← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 119

Sashe 29

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

M Shakur
2
Not edited
Fitowa yayi daga masallaci ya shiga motarshi ganin wayarshi daya bari na kuka kan kujera yasa yadauka ganin Chairman ne, murmushi yayi yakara akunne yace "Sir" daga tachan bangaren Chairman yace "My Friend kana inane ina jiranka fa, Judge yakira yaji komuna hanya yana jiranmu" dan sosakai Sameer yayi yace "yanzu nagama daga aiki natashi, I think katafi karyayta jiranmu mu duka ba dadi, am right behind u zanje gida nai wanka na shiryo nazo just go Sir" dan shiru Chairman yayi kafin yace "shikenan Lieutenant Sameer dina, saikazo" katse wayan yayi yatada mota zuwa gida da ya shirya.....
Wanka Rahima ta shiga tafito, zama tayi agaban madubin ta dudda gatanan gatanan ne she is feeling sick sosai amma saida ta daure tai hadadden makeup kaman zataje biki tasa wani nude lipstick tasaka kwalli idanuwanta sukai shegen kyau, tashi tayi tabude wardrobe dinta wani black dogon riga ta dauko mai hannaye baby pink tasaka dayake tai shaping rigan ya bala'in mata kyau sanan tadau dankwalin takoma gaban mirror ta zauna kan kujera tana kokarin daura dan kwalin aka bude kofar dakinta, dagakai tayi ta kalli kofar, Lubabatu ce itama taci gayu tasa doguwan rigan atampa ja yay mata kyau sosai, ta yafa jan veil hakan yasa ta ballamata harara tace "baki iya sallama bane malama" hararanta itama Lubabatu tayi tace "sabida baki koyamin ba saisa banyiba, kuma malama kifito Dady yace sun iso kowa na falo, stop trying ki daura gyalen nan akai, better learn how to yafa gyale da shegen kananun kitson kanta dasukai tsufa" tamata gwalo tasowa tayi cikin fushi tabiyota Lubabatu takwasa aguje tana dariya tai falo ganin haka yasa tai kwafa takoma daki turare ta dauka ta fesa sanan ta yafa gyalen akanta tawuce tafita tai kyau kayan daidai ita, daga Mummy saisu Siddiqa a falon kowa yay kyau Mummy tasaka wata doguwan riga brown irin na manyan matan nan tai kyau sosai ta yafa mayafi na alfarma, zama tayi kusada Mummy kaman zatai kuka tace "Mummy kinga Ya Luba tazo har dakina tana neman tsokana na ko" hannunta Mummy ta shafa tace "yakuri anjima zan mata hukunci, kinga yanzu bakin Abbam ku sun riga sun iso yafita shigo dasune kiyakuri kinji" gyadamata kai tayi daidai Dady ya kwada uban sallama, amsashi Mummy tayi ta tashi daga zaunen datake ganin Chairman mutumin jiyane yazo yasa tace "ahh Chairman kaine, marhaban dasu lale barka da zuwa" cikida fara'a Chairman yace "barka dai Hajiya, kingafa haka Allah ke hada zumunci komi da sanadi" dan dariya Mummy tayi tace "hakane, bismillah ka zauna, a'a kai kadai ne ina dayan?" kafin Chairman yay magana Dady yace "yana hanya bai dade da tashi daga wajen aiki bane yanzu muka gama waya dashi yace gashinan zuwa" cikeda fara'a Mummy tace "ayyah to Allah yakawo shi lpy" Siddiqa ce tafara gaidashi tace "barka da zuwa Abba ina yini" kafin ma ya amsa sauran suka gaidashi. "ina yini Abba" ahankali Rahima dake gefen Mummy tace "ina yini" murmushi yayi yace "sannun ku yarana, ya karatu?" atare sukace. "Alhamdulillah" Abba ya kalla yace "what a nice family you have Masha Allah, Allah ya rayamana" ahankali Abba yace "Ameen Ameen" Chairman yace "yaranka nakama dakai sosai wlh, Rahima ce kadai batai kama dakaiba" yanuna Rahima dake gefen dadi dan itakadai ce fara a yaran as auran duk black beauties ne, murmushi Abba yayi ya kalli fuskan Rahima yace "Rahima auta" dan dariya sukayi Mummy tace "Alhaji food fa is ready akawo ne?" da sauri Chairman yace "No no madam abarshi bayan isha'i lokacin Sameer ya iso, sai ayi komi by then in sha Allah" hira suka cigaba dayi kafin akira isha'i suka tashi sukai masallaci su Siddiqa kuma sukai dakin dan zuwa yin salla, wayan Chairman dana dasuka bari akan kujera dan zuwa salla ne ya shiga ringing, ahankali Rahima tace "Mummy ana kiran wayan abokin Abba" gyadamata kai Mummy tayi tace "eh" ganin wayartai shiru na Abba yadau ruri yasa Mummy tace "bani wayan nan Rahima ingani" tashi Rahima tayi tadau wayan takawoma Mummy karba tayi ta kalli wayan Lieutenant, da sauri tace "ina ganin abokin Baban ku dazaizo ne yakira wayan Chairman yaji shiru yakira na baban ku, tashi kije kidubo waje Rahima inkinga bako ki shigo dashi kar abarshi a tsaye" gyadama Mummy kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce tafita, slippers dinta dake bakin kofa tasaka tai hanyar Gate tana turo baki yau ko kadan bata hutaba, ahankali tabude Gate dinsu ta leko wani black mota Bentley tagani pake akofar gidansu gawani mutun tsaye jikin motar da bata ganin fuskarshi dan yabata baya fuskarshi na kallon hanya rikeda waya a hannunshi yana dannawa yana sanye da skyblue shadda bugaggiyar gaske tundaga Gate din takejin kamshin dayake yi, fitowa tayi daga Gate din gabaki daya ta tsaya daidai Gate dinsu tadan daga zazzakar muryan ta tace "kaine ke neman Abban mu?" wani irin juyowa Sameer yayi hannunshi daya sanye cikin aljihun wandonshi daya kuma yana rike da waya faduwa gabanta yayi sosai dan taga fuskarshi sabida hasken wuta dayazagaye kofar gidansu, kaman yanda ta zuba mai ido haka ya zuba mata ido, daure fuska tayi ta dauke kai daga kallonshi sabida yanda yawani cikamata ido tace "me kazo gidanmu?" daure fuska yayi yace "are you talking to me?" juyawa tayi batare data kalleshi ba tace "ance kashigo" tabude Gate dinsu ta shiga, ahankali yabiyo bayanta ya shigo gidan yana kallon yanda take tafiya kaman zata tashi sama har zuwa gaban flat dinsu ta tsaya ta juyo tareda kallonshi dan tasan inta shiga batare dashiba Mummy zatace mata ina bakon, kallonshi tayi yanda yake tafiya daidai hannunshi har lokacin a cikin aljihu dayan kuma yana daddanna waya yana tafiya ahankali, ashagwabe kaman zatai kuka dan ta gaji bacci kawai takeso tayi tace "ni kayi sauri kona tafiyata wlh na barka anan" dagokai yayi ya kalleta jin anbude Gate yasa ta kalli Gate da sauri ganin Abba ta ne yasa da sauri ta taho inda yake jikinta har rawa yake ta kallai tana satan kallon Abba tace "uhmm sannu dazuwa, ance ka shigo ciki" "Lieutenant" yaji Abba ya kirashi hakan yasa yajuya da sauri ganin Abba ne da Chairma yasa yakarasa suka hade ya mikamusu hannu cikeda girmamawa yace "welcome sir" cikeda farin ciki Abba yace "yaushe kazo Lieutenant?" ahankali yace "just now sir" kallon Rahima dake tsaye Abba yayi yace "what are you doing outside Rahima?" ahankali tace "Mummy tace naje na shigo dashi taga yakira wayar ka ne" cikeda fara'a Abba yace "Allah sarki sorry masallaci mukaje munbar wayan mu aciki, kumuje ciki" da sauri Rahima tai gaba suka biyota abaya suna hira.
Sallama Abba yayi suka shigo falon tashi Mummy tayi cikin fara'a tace "sannu ku da zuw......" kasa karasa maganan tayi sabida sauka da idanunta sukayi akan Sameer dayake shine ya shigo na karshe, cikin fara'a Abba yace "kinga shine Lieutenant din, Lieutenant meet my wife the mother of my children" cikeda girmama wa Sameer yace "barka da dare Mama da fatan na sameku lpy" wani irin murmushi Mummy tayi tace "lpy kalau Sameer, aiko suna mai dadi shigo shigo mun barka tsaye, zoga wuri ka zauna" tanunamai kujera zama yayi anatse looking compose fitowa su Siddiqa sukayi harda Rahima cikeda girmamawa suka gaida Sameer. "sannu da zuwa ina yini" kallonsu yayi fuskanshi cikeda murmushi yace "sannunku ya school" ahankali sukace Alhamdulillah, murmushi Abba yayi yace "to Masha Allah sannunku da zuwa Chairman and Lieutenant Sameer, this is my Family, Allah has blessed me with four daughters, ga Siddiqa nan" ya nuna Siddiqa yace "itace babban y'ata ta farko, mai sunan Mamana, ansamata rana in sha Allah June-July zata rubuta final exams dinta accounting taje karantawa August ne bikinta nan da four month" cikin jin dadi chairman yace "masha Allah, Allah ya sanya alheri" atare Abba da Mummy sukace Ameen, Abba yace "sai Zeenatu" yanuna Zeenatu dake kusada Siddiqa yace "she is my second daughter Zeenatu, tana 300 level a makaranta tana karanta mass communication tace ita yar jarida takeso tazama" duk dariya akai afalon Zeenatu ta boye fuskarta cikeda kunya, Abba yace "sai Lubabatu" yanuna Luba dake zaune kusada Zeena yay murmushi yana kallon Zeenah yace "itace tace tanason ta gaji mahaifin ta saidai ba Civic law ba shari'a law takeyi tana 300 level itama" kabbara chairman yayi Sameer yay dan murmushi, Abba yace "sai autan gidan Rahima" yanuna Rahima yace "kwanan nan ta shiga University, medicine tai applying bata samu ba sai suka bata veterinary medicine, nace tafara shi ahaka mugani next year saitai applying change of course hopefully zasu bata medicine din" ahankali Chairman yace "Allah ya yarda".
