← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 119

Sashe 19

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M Shakur
1
Kunna motar yayi yaja yana tafiya ahankali yazo yawuce su ko lura basuyi dashi ba yay gaba da gidan yana hango asalin mutanen cikin gidan dake main rawan dan anbude Gate, rawa kawai suke na hauka definition of real clubbing suke yi abunsu, ga drinks tako ina sunasha, wata mace dan wandon datasaka mai kama da pant ne ta zameshi kasa zuwa wurin gwuiwa ta shiga rawa da bare duwaiwai ta hakan yasa mazan sukayi ihu suka taru akanta suna zuba mata kudi suna shasshafa ass din suna ihu suna DJ DJ give us shake up your bombom, duksun rude, ganin haka wata tafito itama da nonuwanta waje ta hanyar tuge bra ta yar akasa dan attention din yakoma kanta da mugun sauri Sameer ya dauke kai yace "subhanallah!" txt message daya shigo wayanshi ne ya kalla _we are close Lieutenant at kaduna kano express road already_
dan gaba yayi sanan yay reverse yasake wucewa ta kofar gidan yafita daga layin yafito hanya ta yanda dazaran sunzo zasu ganshi ya kashe motar ya saukar da tinted glass din motarshi kasa yana kallon hanya, ko minti biyu baiyiba ya hangosu sun taho motoci biyune na gaban golf ne da maza kusan takwas ke ciki mutum uku a gaba hudu a baya suna fanfala uban gudu kaman motar ambulance, sai dayan vehicle dinkuma nakama mutane ne, horn ya danna musu sau daya hakan yasa suka gane suka karyo kwana suka shiga layin da gudu shima ya kunna motar ya shiga, ta baki bakin layin sukai parking dan basuso su gudu, kashe motar yayi yabude yafito kaman yanda suma suka fito suna sanye da normal kayan gida sai bullet proof jacket maroon color da aka rubuta NDLEA ajiki, musabaha sukai da Sameer kafin yace "musu let's go, no shooting no maltreatment, just catching them dat is all what we are up for" atare dukansu sukace "yes Lieutenant" wani mugun respect suke bashi dan Sameer yayine kawai arayuwa, sukai wajen da gudun su, wata yarinya dake kiss da saurayin ta agaban gate dinne idanunta a lumshe kaman ance ta bude ido tabude ta hango maza da soja na dumfaro su da sauri, fizge bakinta tayi tawani irin kurma uban ihu. "policeeee, everybody runnn!" dudda dukansu are drunk kalmar police kalma ce da duk wani dan shaye shaye is so caution of, sunan kaman kararrawa yake in the mind so it always ring and alarm to their ears, kaman an zubamusu wani irin dawowa hankalin su, firgigit idanunsu ya washe diddirkowa sukai daga motan sukahau gudu wasu suka yanka dajin wajen yayinda yan NDLEA din suka chapke na chapkewa suna dannesu suna kulle musu hannu da disposable plastic handcuff, some na dagasu suna kaisu mota suna rufe su aciki su dawo su kwashi wasu, all this while masu rayen cikin gidan bamasu saniba, cikin gidan Sameer yashiga wasu yan NDLEA guda hudu biye dashi, ihu gidan ya dauka kowa gudu yake, Djs dinma sukabar kayan kidan sukai tatayi, wasu sun rasa inda zamasuyi hakan yabasu ikon kamasu, wasu are running to the fence jumping suna shiga dajin baya suna guduwa, karasawa Sameer yayi yasa hannu ya cisge wayoyin kidan hakan yasa gidan yay tsit.....
Ihun da Chris yaji tako ina da kuka wanda matayen da aka kama keyi yasa yasaki Rahima daya danne ta suna kaukawa dadan ragowan karfin daya rage mata yatashi da sauri dagakan jikinta jin ihu da sahun gudu ga music da kida dake tashi tun dazu shima yay shiru kaman an kashe, labulen window yadan kama ya yaye kadan ya leka wani irin dallo idanu waje yayi hango abokanenshi maza da mata su kusan 15 da aka kamasu an daure musu hannu da disposable plastic handcuff ansasu kneeling down agaban gate ana fitar dasu daga gidan one by one, wasu yan NDLEA guda biyu kuma tsare dasu gudun karsu gudu, dawani irin mugun sauri yasaki labule window jikinshi har rawa yake ya kalli Rahima dake kwance yanda ya barta duk riganta ya chukwuikuye idanunta a lumshe tasaki baki abude tana bacci, hannunta yakama yadaga ta zaune yace "Beautiful stand up let's run" wani irin luuu Rahima tayi takoma kwance tana buge hannunshi cikeda masifa, tsaki yaja da sauri yadauki key motarshi daga kan table yabude kofan ahankali gudun karyay kara asirinshi ya tonu sanan ya leko da kanshi kadan dan duba ko akwai mutane a falon, ganin babu kowa a falon yasa da gudu yafito yay hanyar kitchen sabida yabita backyard fence ya dirka ta baya ya arce daidai lokacin Sameer ya shigo flat din, ganin Chris yafito daga wani daki da gudu yayi ta kitchen yasa yabishi da gudu, daidai ya shiga kitchen wani officer NDLEA dayaji fitowanshi ya labe abayan kofan gudun karya ganshi yafito ya tadiyeshi yafadi timm akasa, ihu Chris yayi dan yaji zafin faduwan yace "officer I didn't do anything naaa, we are just having birthday party fa, why u wan arrest me en? Wetin I do naaa?" dagashi officer yayi bayan ya kulle hannayen nashi cikin tsawa yace "my friend shut up, we we are busy having sleepless night