Sashe 80
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ahankali tace "a'a ni am on my period ma" wani irin murmushi Mummy tayi tace "to yaushe zaki gama?" cikin yar muryanta tace "gobe is the last day, the fourth day, jibi zanyi wanka" gyadamata kai Mummy tayi tace "shikenan dudda gobe zanzo dole nafada miki wanan maganan for security purpose, Rahima in mutumin nan yazo zai sadu dake ke sai inda karfinki ya kare, dambe zakiyi dashi kome kika samu ki buga mai, keko zai kasheki da kuka gwara ya kasheki din amma karki yarda ki yardan mishi yay amfani dake dan yanayi ya zubamiki kanjamau kenan S, HIV, HIV baida cure yana zuba miki mutuwarki yazo kenan gashi ke bakison mutuwa, koba wanan ba dama nariga na tsine miki albarka inhar kika yarda ya sadu dake, Rahima inhar zaki iya budema wanda yama mahaifiyar ki lilis gaba yaciki ai keba yar halas bane, sanan baki kishin mahaifiyar ki, Sameer makiyin kine, makiyanki nahar abada, ko hannun ki bai kamata kibari yarike ba Rahima, Rahima banson nafadi miki ne, kuma baniso nafadi ma Abban ki dan nasan nagayamai Sameer yamin dukan fitan hankali saiya kusa kasheshi zai iya samun heart attack Abban ku ya tsufa but Rahima naji jiki sosai a hannun Sameer....." tafashe da kuka sosai daya wani irin mugun taba zuciyan Rahima event din ranan yadawo mata sabo fil arai, hawaye ta share tace "kiyakuri Mummy kinji, wlh sainasan yanda nayi na ramamiki, mugu kawai azzalumi, Mummy kiyi shiru in kina kuka jinake kaman zan mutu kaman in kashe kaina, Mummy banso ana batamiki rai am sorry Mummy....n.....a" tai maganan muryanta na rawa zata sake fashewa da kuka, murmushi Mummy tayi ganin ta dana tarkon da kyau tana kara yabama kanta wato tagama da zuciyan Rahima ne tatas da babu wani matsiyaci aduniyan nan daya isa yace zai shigo yafadi nashi Rahima taji, ahankali Mummy tai magana cikin muryan ban tausayi ta yanda Rahima zata kara dilmiyawa tace "is okay, am fine, zanzo na daukeki gobe garinma zamu bari gabaki daya, nakaiki wani gari daban da babu wanda ya isa ya ganki, gobe kawai ki zauna da shiri sanan ki ijiye kunnenki akasa, take good care of yourself kinji, I love you so much Autana, kin tuna wakan danake miki?" gyadama Mummy kai tayi cikin wani irin kuka mara sauti gwanin ban tausayi tana mugun kewan Mummy tace "uh.....mm" jin muryanta yasa Mummy cikeda so tace "I said is okay kinji, don't cry your Mummy is coming tommorow, and trust me I am coming da shiri na babu abinda ya isa yamin so karkiji tsoron komi, stop crying wipe your precious tears, dakiyi kuka gwara kowa na duniyan nan yayi da Autana tayi, oya oya goge fuskar nan tass Mumy's heartbeat" da sauri Rahima ta goge hawayen tanajin kaman duk duniya batada kaman Mummy, Mummy tace "yauwaaa Auta na, My little little Rahima, my ballarina girl, bari namiki wakan kiji" _"Rahima Rahimomi, ta burka uban tumbudi, tadinga uban karni, yan-yan-yaaaaaaa"_ kyalkyacewa da dariya sosai Rahima tayi harta manta tana ma cikin bayine cikeda shagwaba ta turo baki tace "Mummy nifa bana tumbudi" da sauri Mummy tace "wai wai wai ai kece tumbudi factory Auta, kinsan nono baya kosanki anhada miki da madara aiko dan jijjiga kadan burrrrr kin burko tumvudi" dariya Rahima tadinga yi kaman ba itaba aranta tana cewa uwa dabance yaushe rabon datai dariya haka niko nace Rahima