← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 119

Sashe 44

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zakiyi duk zaki iya" cikin fushi Rahima tace "Allah ya kyauta nai wanka agaban mutane" murmushi nurse din tayi batare datace komi ba, hawaye ta share tabude box din taciro brush da toothpaste tai wajen wash hand basin, brush tayi tass tagama sanan ta mayar tadauko soso da gel din wankan tai wajen bayi shiga tayi ta gyara labule ta shiga wanka, dudda bayin is very neat but kyama ya dinga bata danjun warin different sabulu da different mutane takeyi ko minti biyu batayi cikiba tafito daure da towel takaraso inda nurses din suke suna jiran ta mayar da sosin tayi sanan ta rufe nuser din tace "saura password" wasu nambobi kawai ta danna nurse ba tace mata komiba tace "mutafi" suna biye da ita suka koma ward dinsu, jakanta da Sameer yabasu jiya nurse din tadauko, wani black bra mai kyau ta ciro ta ijiye mata akan gado, da black singlet, sai wani black pant da cream ta ijiye, sanan tadauko new uniform dinta baby pink ne uniform din dakeda wasu irin Zane zanen abubuwa ajiki bakake, sai musulmai za'a basu wani dan karamin Black hijab iya kirji, but sawan in kaga damane da hula, sai black rubber crock shoe da nurse din takawo size 37 dan tun jiya datana bacci suka gwada mata sukaga yamata, rigan mai V neck ne daya tsaya daidai iya cinya sai dogon wando da baida shape an saki wandon, bayan rigan akwai number ajiki da suke amfani dashi wajen gane patient, number last two digit din hospital number da aka bakane, sanan digit din shine number gadonka, sanan number dake jikin riganka, suna hakanne da boye info din patient koda wani zaizo, haka akomi basa addressing patient da suna sai number, warware rigan Rahima nurse din tayi taga 16 ajiki tace "u are number 16, dagayau sunanki 16" wani kallon ranshin kunya Rahima tamata tace "sunnu ubana yaushe kika yankamin ragon" murmushi kawai nurse din tayi dan sunsaba da wanan halin na patients nasu rashin kunya kuma ka'ida ne a rehab centre din babu duka duk nurse din data daki wata patient kodakam patient dinne tafara dukansu inhar ta mayar da martani to tarasa ajikinta, saisa awajen Binta da Asabe ne kawai are in charge su hukunta wasu su dinma basayi dan ganinsu kadai yana firgita patient, ajiye mata komi nurse din tayi kan gado tace "get ready number 16 kafin naje nadawo" tajuya zata wuce cikin tsananin kunan rai Rahima tace "kece dai number 16 malama bani ba" ko juyowa Nurse din batayiba tabude kofa ta fita, Rahima tabi sauran yan dakin da kallo dake kallonta suna shiryawa ta murguda baki tace "bashi ko tara malamai?" taja tsaki ta finciki pant din batare data cire towel ba ta saka pant din tana karya tag din jikin pant din dake nuna sabone, fess pant din yamata sanan tadau wandon makarantan tana warware wa ta kalli fadin wandon fashewa da kuka tayi cikin fushi sosai tace "angaya muku ni matsiyaciya dazansaka wanan burgujejen wandon dakika dinga da kyallen tatan kamu? Bazan sakaba din" tajefar da wandon kan gado tana kuka sosai. Duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa. Daukan wandon Binta tayi tamika mata babu alamun wasa tace "sakashi" hawaye ta shiga sharewa tasaka wandon ahankali sanan ta warware towel din tadaura kan kafada ta dauko bra din tasaka, yamata daidai amma cups din bra sun mata kadan sosai hakadai tasaka tana tsaki almost half of her boobs sun taso waje, singlet din tadauka tasaka hakan sai yay balancing abin sanan tadau rigan tasaka tana kuka sosai, tazauna ta saka takalmin ta daure, daidai nurse din ta shigo tace "gud girl saura hijabin" cikeda tsiwa tace "baza'a sakaba din" da sauri nurse din ta daga hannu tace "maida wukan ba fada bane, dole dai kizabi daya ko hijabi ko hula, ga bakin hulan nan dukna hado miki, yi maza ki saka muje" juyawa tayi ta harari hulan kafin ta dauka tasaka ya bala'in yimata kyau, tai kyau sosai akayan bana wasaba, tai yar charas yar karaman nan nata aciki, nurse din tace "gakoshi kinyi kyau oya hada kayan tsaf ajaka muje na nuna miki wajen kayanki danke new comer ce daman saisa muka taru akanki, hada kayan tayi tana share hawaye sanan ta tashi sukaje har gaban dankareren wardore din wajen tanuna mata bangarenta ajiya kayan sukayi suka juyo, nurse din ta kaita har dakin detox babu kowa adakin, wani machine datagani mai wayoyi ajiki yasa da sauri tace "me za'amin anan wurin? Wai menekeyi anan ne?" ganin yanda tarude tana kallon machine din yasa nurse din tace "calm down dakin detox ne nan?" da sauri tana kwalalo manya manyan idanunta tace "detox? Mekuma detox?" ahankali nurse din tace "let's just say wankin ciki za'a miki" tura nurse din tayi tareda kwala ihu tace "uwar me cikina yayi da za'a wanke min, kasheni dai zakuyi, wayyo Allah na Mummy" ta fashe da kuka sosai tana turasu zata fita amma suka ki bata dama daidai wani Dr yafito