← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 119

Sashe 78

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

talk to Noor properly, bayanta yashafa ahankali yay cuddling nata tight with both hands sanan yajuyo da kanshi ya manna mata kiss akafada, hannunshi yadaga daga bayan nata yamika yadauko bra dinta daya wurga chan gefe yana kallon Bra din, bayanta yashafa cikin wata siriruwan murya yakirata. "Rahimah" ahankali batare datayi ko motsi ba tace "uhm" cup din bra ya matse cikin wata Yr karaman murya yace "isn't this bra too small for you?" gyadamai kai tayi ahankali batare data dago kanta daga kirjinshi ba tace "wanda kasawo minne awajen nan" tana maganan dawani irin sanyi kaman wacce bataci abinci ba for a year, sosai yaji yana wani irin jin shauki is he in love with this girl? Kai Haba No mana yay maganan aranshi, this Indomie generation. Ahankali yashafa bare bayanta yace "you mean haka kike ta saka bra dasuka miki kadan?" cikin sanyin ta tace "the strap are okay but the cup were way too small" bayanta ya shafa yadan saki wani naughty smile yace "Booby girl" manna fuskarta tayi akan kirjinshi cikeda kunya kaman zata nitse awajen jin sunan daya kirata dashi, dan dariya yayi ganin yanda taji kunya kafin ahankali cikeda neman tsokana yace "tashi lemme see them again ma" rungume shi tayi sosai tadaura hannunta kan wuyan shi tana murmushi tace "ohh'oh" murmushi yayi shima yace "tashi ki shirya mutafi" yay maganan yana bambarota daga jikinshi, ahankali ta tashi batare data bari sun hada idoba bra dinta na hannunshi ta fizge ta sauka kasa baya tai luuu zata zube dan batada karfi da sauri yariketa yace "hey careful" hada ido sukayi kafin ya janye idanunshi yadaura akan boobs dinta tureshi tayi da sauri tajuya tabude bathroom ta shiga yabi waist dinta da kallo, bra tasaka sanan tafito ganin bataganshi adakin ba takarasa da saurinta tadau pad takoma bayin ta shirya tsaf dan she was wet ta jika pad din dazu sanan tafito rigan ta dauka ta saka taja zip din daidai inda zata iya sanan ta gyara daurin dan kwalin ta tana kallon lips dinta daya shanye lipstick din tatas tasake saka sabon lipstick sanan yadau dan mininin gyalen ta yafa tafito daidai bakin kofan ta sukaci karo yace "ina zaki da wanan abin?" yanuna mata mininin gyalen, kasa magana tayi tace "dont you know that you are now a married woman, go back jeki sako babban mayafin nan not this" ahankali tajuya duk ranta yabaci tadauko mayafin ta yafa kuma yamata kyau sosai kodan bata saba saka irinsu bane oho amma dai tai kyau baice mata komiba yay gaba tana biyeda shi har mota yabude ya shiga itama tabude dayan bangaren ta shiga, tada motar yayi sojojin suka budemai gate yafice, sai kallon hanya takeji tanaji kaman yakaita tadubo mummy taga ya jikinta amma tasan bazai tabayiba mutumin daya tsani Mummy ta, agaban gidansu yay horn mai gadi yabude mai gate ha danna motarshi ciki. Hadadden gidane sosai dan zata iya cewa yamafi gidansu kyau sosai, wasu yara guda biyune suka fito daga babban flat din da gudu daya doguwa ce dan tamafi Rahima tsawo sai dayan da batada wani tsayin kirki sun saka wani paper lace milk color da orange mai shegen kyau aguje suka taho suna ihu. "oyoyo Ya Sameer, Oyoyo Ya Sameer" bude kofan motan yayi yafito wearing a smile ganin kannenshi da gudu Yusra tafada jikinshi tana murna. "Ya Sameer oyoyo, ina matarka, Mummy