Wani irin kallo Mummy kema Sameer harsaida yaji ajikinshi yadago kai hada ido sukayi wani irin murmushi tayi tace "atashi aci abinci bayan angama sai kumana introducing kanku ko Lieutenant" gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba, Mummy ta kalli yaran tace "alright girls to the kitchen time for dinner" tashi dukansu sukayi sukai kitchen, warmers da suka shiga fitowa dashi Rahima kuma ta kwaso broken plates tana tafiya ahankali takawo tsakiyan falon dayake fankacecen falone suka ajiye Mummy kuma tafito daga kitchen din tai corridor ta shiga ciki, dakinta tayi tabude wardrobe dinta, wani hadadden lace
dinta ta ciro na 98k da aka mata dinkin riga da skirt blue black ne kalan lace din, agurguje ta shiga shiryawa cikin kayan aiko sun kamata chip chip kaman wata yar matashiya ta zauna gaban madubi hoda ta shafa tasaka wani jan jambaki sanan ta daura kallabi tafito tai dakinsu Siddiqa, drawer su dasuke saka gyaluluwan su tajawo tabude wani hadadden dan karamin gyalen Lubabatu blue taciro tana murmushi, yafawa tayi akafada tana kallon kanta a dogon babban madubin su, koyan murya tafarayi agaban madubin cikin wani murya irin na yan gayun nan tace "Lieutenant Sameer sauko kaci abinci please, ko kanaso adafama wani special ne?" wani irin murmushi tayi tace "yes yes yayi" da sauri tafito ta maida kofan tarufe hartakai hanyar fita ta juyo da sauri tace "turare" dakinta takoma ta feshe kanta da turarurruka sama da shida sanan tafito tana taku daidai kaman jimina, ahankali ta yaye labule tafito tana kallonsu ganin duk basu sauko kasa an faracin abincin ba, dan ware ido tayi ta juyasu cikeda yanga takaraso cikin falon tana kallon Sameer da hankalin shi kekan maganan da Abba keyi dan zancen politics sukeyi, cikin wani irin strange new voice tace "Sameer, I mean lieut" tawani kaurara Lieut din, tace "sauko kaci abincin ka karka biyema wayan nan indai Abban sune zai iya kai gobe yana maganan siyasa bai gajiba" dagokai Abba yayi ya kalleta, murmushi tayi tace "Alhaji cemai ya sauko please" kallon Sameer Abba yayi da Chairman yace "let's all have dinner, bismillan ku" saukowa kasa Abba da Chairman yayi hakan yasa ahankali Sameer ya sauko kasa shima tareda tankwashe kafa, cinyoyin shi Mummy tabi dawani irin kallo kafin ta juyo ta kalli su Siddiqa tace "oya ku matso za'ai having dinner" sanan ta kalli Rahima datai shiru ita kadai kan kujera duktai wani kalan tausayi she is not just comfortable dandai Abba nanan ne da wlh tuntuni tagudu dakinta, murmushi Mummy tayi tace "sorry Autana oya come have your dinner sai kije ki kwanta bacci kikeji ko?" gyadama Mummy kai ashgawbe tayi ta sauko kusada Mummy tazo ta zauna ta dafata murya chan kasa tace "Mummy tare zamu kwanta ko?" girgixa mata kai Mummy tayi tace "no Autana sai bakin mahaifin ki sun tafi, idan kin kasa baccin kije dakin yayinki ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi Mummy tai murmushi tace "gud now let's eat" dan satan kallon Sameer Mummy tayi ganin hankalin shi bamaya kansu yasa cikin wata yar murya tace "me zakaci Lieuttt?".
*_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always
Chapter 29 · 0% Book details