← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 119

Sashe 37

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aguje su Mummy da Siddiqa suna binta Abba ma na binsu dudda baya wani iya gudu sosai kaman su, Rahima kuma tai gaba chan wajen board tana jiran Zeenatu dan tamata passing kwallon, wani irin circling Zeenatu su Mummy sukayi dan dama batada gudu sosai dan tanada dan jiki tafi su Siddiqa kiba, ganin suna shirin kwace kwallon yasa tai tsalle tareda wani irin ihu. "Autaaa" chabe kwallon Rahima tayi Abba yace "wurga da sauri, wurga Auta" ganin haka yasa su Mummy suka kwasa da gudu sukai wajen Rahima kafin su karasa Rahima tai wani tsalle ta jefa kwallon cikin raga Abba da Zeenatu sukai ihu tareda rungume juna. "is a goal" wani irin tsallen dadi Rahima tayi tataho da gudu ta rungume team dinta Zeenatu da Abba, kafin ta sakeshi tahau rawa tana dariya Zeenatu ta shiga tayata suna rawa suna tsalle suna tafi, kama waist Abba yayi cikeda jin dadi yana kallonta yanda ta sake sosai tana murna rabon daya ganta haka harya manta, dudda he is super tired amma the whole basket ball idea was worth it look at his Rahima now, da gudu yakarasa wajen inda sukema us Mummy da Siddiqa da Lubabatu dasukai kini kini darai yace "who dares stand to Manchester? Am sorry yan Chelsea but Dady team is unbeatable right girls?" atare Rahima da Zeenatu sukace. "right Abba" suna wani feeling kansu, dariya Abba yayi ya rungumo Rahima a one side Zeenatu a one side of his hand, ya zare p-cap din Rahima yana kallon fuskan Mummy yana dariya yace "haba wifey, team dinku ar......" kaman ance ya juyo, Sameer yagani sanye da kayan sojoji ya tsaya jikin Gate rikeda car keys a hannu yana kallonsu yana murmushi, da sauri Abba yasaki yaran yana maidama Rahima p cap dinta akanta yace "laaaa Lieutenant, barka da zuwa" Lieutenant da Abba yakira yasa kowa yakalli Gate din, karasawa gaban gate din Abba yayi shima Sameer yakaraso Abba yamikamai hannu yace "welcome Sameer barka da zuwa, sorry fa, we were actually playing basket ball, halama ka kirani banji kiranba wlh" gyadamai kai Sameer yayi yace "I actually called twice" cikeda rashin jin dadi Abba yace "so sorry, yaran nan ne wlh muke basket ball, yau sunada mid semester ba school shine suka tasani agaba" murmushi Sameer yayi yace "what a nice family, hakan yakamata" dan dariya Abba yayi ya shafa bayanshi yace "tafi study room din bari naturo maka ita, kaganta chan" yanunamai Rahima dake sanye da p-cap itada Zeenatu suna rawa, kallo daya yamata ya dauke kai ya gyadamai Abba kai yafara tafiya, da sauri Mummy ta dunfaro su tace "a'a su soja ne agidan namu haka, yau munada manya manyan baki, aiko gashi ansha kayan sojoji an wanko kyau, and you know you look good da kayan fa, so handsome and se.....xy" tafadi ahankali ganin Abba yawuce zai kira Rahima dake raye raye, dan sunnar dakai Sameer yayi ganin ta babu mayafi yajuya yadan kalli Rahima dake rawa Zeenatu tagaji takama gwuiwa tabarta ita kadai tanata tikawa yace "good morning Mama" dan juyawa Mummy tayi ta kalli inda yake kallo ganin Rahima ne yasa taji gabanta yafadi tace "wanan kallo haka Sameer bazafa mubama soja ba, banda hakama Rahima yarinya ce, tuzuru irinka yakama min y'a ai saidai akirani ace ga gawarta abu ba kadan ba, irinka sai mata nunannu