tacemana kaima kanada wife like Ya Noor and Ya Muhammad hakane?" dagata sama yayi ya sauke yana murmushi yace "that's right Yusra" yay maganan yana kallon Asiya data tsaya tana murmushi sosai tana kallonshi kaman zata hadiyeshi raman dayaga tayi yadauki hankalinshi yace "what happen to you were you sick?" yay maganan yana rike hannun Yusra datake kamamai hannu, gyadamai Kai Asiya tayi ahankali takaraso kusadashi saikuma tafada jikinshi ahankali tace "ina yini yayan mu" tai maganan tana dagowa yabi fuskarta da kallo trying to read her kafinma yabata amsa Yusra tace "Ya Sameer where is your wife? Mummy said u are coming with her inatake?" motan yanuna mata yace "tana ciki" da sauri Yusra tazagaya zuwa sidedin da Rahima take tana zuwa tasa hannu tabude marfin motan takamo hannun Rahima tana murmushi kaman anmata bushaea da aljanna tace "laaaaaaa Anty Asiya come and see Ya Sameer's wife, wlh she is so beautiful kaman those Arab ladies damuke gani a Saudi Arabia when we went for Umrah" tai maganan irin yaran yan gayun nan tana kallon Rahima dake kallonta tasake washe mata baki shafa hannunta dayaji lalle tace "please Anty Ya Sameer wife come down let's go kinji" gyadamata kai Rahima tayi ta sauko ahankali Yusra bamata bari tarufe motar ba takamo hannunta suka zagayo ta inda Sameer yake dan waigowa Sameer yayi ya kallesu batare da Asiya ta kalleta ba tajuya tai cikin gida abinta wani abu ya tsayamata amako giro, karasowa sukayi har wurin Sameer din sanan Yusra tace "yauwa Yayan mu mutafi" dan murmushi yasakin mata yajuya gani yayi ba Asiya, abin ya mugun bashi mamaki saikuma ya fuske yafara tafiya suna biyeda shi har falonsu, su Noor ne da matayen su a falo sai Asiya dataje ta zauna kusada Mu'az, sallaman Sameer yasa dukansu sukadau ihun isgilanci. "oyoyo angooo hohohaiiii" su Nabila kuma sukai wajen Rahima datakasa dago kanta, hararan su Sameer yayi ya amsa gaisuwan su Nabila sanan yace "inasu Baffa" wani makirin murmushi Noor yayi yace "suna dakin Abba" hanyar stairs yayi Nabila kuma takamo hanun Rahima tace "muje ki gaishe da Baffan mijinki da matarshi maman su Yusra da Asiya kenan sai kuma Ummi Maman mijinki" gyadamata kai Rahima tayi wani kuka na zuwan mata abakin kofar dakin Sameer ya tsaya yana jiran isowar su Rahima, har gaban dakin Nabila takawota tanama Sameer murmushi sanan tajuya tai kasa, dan dagokai tayi ta kalli Sameer kaman yanda shima yake kallonta raurau tayi da idanu zata fashe da kuka hannu yamika mta da sauri tarike hannun ya jawota har gabanshi cupping fuskarta yayi murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasu iyajin mesuke cewa yace "menene? Don't cry for me wat is it?" hawaye ne shar suka zubo da sauri yasa hannunshi ya sharcesu yace "menene?" cikin kuka tace "am scared they're many people here" cikin wani irin sweet tone yace "kin fison dagani saike?" da sauri ta gyadamai kai, dan murmushi yayi yace "let's go in kiga Ummi na" gyadamai kai tayi yabude kofan ahankali taredayin sallama dagokai Ummi dake zaune tareda Baffa da matar shi tayi ganin Sameer tareda wata yar yarinya da kanta ke kasa yasa tadauke kai kaman bata gansu ba, tsayawa yayi chak yana kallonta ganin haka yasa Baffa yace "ku shigo mana Sameer kabar yarinya atsaye angayama kowa sojane irinka?" shigowa yayi ahankali Rahima biyeda shi yasami waje yazauna aksa Rahima ma haka a gefenshi, ahankali