bakisan dawa kike tareba, Mummy ne ta dakatar da ita tahanyar cewa "okay okay dariyan ya isa haka, jeki ijiyema masu waya waya, wait, a inama kika sami waya dan wanan ba number Sameer bane" cikeda dariya kan fuskanta tace "gidansu mukazo, wayar matar kanin shi ne, Mummy kinga tsoho ne duk kannenshi sunyi aure" da sauri Mummy tace "bashine nake fadamiki ba, yaki auruwa ne, wace jakace zata yarda ta auri mai kanjamau shima babanki baya bincike ne saisa nakeso nazo na daukeki mu gudu na kaiki chan wani gari" aranta tace "straight to gidan karuwanci" sanan tace "just stay put koki ganni da wuri ko akasin hakan, karki fadama kowa da zuwana, oya bye" murmushi tayi tace "okay bye Mummy na I love you sosai Mummy na mai sona" tabe baki Mummy tayi tace "bye my Auta, the apple of my eyes" sanan ta katse wayan. Murmushi Rahima tayi ranta fess kaman anmata bushara da gidan aljanna tai deleting number Mummy daga wayan da call log din, bude kofan bayin kadan tayi ganin babu kowa adakin yasa tafito da saurinta ta ijiye takoma kan gadon tafada gadon cikeda murna ta kwanta yanda gadon yay kara yasa princess tabude idanu atsorace, fashewa da kuka tayi hakan yasa Rahima ta tsorata hannunta tasa tai patting bayanta cikeda lallashi tace "shiiii yakuri natasheki? Sorry" inaaa princess bamatasan hakuri ake bataba, da sauri Rahima ta tashi zaune cikeda tsoro yanda yarinyan ke tsala uban kuka saikace dukanta tayi, zamewa dan kwalinta yayi yafadi akan katifa, atsorace tasa hannu tadauki Princess cikin yar siriruwan muryanta tace "menene, sorry baby kinji, don't cry?" yarinyar ko kadan bamatasan anamata magana ba sai tattaba nonon Rahima take da hannu tanajan rigan tana daura kanta akan saman rigan daidai wajen nonon ta tana tsala ihu ita dole abata nono, rawa jikinta ya shigayi tama rasa mezatayima yarinyar yanda takejan gaban riganta da hannu daya tana kakkama nononta tasaman riga yasa kaman zatai kuka tace "yakuri kinji please" jin anbude kofa yasa tadago kai arude Sameer ne tagani yana sanye da kayanshi na dazu idanunshi sundan yi ja alamun bacci yayi kokuma daga bacci yatashi ya shigo dakin yana kallonta da princess kaman yanda take kallonshi, maida kofan yayi yakaraso cikin dakin yayi gaban gadon yace "why is she crying?" ahankali tasauke kanta ta kalli princess din tace "nima bansani ba yanzu ta tashi daga bacci shine taketa kuka kaga mamanta zatace nina daketa kuma wlh banmata komiba amma sai ihu takeyi" murmushi yayi jin maganan ta yadan duka yana kallon fuskan Princess din dake mugun ihu tana daura bakinta saman rigan Rahima daidai wajen boobs dinta sanan tana taba saman nonon ta daya leko ta saman riga da hannu tana kuka, hannunshi yasa ahankali yakama hannunta datake taba saman nononta dashi yaja hannun baya da sauri Rahima ta kallai shima dago kanshi yayi ya kalli kwayar idonta, sanan ya kalli princess din tareda sa hannenshi biyu yadauke ta yadagata sama yace "Hey princess stop touching what belongs to Uncle am I clear" saukar da kanta ahankali Rahima tayi kasa jin abinda yace taji wani irin kunya hannunta tamika ta dauko gyalenta dake bayanta ta yafa ta jan gaban riganta sama danya rufemata boobs, jijjigata Sameer yayi kafin yadagata sama washemai baki tayi saikuma ta kyalkyace da dariya sosai dan tana bala'in son Sameer, dariyan dataji da Rahima