ace yana da damar ganin Hurriya a yanzu. HAJIYA KALTUME POV. Hurriya fa ka ce Yasir ko dai zolayata kake? Taya zan zolaye ki Hajiya? Ga abun da yake zahiri, goro da dabino suna waje, idan baki yarda ba ki tambayi Appa ki ji Hajiya Kaltume ta juyo ta kalli Khairy da ke kallon sarkar kamar wanda ta yi arba da wani abun tashin hankali. Da wannan sarkar aka biya sadakin Hurriya? Wanene? Be san abun da yake yawo a gari ba ne Yaya? Ba za su rasa sani ba, wata kila ma shi ne dalilin da yasa suka zo neman auren a yanzu, kuma zai iya yiyu ba su sani ba din ko ma dai minene an riga da an daura fatan mu Allah ya bada zama lafiya Ya karasa yama dauko wayarsa daya dake aljihu ya amsa kiran Appa. Hello Appa... Eh tana hannuna okay gani nan zuwa Ya mike tsaye ya rufe sarkar. Appa yake kirana, yace ma kawo masa sarkar Ya nufi kofa, Hajiya da Khairy suka bi shi da kallo kamar wasu kauyawa. Hajiya Kaltume ta kalli Khairy Anya Nafisa ta sani kuwa? Sadaki da sarkar zinari? Abun kamar hankali ba zai dauka ba Hajiya, duk wannan cecekucen da ake akan Hurriya ace wani ya zo ya aureta a rana daya kuma ya biya sadaki mai yawa haka? To ni ma mamakin abun nake, abun dai kamar a mafarki Kuma Wallahi idan wanda nake zargi ne dan Alhaji Turaki Hurriya ta warke Hajiya, kin san yan'uwan Momy babu talaka balle kuma AA Turaki Shin waye be san ubansa a kasar nan ba? Wai ko mafarki na ke dai Ta mari kanta baren dama ta koma hagu ta mari kanta ya mursa idonta ta hade yawu. Kuma fa ta makance kuma ya yarda zai aureta ko dai asiri aka masa? Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta dauki dankwalinta a hannu, ta nufi sama. A gurin da wayarta take aje ta dauka ta kira number Hajiya Fatee. Sallamu Alaikum Ba sai na amsa sallamarki ba balle gaisuwa, Hajiya Fatee duniyar nan fa tana shirin rikice min, wai ashe motocin da kika gani dazun sun shiga bangaren Nafisa neman auren Hurriya aka zo? Hurriya? Ko dai Namra? Hurriya dai da kika sani yar wajen Iyami... Kuma Alhaji ya ba su ba su bar gidan ba sai da aka daura auren Ina na taba jin abu haka? A bada aure kuma a daura a take? Anya mutanen kwarai ne kuwa ko da yake Mahaifinta yana neman a raba shi da abun kunya ba dole ya amince ba Ba auren ne abun mamaki ba, wanda ta aura ne da kuma wanda ya zo nemam auren ne abun mamaki Toh... Wata kila dan fashi ne ko ko kuma masu yankan kai, domin su ne kadai za su iya runtse ido su auri Hurriya a yanzu, ganin manyan motoci ba shi ke nuna mai daraja zata aura ba wata kila ma ba zai wuce mai sharar gidan masu arziki, ya walkilta mai gidansa nema masa aurenta Alhaji Aliyu Turaki ne fa Hajiya Fatee, Yayan Nafisa, ya zo neman aurenta. Oh... To... Wata kila yaron gidansa ya yi ma kara ko kuma ubanta ya nemo mai raba shi da abun kunya ayi hadaka, ke waya sani ma ko tsoho ne za a hada ta saboda su basa kunyar auren ko wace mace Sugar daddys din nan da kike ji da gani Wannan saurayi ne sabo dal a cikin kwali, an Alhaji Aliyu Turaki ne wanda yake zuwa gurin Nafisa, ina kare miki zance da zinari aka yi sadakinta na naira na gugar naira har naira miliyan hansi.... Hajiya Fatee ta amsa da karfi. Ke.... Hajiya Kaltume... Hurriyar? Har kin sa cikina ya murda Ai ni fitsari kubce min suka yi, yar Iyami? Sauran yaran gida ba a musu ba sai ita da duniya ta gama wulakantawa? Zama be gan ni ba Hajiya Fatee wannan yakin ba na uwar Hurriya kadai ba ne har da Hurriya, Wallahi ba zan yarda ta fi yayana more rayuwa ba, bayan duk abun da uwarta ta yi min? Ta aure min miji ta zo ta yi miki a gidana yanzu kuma ta tafi yarta zata taka nairar da ta fi ta ubanta, yar mai aiki? Uwarta ta mallake min miji ta yi yadda take so ita kuma yanzu ta take mu koma karkashin inuwar ta muna daga kai mu nunata? Ke ni fa wani abun ma mamaki yake ba ni, anya zuri'arsu suna barin namiji a banza kuwa? Idan yaron be da hankali kuma iyayensa sai suka yarda? Ko da ba yaron kwarai ba ne? Captain ne fa na Soja, Nafisa ma jinsa take ballw iyayensa, kuma ko bayan haka idan ta aure shi ai ta take, nan gaba sai a fara lissafi da ita a cikin yara kanana masu arziki, Hajiya Fatee bana son Iyami bana son zuri'arta dan haka bana fatan wani abun farinciki ya same su To yanzu me ye abun yi? Abun yi ki shirya gobe a gidanki zan yi karin kumallo, mu kama hanyar kauyen nan muje mu samu malamin nan da kanmu, idan be fara aiki ba ya tada idan kuma ya riga da ya fara a kara fetur hayaki ya baibaiye ko'ina a rikita Iyami da iyalinta a karkato da hankalin mijina gareni Amman fa ina tsoron kauyen nan Hajiya Kaltume kin san fa irin wahalar da muka sha wacan karon, mussamman ma ni da kanana yara suka haikewa har da guziri na yo, ko dai aika zamu yi? Wannan zuwa da kai ne ya fi aike, yadda hankalina yake a tashe idan ban je garin nan na yi magana da Malam ba na hura masa wuta ba zan samu salama ba, duk wani tsoro ya kau min a yanzu, ai sawun giwa ya zarce na rakumi, idan ma ba zaki je ba, ni zan shirya ma tafi Aa ba zan bari ki tafe ke kadai ba, idan kin zo zamu tafi tare Sai na shigo Ya katse wayar tana daga zanenta ta duba fitsarin da ke bin kafarta har lokacin mararta ta kasa rike su. Dole, wannan tashin hankali da me yayi kama? Ina ga Iyami ta dawo gidan nan kuma yarta ta auri mai kudi? Goma ta hadu da ashiri, rayuwa ta samu kenan Ta jefar da wayar akan gado. Ba zan taba bari ba, ba za a mareni a tsinka min jaka ba... Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo
Chapter 122 · 0% Book details