kanshi akasa yace "ina yini Baffa, Ummi ina yini, ina yini Mum" tsaki Ummi tayi ta mike tsaye tareda kallon Baffa tace "Baffan su bari nadan kwanta" , ya kalli Mummy su Yusra tace "bari nadan kwanta Maman Asiya" bata tsaya jiran amsan suba tawuce tafice abinta daga dakin Sameer yabita da kallo ranshi duk adagule saikuma ya saukar da kanshi kasa, jin shiru yasa cikin siriruwan muryanta dake dan rawa Rahima tace "ina yini Abba, ina yini Mummy" daga Baffa har Mummy murmushi sukayi kafinma Baffa yay magana Mummy tace "ahh lallai su Soja yanzu nagane abinda yasa kaki aure dawuri ashe jira kake ka dallo mana balarabiya haka, yarinya murya kaman an busa algaita, Masha Allah, Allah yay albarka sanan Allah yabada zaman lpy yakawo zuri'a dayyaba" ahankali Sameer yace "Ameen, mun gode Mummy" sanan Baffa yay gyaran murya amatsayin shi na babba nakuma mahaifin Sameer yashiga musu waazi yana tunatar dasu hakkokin aure da yanda ake rayuwan aure, waazin yadan dau lokaci sanan yamusu addu'a shima yace "tashi Sameer ka dauki matarka ka kaita har dakin mahaifiyar ka ta gaidata" gyadamai kai Sameer yayi yamike tsaye itama Rahima ta tashi ahankali kanta akasa yana gaba tana biyeda shi har falo babu kowa a falon sai Asiya dake kallon wani Indian series ta kwanta kan dogon kujera da alamu sauran kodai suna flat din Noor kona Muhammad dayan biyune danya tabbatar Ummi ce ta kadasu data sauko maybe sun cika falon da hayaniya, baice ma Asiya komiba yay dakin Ummi Rahima biyeda shi, ahankali yabude kofar dakin Ummi tareda yin sallama Ummi na zaune kan kujeran dakin rikeda littafin zikiri tana karantawa, ga akwatuna guda 24 jere atsaye a tsakar dakin hadaddun gaske jin sallama yasa ta dago kanta Sameer tagani da matarshi da kanta ke kasa, hannu ta nunamai babu alamun wasa kan fuskarta tace "karka yarda kabar yarinyar nan ta shigo dakina mena fadamaka? Nacemaka babu ruwana da auren ka babu abinda yashafeni daku to me kake neman chusamin ita, take her out of this room Sameer!" Ummi tafada tana dakamai mummunan tsawa, fashewa da kukan da tuntuni Rahima ke rikewa tayi Sameer yakama hannunta ahankali suka juya zasu fita cikin fushi Mummy tace "and kadawo ka kwashi tarkacen nan" tanuna mai akwatunan tace "darajan Baffan ka yasa nabari ma aka shigomin dasu daki but Allah yakawo ka yanzu kaje kadawo kafita dasu" Da sauri Sameer yajuya yafita da Rahima yazauna da ita kan kujera murya chan kasa yace "stop crying am coming" tashi yayi yakoma cikin dakin yabar Rahima da Asiya datai kaman kallo takeyi afalon, wani irin murmushi Asiya tayi ta tashi zaune saikuma tamike tsaye tazo daidai gaban Rahima dake goge hawayen da takeyi da bayan hannu tace "this is what you get for marrying wanda baison ki, Allah kara kuma in sha Allah kwanannan Ummi zata sa yasake ki yakadaki gidan ubanki" wani mugun kallo Rahima tamata kawai tsoron Sameer yasa tai shiru dan nan gidansu ne amma dasaita nunama yarinyar nan ainda take ita bama ta iya komiba dan tafi uwatta iya rashin kunya, gwalo Asiya tamata tajuya tafita daga falon tai waje. Sallama Sameer yayi ya shiga dakin yana kallon fuskan Ummi data amsashi da kyar, kaman zaiyi kuka haka yakeji, karasawa gabanta yayi ya tsugunna ahankali yakama hannunta ahankali yace "Ummi am sorry dan Allah kidena fushin nan dani konazami kwanciyan hankali please Ummi na, Ummi" yakira
Chapter 78 · 0% Book details