taji tanayi yasa tadago kanta ta kalleta, hada ido sukayi da Sameer daya wai go shima danya kalleta, dan murmushi yayi yace "inkika haihu zanga yanda zakiyi raino, can't wait" yajuya zai fita zai bude kofa kenan Nabila tabude murmushi tayi tace "tanata muku ihu Ya Sameer ina bayine, oya come here princess" tamikama princess hannu da sauri tazo sanan tamusu sallama tajuya tafita, maida kofan yayi yarufe yadawo. _CHASING THE HEART CRAVINGS_ _See en if you no get money, abeg no read my novel o if not I no yafe you u dey feel me?_ _where the people wey wan subscribe and read, but they no no how they go do am? Oya make una waka come here make I tell una_ _How to subscribe to CHASING THE HEART CRAVINGS_ _send 300 naira only to my account number 3107021073 aisha Muhammad first bank, then u do screenshot, send am for me on my watsapp 07012181461 then wen I see am, comfirm am, I go add you to the group wey I dey post this sweet book, wey sweet die, some people dey ask me Iya Shakur I no get bank oo, hahahha oya ejo Sisy London just send MTN card 300 me dey collect am you hear ba_ _Raise and Shine lovelies, and Happy Friday_ Ciki ya haryazo wajen inda take zaune tana fama dajan riganta sama yarufe nata kirji, ahankali yazauna kusada ita har jikinshi na gogan nata chak da sauri tamike tsaye dan hakanan taji ta tsani yamazo kusada ita yau Mummy takara tunamata abubuwan dayamata, hannunta yakama da sauri yarike, batare datajuyo ba kotai magana ba ta shiga kokarin fizge hannunta ta shiga yi hakan yasa ya jawota baya da sauri batare daya saketa ba yadaura kan kafafunshi ya matseta ganin tana kokarin fizge kanta yadaura kanshi kan wuyarta tareda jinginar da fuskanshi kan gefen fuskarta, Murya chan kasa yace "fushi kike dani?" yay maganan ahankali kaman bashiba shi kanshi baisan mesa yawani damu da yarinyar yanzu ba, shiru Rahima tamai bata tankashi ba yanda yasata ajikinshi yawani matse jitayi kaman yasata akaya ganin batada karfin dazata kwace kanta yasa tahakura da kiciniyar ta saukar da ajiyan zuciya tareda lumshe ido tana kokarin hana kanta numfashi sabida mayen kamshin shi daya gama mamaye mata jiki, shiru sukayi dagashi har ita suna sauraron yanda suka sauke ajiyan zuciya kusan atare, sosai yake kallon fuskanta ganin kaman ma batason yana tabatane ko batason kallonshi ne oho, murya chan kasa kaman mai rada irin muryan nan dayake ratsa zuciyan mace yace "sorry about what Ummi na did to you, Ummi is angry with me saisa kikaga tai miki haka, but I promise she's the sweetest Mum dabaki taba tunani ba, and I promise she will come around just give her some time, sorry Booby girl" yakara she maganan dawata irin yar gajeren murya mai dadi yana kallon fuskanta yadan saki murmushi, ganin kaman bataji meyace ba tamaki bude ido yasa yasakin mata light kiss akan white kumamtun ta yana kallon yanda gashin gaban kanta yawani kwanta yay wave kaman ta shafa gel, cikin wata irin shaukin murya yace "mesa kin iya komi u are very smart and very intelligent but kin kasa banbance tsakanin tsakuwa da aya, bakisan mai sonki ba bakisan mara sonki ba?" kaman bazatai magana ba saikuma ahankali tace "Mummy na ita kadai kesona, tafi kowa sona aduniyan nan, kuma......kuma....aikaine baka...sona" tai maganan tana bude idanunta, shiru yayi dan baisan mesaba yanda tacemai