← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 143

Sashe 60

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dinsa kamar ke da Yayana Shi ke nan sai kuma aka ce miki wani abu ne tsakanina da shi? Hmmmm ai yau idan ya zo fita zan yi na tsareku da ido har na gane komai Okay ai tare zamu tafi, daman yace yau sai ya ga kanwata da nake ta masa rowa, but bari na fada miki Gaskiya babu komai tsakaninmu fa, gaisawa kawai muke shikenan Hmmm Yaya Namra i can read your eyes fa, shi ma alamunsa suna nuna akwai abu a zuciyarsa fa Namra ta watsa ido da mamaki. Ke Hurriya yaushe kika zama haka? Wato ko kunyata baki ji kai tsaye kike fadar haka Hurriya ta saka dariya sosai, sannan ta matsa kusa da Namra. Yaya Namra maganar Allah mutumen be miki ba? Namra ta yi shiru tana murmushi. Yaya, amman ba abun da kike tunani ne ba Zai zama abun da nake tunani soon Yaya Namra, daga ganinshi mutumen kirki ne dan Allah idan ya ce yana sonki karki ce aa Namra ta girgiza kai tana dariya ganin Hurriya ba zata barta da zancen ba, ta dauki filo ta rumgume. Kyaji da shi ke dai Hurriya ta yi murmushi. Haka Hurriya ta saka mata ido har yamma tana lure da yadda ta shirya turaren ma na musamman ta saka ta feshe jikinta ta ko'ina kamshi take. Ana gama Sallah Magariba before Isha'i Namra ta sauko tana sanye da wata Egyptian Abaya ko ina kyalli take gashi ta sha kamshi kamar wata amarya. Kusan wannan ne karon farko da wani ya ziyarci gidansu da sunan ganinta kuma shi ba dan makarantarsu ba kuma ba dan'uwanta ba. Har ta fita sai kuma ta dawo ta shiga dakin Hurriya dake kwance tana karatun Qur'ane. Hurriya ta so mu je Hurriya ta juyo ta kalleta. Ya zo Namra ta daga mata kai tana murmushi fuskarta har annuri take. Hurriya ta aje kur'anen ta dauko ta nufi Hijab dinta ta dauka ta saka. Amman Yaya Namra ki fadawa Momy? Kar ta fito nemanki ko nemana ba mu kusa Ban fada mata ba, dadina dake akwai zurfin tunani, bari na fada mata sai na sameki kasa Okay Ta juya ta fita daga dakin ta nufi dakin Momy, daga bakin kofar dakin ta tsaya ta fada mata tana da bako a waje zata je su gaisa, a take Momy ta yanke wayar da take fuskarta ta cika da annuri. Maa Shaa Allah, haka nake son ji a gaishe shi Ta yi murmushi ta yi baya ta ja mata kofar, kasa ta sauko ta samu Hurriya tsaye tana jiranta. Hannunta ta kama suka fita tare. Sai da Namra ta yi ta rabon ido kamin ta hango shi tsaye can gurin gate din gidan. Laa har can ya faka? Hurriya ta fada tana ganin kamar ya tsananta ma kansa fakawa a nesa da apartment din Momy. Tun kamin su karaso ya bude motar ya fito, farar shadda ce a jikinsa da hula shi ma sai kamshi yake zubawa irin na manyan samarin nan dake gasar nuna ado a gurin yan matansu. Haka nan Namra ta samu kanta da kunyar kallonsa har suka karasa gurin. Salam Salam... Ya amsa musu yana kallon Hurriya da murmushi a fuskarsa. finally yau dai an fito min da kanwar nan da ake ta min rowa Namra da Hurriya suka yi dariya kusan lokaci daya. Ba rowarta nake maka ba, kai ne baka bukaci gaisawa da ita ba To ai tsoro nake ji, kar ki ce min na karya doka kuma kin san mai nema taka tsantsan yake Haka ne Hurriya ta kalleshi ta ce. Barka da dare Hey Young Lady Lafiya Kalau Maa Shaa Allah, yau dai na ce zan zo na dubaki, even though dai aiki yana min yawa amman Yayanki tana min rowarki kullum idan ina cewa ina gaisheki bata ce min kina amsawa sai dai tace min zaki ji kina ji kuwa Hurriya ta yi dariya tana kallon Namra dake girgiza kai tana murmushi kawai yadda yake da son ban dariya abun yana burgeta. Tana fada min, kuma ina amsawa Good Ya fada still yana kallonta. Namra ta kalleshi kadan ta ce Ka shigo ciki No nan ma ya isa, kawai dai ki kawo min kujera na zauna Hurriya ta wara hannunta Bari naje na dauko... No bari na dauko Kamin Hurriya ta sake cewa komai ta juya ta nufi cikin gidan. Hurriya ta juya zata bi bayanta sai ya kirata. Ina zaki je? Zan taya ta daukowa ne Hmmm baki son yayarki ta wahala kenan, ni kuwa na saba bata wahala kullum saboda sai na ce ina gaisheki Hurriya ta yi murmushi ta bi bayan Namra, a tare suka dauko kujerun biyu ta nufi bangaren da Motar Momy take suka aje a gurin, yana ganin haka ya san baya bukatar ace masa ya karaso ya zauna, dan haka ya cira kafarsa ya gurin ya zauna a kujerar da Hurriya ya aje. Namra kuma ta zauna a dayar, sannan Hurriya ta koma ciki ta dauko musu ruwa da