kaman su mu" tai maganan tana murmushi tareda dan lashe lips tana kallon fuskarshi, juyowa yayi ya kalleta ido cikin ido kaman maison karanta wani abu atattare da ita, Mummy jitake abu na tsayayo mata, tanason namiji dakakke jarumi haka, yanda Sameer ya kalleta cikin ido babu wani alamun darr ko tsoro yasa taji organs din jikinta sun mike, Lord! She is crushing on this sexy giant guy, dauke kai yayi yafara tafiya yace "excuse me Mama" da sauri Mummy tabishi tace "haba Sameer da shekaru nawa na girmeka duka duka yar yarinya dani eh Sameer kake cemin Mama?" dan kallon Mummy yayi kaman yanda ta zubamai idanu itama ta tsaya chak tana wani irin murmushi jitake kaman tajawo shi ta rungume shi. "Wifey" Abba ya kwala mata kira da sauri ta juya yana tsaye tareda su Zeenatu ga Rahima kuma ta taho tana tafiya ahankali tana tahowa, da hannu yamata alamu datazo yace "zomu cigaba wifey" dan batarai tayi tadan harari Rahima dake tahowa tana kallonta sanan tawuce batare dataima Sameer sallama ba dan ko kadan bata so Abba yakirata ba, tsayawa Sameer yayi yana kallon Rahima dake tahowa tana kallon Mummy tana murmushi sosai duka white hakoranta awaje, fadawa jikin Mummy tayi ta kyalkyace da dariya sosai ganin Mummy ta daure fuska tace "Mummy na are you sad we won?" dan tureta Mummy tayi tace "common leave me alone, go and hug your team leader tunda har kun iya cinmu" fashewa da dariya Rahima tayi data dade batai irin shi ba ta kankame Mummy ashagwabe tace "kai Mummy na, inda kunefa kuma da kunci mu muyita jin haushi, kai Mummy wayau ko" takara kyalkyace wa da dariya tana chusa fuskarta kan kirjin Mummy kaman wata yarinya maishan nonno tana dariya, juyawa da Sauri Sameer yayi yadauke kanshi yawuce study room this is the first time yake ganinta so happy like this, kwala mata kira Abba yayi ganin shirmen dasukeyi da mamanta. "Rahima bazaki wuce kitafi ana jiranki ba" da sauri tasaki Mummy tai hanyar study room dinta da gudu, hannu tasa tabude kofan da sauri ta shiga, hada ido sukayi da Sameer din dake zaune kan kujera yadago kai yana kallonta, ahankali tace "good morning" dauke kai yayi daga kallonta hakan yasa ta tabe baki tawuce ta zauna kan kujeran gaban table din Abban tai shiru tana karkada kafafu.28. Free page Tana karkada kafafun ta dake sanye cikin sneakers, kafe kafafuwan nata yayi da ido yanda right leg wrist dinta ke sanye dawani hadadden leg chain dayama tiny leg din nata kyau kaman ka sace, batare daya kalli fuskarta ba yace "mesa kike saka leg chain?" kallon kafafun nata tayi kafin tasaki murmushi tace "sabida ina sonsu ne, sunada kyau" zai kara magana wayanshi yadau kara hakan yasa yaciro wayar daga aljihu ya kalli screen din sanan yay picking yakara a kunnenshi batare dayay magana ba but da alamu sauraron maganan dayan bangaren yakeyi, dan dago fuska Rahima tayi ta kallai, kayan sojojin sunmai wani irin shegen kyau, bakin fatanshi na shining yana daukan ido, pink lips dinshi ta kafe da idanu shi kadaine abu dan jajja jajja a fuskarshi aranta tace wai mesa yawanci sojoji bakake ne, ahhh dark men are ugly, dan fari zan aura inna tashi aure sunfi kyau, dago idanunshi yayi karaf suka hada ido, dan zaro fararen eyes dinta tayi cikeda rashin gaskiya gabanta yawani irin fadi, batare daya cire nashi idanun daga kanta ba yay magana