daga wani daki yana yarfe ruwan hannunshi da alamu bayi ya shiga yana ganinsu da hannu yamusu alamu su zaunar da ita kan kujeran, daukanta chass Binta da Asabe sukayi suka zaunar da ita kan kujeran machine din, nurse din tazo da sauri ta kulle hannunta da belt din jikin kujeran, Asabe ta kulle kafafuwanta da belt dinsu datake ta shurewa tana ihu, ko motsi bata iyayi da hannu da kafafunta hakan yasa tafashe da kuka kaman zata mutu. "wayyo Allah na Mummy, Mummy, Mummy zasu kasheni, Abba, ya Siddiqa, na shiga uku na lalace, innalillahi wa innailaihi raji'un" dawowa tagabanta Dr yayi yace "calm down number 16, bakiso kar amiki?" da sauri ta gyadamai kai tana kuka sosai yace "to okay naji amma dena kuka in kinaso na kwance ki" shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta yace "gud, bude bakinki to kawai na duba saiki tafi" yay maganan yana komawa tabayanta, ahankali tabude mai bakinta tana sauke ajiyan zuciya, torch yadauka yana haska bakin yace "gud girl yanzun nan zaki tafi, rufe idanunki akwai abinda saikin rufe ido zan iya gani abakin ki kina rufewa zan gani kitafi". How to subscribe Pay 300 to my account number 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO Gyadamai kai tayi ta runtse idanunta gam, wani abu yasa yadaura akan bakinta bakinta ya kame sanan abun ya danne harshen ta ta yanda takasa motsi da harshen in anyway, da sauri ta bude idanun tana kokarin tai magana takasa, jikinta ko ina na rawa takasa motsi, ahankali Dr yace "I know, I know, just calm down bazamu wuce 30min ba zamu gama kitafi kije kici abinci okay just relax" yay maganan yana daukan wani farin pipe din roba yajonashi da machine din dake tsotso da washing toxin daga jikin mutum sanan yashiga yakawo bakin pipe din bakinta ya shiga turawa cikin bakinta yana kallon computer dake nuna mai inda pipe din yakai a cikin jikinta, yanda Rahima take zaro ido jikinta nabari zaka zaci zare mata rai akeyi sai wani irin nishi take babu halin motsi, saida yagama zura pipe din yakai har cikinta sanan ya danna wani button a jikin kujeran kujeran yadawo gado yazamto tana kwance, murmushi Dr dake tsaye kanta yayi yace "alright yanzu zamu fara are you ready number 16?" wani irin kyafkyafta idanu Rahima tayi da hawaye suka shiga fitowa, wani button Dr ya danna a jikin machine din pipe din bakinta yafara kara kaman irin ana zuko Bobo dake gab da karewa a goranshi, wani irin lankwashewa Rahima keyi hawaye na zuba daga idanunta, ita kadai tasan irin azaban datakeji, jitake yi kaman ana wanke cikin cikinta da sabulu ana dauraya, combination of uncomfortable and painful haka takeji kaman ana kasheta, almost 1hr Dr yadauka yana detoxing nata kafin ya kashe machine din yazaro roban ahankali ya ijiye, sanan yacire abinda yakama bakinta dashi kasama magana tayi sai ajiyan zuciya takeyi tana kuka, hannunshi yasa ya bude daure mata hannu da kafa da akayi sanan yasa hannu yadagota zaune tareda kwalamata Nurse kira da sauri ta shigo yace "take her to dinning tai having breakfast dinta and make sure she takes lot of water" gyadamai kai Nurse tayi takama hannunta tace "sauko mutafi" saukowa tayi tai luuu zata fadi da sauri Nurse ta tareta jitake kaman ba jikinta ba, tadaiga nurse din tarike ta gam an fitar da ita daga dakin wata nurse ta shiga da wata dakin, dinning Nurse din ta kaita ta zaunar da ita kan kujera, jiri ma take gani hakan yasa ta kifa kanta kan table din tana kallon mutanen dasuka cika wajen duk sun saka Uniform kaman ita sunacin abinci wasu na soshe soshe kaman mahaukata, daga ta Nurse din tayi ta ijiye mata wani abinci da in her life batasan sunan abincin ba, sai wasu kwayoyin magunguna a dan karamin rober tace "oya tashi kici kisha inba hakaba jiri zaita damunki, yi maza ci" ganin tayi kaman batajita ba yasa ta kwalama su Binta da Asabe kira da sauri sukazo wajen wani mugun kallo Asabe tamata tace "ci abinci" ahankali tadau spoon tafara cin abincin dataji amai ne kawai yake tasomata tanaci amma haka suka tasata agaba ta cinye da karfi da yaji sanan suka bata magani taci zata kwanta suka hanata danko kadan batajin dadin jikinta saida tai kusan minti goma zaune har lokacin idanunta juyawa sukeyi sanan Nurse ta dagata tace "muje kiyi bacci" kaita daki sukayi tahau kan gado da kyar sanan nurse ta rufa mata bargonta lumshe ido tayi tai shiru babu wani abu na jikinta datake jinshi daidai wani irin tausayi kawai taji tabama kanta hakan yasa ta fashe dawani mugun kuka tana shesheka ita kadai cikin bargo, Nurse ba tace mata komiba suka wuce suka fita, haka ta dinga kuka tarasa waya kawota wurin nan, bama tasan inane ba, tarasa ya akayi ina Mummy tasan cewa Mummy batasan tazo nanba, gashi sun kwakule mata ciki jinta take wani iri gabaki daya, she is so lonely, ga all matan datake gani da Uniform irin nata duk sai ahankali, soshe soshe taga sunayi,
Chapter 44 · 0% Book details