to make sure youth like you stop all this kind of life and be serious with your education so that u guys will have a bright future but you guys are here busy taking what is killing you and killing your future as well, let's go my friend" ya fincikeshi sukabi ta gefen Sameer dayay irin tsayuwan sojojin nan yana kallonsu suka fita sanan yadaura idanunshi akan dakin dayaga Chris yafito daga ciki kafin ahankali yadaga kafa yafara tafiya daidai boot dinshi na making sound yakarasa wurin dakin da Chris yafito daga ciki, yadade yana kallon kofan yanabin rubuce rubuce da Zane zanen dake jikin kofan da kallo zanen shisha pot dasu cigarette ne a jikin kofan katakon da akai da biro, ahankali yazare hannunshi daga bayanshi yakama handle din kofan yabude kofan wani irin warin wiwi da sauransu ne suka dakanmai hanci hakan yasa ya yatsine fuska kafin idanunshi su sauka kan Rahima dake kwance tana dirkan baccinta hankalinta kwance, kallo daya yamata yagane musulma ce ita, ita kadaice musulman dayagani tunda aka fara fito da matayen dake wurin, wani officer ne ya shigo dakin yana tahowa wajen Sameer yace "da saura ne Lieutenant?" gyadamai kai Sameer yayi kafin ya nunamai cikin dakin dayake tsaye a gabanshi da sauri officer ya shiga cikin dakin yay inda Rahima ke kwance, hannu daya yasa ya fincikota hakan yasa ta tashi tsaye luu kaman zata fadi, turo baki tayi sosai idanunta arufe cikin fushi da shagwaba in a very slow way tace "leave me aloneeeeeeee Chris" tai baya luuu takoma zata fada kan kujeran a mugun buge, sake fincikota officer yayi yana kokarin kama hannun ta tabaya ta fizge kaman zatai fada dashi tana layi, cikin slow tsiwa irin na wanda ya bugun nan tace "leave me kona dalla maka mari, I want to shower, uhmmmm wanka nake kadena damuna, kawomin ruwa in sirka ruwan zafin Ya Siddiqa" tawani irin zube akasa wurin kafin ta daura kanta kan table din dasu shisha pot kekai tacigaba da bacci, officer zai kara kamota akaro na Uku Sameer yace "wait!" tsayawa chak officer yayi ya kalli Sameer din dahar lokacin bai shigo dakinba, takowa yayi ya shigo cikin dakin, babban bottle water Swan daya gani kan side drawer gadon dakin yadauka ya shiga budewa yana tahowa inda take kwance gaban kujera ta daura kanta kan table tana bacci tana surutai kasa kasa, matsamai Officer yayi yakoma baya, tsayawa Sameer yay akanta ya cillar da marfin goran gefe, daga goran sama yay da hannu daya ya shiga kwararo mata ruwa kaman ana mata fitsari akai yana sauka saman dankwalinta, dudda she was damn high amma saukan ruwa dataji akanta yana sauka kan fuskarta wasu na shiga kunnuwanta, wasu na gangarawa wuyan ta zuwa cikin riganta yasa ta mugun zabura kaman wacce ta zare ta mike tsaye tana shashare fuska tana wanan nishin da mutum keyi in ruwan sanyi na tabashi tana sauke ajiyan zuciya tana share fuska tana kokarin ta bude idanu takasa sabida yanda ruwan ke saukowa, dudda ta tsaya agabanshi tana shashafa fuska trying to open her eyes baisa yadena kwara mata ruwan ba harsaida ya juyemata ruwan goran tass sanan ya tsaya, wani irin ajiyan zuciya ta sauke tasa hannayenta duka biyu ta share fuskanta ruwa na diddiga harta cikin riganta, ahankali ta janye hannunta daga kan fuskar nata cikeda bala'i tace "uban wayace kazubamin ruwan sanyi ajikinta eh?" sanan tabude idanun nata tass ta saukesu kan fararen kafafun ta dasuka jiku da ruwa tana kallon wani boot army green dake gab da kafafun nata ga dilli dillin ruwa akan boot din shima, tundaga kan takalmin shi take binshi da kallo har zuwa kan cikinshi zuwa kirjinshi da a iya nan tsawonta ya tsaya kafin ta daga kanta da fararen idanunta dat look moist tsabagen ruwan dasuka sha ta daura dara daran idanunta akan fuskarshi kaman yanda shima yake kallonta fuskarshi babu alamun Rahama balle dariya, wani irin faduwa gabanta yayi ganin wani babban soja a gabanta gashi da tsayi bakin mutum, kasa motsi tayi balle ma tasake yunkurin magana batare daya janye idanunshi daga kanta ba yawani irin cillar da goran ruwan dayagama juyemata cikin kakkausar murya yace "take her away Officer" da sauri officer yakaraso wajen yana kama hannunta ta baya yana handcufff nata Sameer kuma yajuya yana takun nan kaman wani bijimin zaki yafita daga dakin, saida yafita daga dakin kaman anbude mata baki ta shiga kokawa da officer tace "me haka kakesamin a hannu ina zaku kaini? Su waye ku mena muku? Ina zaku kaini eh? Chris" ta kwalama Chris kira.
_Zan baku another page anjima koda bayawa, ina bimuku book din daki daki ne VIPs, I've been busy yau wlh, sababbin kajina nata mutuwa, guda goma shadaya sun mutu yau, cuta takamasu, nakira Dr wai sanyine, sauran ma don't look good at all, wlh kaman zanyi kuka, dan Allah kumusu addu'a banso nai asara, gobe fa zamasu cika sati daya da sayosu
innalillahi wa innailaihi raji'un_
*_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always
Chapter 19 · 0% Book details