yace "Alright ganinan zuwa" zare wayan yayi daga kunnenshi yana kallonta, cikeda rashin wasa yace "why are you looking at me?" dan turo baki tayi tana kallon nashi cike da rashin gaskiya kafin tawani irin washemai baki ta kyalkyace da dariya tareda tashi da gudu tai kofa, da sauri yakirata. "Rahima" juyowa tayi ta kallai tana kokarin bude kofa tana murmushi, dan sakin fuska yayi kadan ganin yanda takemai murmushi yau she seems very happy. "come" makemai kafada tayi tabude kofar da sauri tafita, tashi yayi yafito batawani nisa da study room dinba yakirata. "Rahima" da sauri tajuyo sanin su Abba na iya juyowa and Abba yana ganin yakirata bata amsaba fada zai mata, yaga ana kiranta taki zuwa yasa ta juyo da sauri, alamu yamata da hannu datazo inda yake, takowa tayi ahankali ta taho ta tsaya har gabanshi ta daure fuska, Mummy dake buga basket ball sai satan kallon su zuciyata na bugawa bim bim bim. Karasowa tayi har inda yake agaban dakin, kaman 5 feet tsakanin su ta tsaya yanda yake kallonta yasa tadan juya ido tareda wani lankwasa kai tace "ni gani me kake kirana?" shiru yayi yana kallonta, ahankali cikin low voice yace "ni kikema dariya? Wats funny about me?" yafada babu wasa, dan juyowa tayi ta kallai kaman yanda shima ke kallonta, wani irin murmushi ta sakinmai duka white kananun hakoranta suka bayyana tace "su Mummy ne suka bani dariya ni ba kaiba, wai dan mu Team Dady Manchester munci shine suke fushi sunata hararan na sabida ninaci ball din, kaga ko na iya basketball tun a school Inna karbe ball din saina wurgashi cikin raga sanan zasu sake iya rike ball din, sabida wai Ya Zeenatu tamin passing ball din aiko su Mummy, da Ya Siddiqa da Ya Lubabatu suka biyoni da gudu, na daka wani high jump and throw the ball sai cikin basket and it was a goal, shine suke fushi hahahahha" takara kyalkyacewa da dariya tasa duka hannayenta kan bakinta tana rufe baki tana dariyan harda hawaye, shiru yayi yana kallonta she looks so innocent, so cute while laughing, yanzu dai wats funny acikin wanan labarin datake bashi tana dariya, this is the first magana datamai batare daya tambayeta ba tana uban dariyan nan kaman zararra, murmushi zaiyi amma yahana kanshi dan smirking yayi yasa hannunshi cikin aljihun gaban riganshi yaciro wani dan karamin card ya mika mata, tsayar da dariyan tayi ta kalli card din dayake mika mata tace "menene wanan?" ahankali yace "is my card, just keep it with you, anytime dakike da any problem, ko u are sad or anything my digits are there just give me call" daure fuska tayi tace "why will I call you kaida baka ma mutane dariya, fuskan ka kini kini kaman wani mala'ikan mutuwa Astagafurullah" wani irin kallonta yayi kaman mai shirin tuhuman ta yace "kintaba ganin mala'ikan mutuwa ne?" girgixa mai kai tayi batare data kalli fuskanshi ba tace "ai Mummy naji tana cewa basa dariya kuma baka dariya" dan shiru yayi hakan yasa tajuyo ta kallai hada ido sukayi, strictly yace "idan na bama mace abu dolene ta karba so take it" yanda yay maganan kaman magic ahankali ta mika hannunta ta karba ta tusa a aljihun bayan Jean din dake jikinta, tace "uhm kanada sisters?" fara tafiya yayi tabishi da sauri tace "to kamin shiru nace kanada sisters?" gyadamata kai yayi. "eh inada sisters 5" tabe baki tayi
Chapter 37 · 0% Book details