cups ta aje a gabansu. Ke ina taki kujerar? Hurriya na kallon Namra sai suka yi ma juna murmushi saboda tunawa da ta yi da cewar ta fada cewar zata tsaresu da ido har sai ta gano komai. Tana falo tana jirana, a sha ruwa lafiya Ta bar shi a gurin ta wuce, sai ya bita da ido har sai da ta kauce daga ganinsa sannan ya juya ya kalli Namra. Kanwarki nan tana da kirki, kuma tana da kyau ba zan yi karya ba Yeah haka ake yawan fada duk ta fimu kyau, kuma maganar gaskiya ta fi mu kirki, Hurriya tana da kirki sosai Maa Shaa Allahu haka ake so, ina take karatu? Tukuna nan dai bata fara jami'a ba Why? Takardunta ba su fito ba ne? Sun fito kuma sun yi kyau domin tana da kokari sosai, akwai abun da Appanmu yake jira ne shiyasa be saka ta ba Ko aure za'ayi mata? Ta yi dariya. Mu ma da muka gama jami'a muke maganar zuwa NYSC ba a yi mana aure ba balle ita, ita ce karama a gidanmu yanzu Oh... Na tambaya da tsoro fa, i thought answer ki would be yes Ta yi murmushi mai alamar tambaya. She's too shy bata son tsayawa ma, tana son saka glasses kuma yana mata kyau That's because of her illness bata gani sai da gilashi Whoo..what... Wow... Ya juya ya kalli part din Momy kamar zai ganta tsaye a gurin. Wow... Wow... He said for the third time. You make me like her more.. Gaskiya duk wanda ya samu yarinyar nan ya dace, and i think I'm the luckiest guy Namra ta kalleshi tana murmushi da ya zame mata kamar na dole ne. Hmmm The true is i like your Sister so much Namra, kuma na zo nan ne saboda na yi magana da ita, amman na ga tana da kunya sosai ko tsoron mutane take ne i don't know Namra ta sauke idonta kasa zuciyarta ta fara bugawa da mugun karfi, but she managing to wear her light smile on her face. Ya mike tsaye ya nufi gurin motarsa sai ta bishi da kallo har ya isa ya bude ya dauko abun da zai dauko ya kamo hanyar dawowa. Sai da ya kusa isowa sannan ta share hawayenta, not because of tana sonshi but because of disappointed, all her life ta dauka ita yake so ba Hurriya ba, yawan tambayarta Hurriya da yake ba saka ta kawo a ranta son Hurriya yake ba. A gurin da ya da ya tashi ya zauna ya mika mata ledar farko kamin ya mika mata ta biyu This one is for you, wannan kuma na Young Lady ne, last time i asked for her contact kika ce bata da waya, so na saka mata waya a ciki, ban sani ba ko za a barta ta yi amfani da ita, idan ma ba a barta ba, ba ki iya amfani da ita, ni dai abun da kawai nake bukata ta fahimci me yake tafe da ni, kuma ta tsaya ta saurareni, ta nan zamu fahimci juna da ita kamin iyaye su shigo ciki, idan Allah yayi, amman kna son ta san cewa ba da wasa nake ba, so ina ganin ke zaki min wannan kokari ki fahimtar da ita Ta amsa mishi da kai sannan ta mike tsaye rike da ledodin ta fara tafiya. Sai da safe...? Ya fada. Sai ta mayar masa ba tare da ta juyo ta kalleshi. Sai da safe Tun da ta saka gaba bata juyo ba har ta shige falon Momy. Tsaye ta yi da ledodin a falo not knowing what to say or do, Hurriya dake kokarin mikewa tsaye ta amsawa Momy dake fadawa Appanta yana nemanta a bangaren Hajiya Kaltume, ta kalleta ta yi murmushi irin murmushin nan na zolaya. ra ta kasa mayar mata da murmushi kuma ta kasa barin kofar falon da take tsaye, Momy ma dake tsaye stairs kallonta take kamar mai karantarta. Hurriya dake sanye da Hijab dinta ta nufi kofar falon ta bude ta fita ba damar ta tambayi yayarta me ke faruwa saboda Momy tana stairs tana kallonsu. Sai da ta fita daga bangaren Momy sannan hankalinta ya koma gurin kiran da Appa yake mata, tana ta tunanin laifin me ta yi? Hurriya... Ta juyo ta sauri ta kalli bakuwar motar dake fake kusa da motocin da suke bangaren Hajiya Kaltume. Na'am Ta amsa ba dan ta fa mai kiranta ba, sai Khairy da ta gani tsaye ta daure fuska ta rumgume hannayenta kamar an mata dole ta tsaya a gurin. Fadeel ya bude motar ya fito ya tsaya kusa da Khairy, Hurriya a ganinsa ta matsa ta gaisheshi. Barka da dare Sannu Hurriya, ya kike? Lafiya Kalau Dan samo min ruwa ciki na sha Ta kalli Khairy kamar ta ce wani abu sai kuma ta ji ba zata iya ba, ta juya ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta shiga, babu kowa falon dan haka ta wuce Kitchen kai tsaye ta dauko ruwa da cup ta dawo ta mika masa da hannu biyu. Ruwa ya fara karba ya bude sannan ya ta rika masa cup din ya zuba ruwan ya ya mika mata da dayan hannunta ya
Chapter 60 · 0% Book details