Sashe 6
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
alamun wasa akan fuskarshi yasa tai shiru, cikin kakkausar murya yace "Rahima nahanaki yima yayyunki rashin kunya koban hanaki ba?" cikin kuka sosai tace "wlh kahanani Abba" gyadakai Abba yayi yace "bance miki kidinga kifitowa kuna aikin gida tareba" cikin kuka tace "kacemini haka Abba" ahankali Abba yace "good, ban hanaki yawo agida da towel ba?" fashewa dawani irin kuka tayi sosai tace "e....e..h kahanani Abba" "bance kidinga fitowa kuna salla tare da yan uwanki kullum ba?" gyadamai kai tayi hawaye kaman anbude dam tace "kacemini Abba" cikin kakkausar murya Abba yace "laifin ki nawa kenan?" cikin kuka tana kara mikama Mummy dake tsaye gefen Abba hannu tanaso tariketa tace "laifina hudu Abba" shiru Abba yayi ayanda yakejin haushinta inyace yamata hukunci da fushin nan zai iya yimata illa, he is just trying to calm himself down, ajiyan zuciya zuciya yasauke yace "jeki dauro alwala kizo nan kiyi salla agabana inkinga dama ki kara dawomin nan da towel, tashi daga nan, will you get out of my sight ko saina saba miki!" ya daka mata tsawa da gudu ta tashi tai ciki tana kuka sosai, cike da kunan rai Mummy tace "Alhaji dan Allah kadinga yimata ahankali...." "don't tell me rubbish Maryam!" Abba yadaka mata tsawan da saida yasa tai shiru da sauri, cikin fushi yace "I said don't tell me rubbish Maryam! while kullum ina fita nema dan na wadataku keda yayan mu, nabarmiki duka yaran nan namu amana, ke kina nan kina lalata Rahima, babu wanda Rahima ke gani da daraja aduniyan nan, bata ganin kowa da gashi, could you imagine saidai mai gadine zai kwaso mata kayan data shanya which am sure bama ita ta wanke suba, kina gidan nan tareda dukansu kin kasa sata tai salla me amfanin kito eh amatsayin ki na mahaifiyarta? An gayamiki Rahima yarinya ce har yanzu? Allah zai tambayeni dagani harke kan yanda muka bama wayan nan yaran tarbiyah" yanuna mata duka su Siddiqa da kansu ke kasa ganin ran Abba yau yabaci yanama Mummy fada which of course sunsan she deserves it, Abba yacigaba yace "yaran nan matane, idan bamuba Rahima tarbiyah ba intai aure me zata bama nata yayan iyye? Wani irin hali kikeso taje tana nunawa agidan mijinta, angayamiki zata dawwama tana rayuwa damune? Dazu da rana awurin aiki Aminina yasamen da magana dayamin zafi yamin ciwo amma nasan alkhairi yake nufi dani da bazaizo yamin maganan ba" yadanyi shiru yana sauke ajiyan zuciya sanan yace "yau zai taho aiki yabiya ta school dan ijiye su Aisha da Hafsat a school yaga driver ya sauke Rahima tana sanye da Jean fa da t-shirt sai dan ficicin gyale akanta rabin gashinta awaje agabanki yarinyar nan tai shiga kaman yarinyar arna ta tafi makaranta haka baki hanata ba, idan kinsan bazaki iya bama yarana tarbiyah ba zanje na auro wacce zata basu, this children are my life, gift din da Allah yabani ne inhar zan fita nema nabarki dazu bazaki koyamusu abinda yakamata ba wlh zan iyasaka konawane na auro wata matan inhar ta yarda tai na'am zata bama yarana tarbiyah nagayamiki" faduwa gaban Mummy ya shiga yi, tasan halin mijinta tsaf kaifi dayane wlh kuma zai iya aikata hakan, babu abinda ta tana aduniyan nan kaman kishiya, ahankali ta tsugunna tareda kama hannunshi tashi Siddiqa tayi daga wurin hakan yasa sauran yaran ma duk suka tashi sukai dakinsu, cikin damuwa sosai Mummy ta damke hannun Abba ahankali tana kallon fuskarshi tace "nai kuskure baban Siddiqa, amma kayakuri, ka gafarce ni zan gyara, ka gafarce ni dan girman Allah karkace zaka karo aure sabida tarbiyah yara, bagasu Siddiqa ba banine nabasu tarbiyah ba duk nice ko, to kayakuri dan Allah" tai shiru tana kallonshi ganin yaki kallonta har lokacin bala'ine bayyane karara akan fuskarshi yasa ta fashe da kuka mara kara sosai ta yanda yaran bazasu jisuba irin kukan nan mai karya zuciyan miji, cikin kuka tace "nayi kuskure, na yarda nai kuskure, Alhaji inason Rahima dayawa ne, ina son yarinyar nan sama da tunanin ka, saisa bana iya mata fada, burina aduniyan nan shine kome yarinyar nan keso tasameshi shikenan burina, banson naga tana cikin damuwa ko cikin bakin ciki, yayyunta kyaranta sukeyi taita kuka, kaima fada kake mata kullum taita kuka, ni inban jata jiki ba abin zaimata yawa she is too small, kowa Rahima, kowa Rahima, komi Rahima, Rahima tai kaza tai kaza, ni kadai Mummy ta ke lallabata najata jiki, na sanyata murmushi amma kayakuri bazan karaba nai kuskure mijina kayafe mini" tafashe da kuka sosai, ba karamin sosa zuciyan Abba kalaman ta sukayi ba kasa daurewa yayi yajuyo ya kalleta ganin yanda take kuka yasa yasa hannu yadago ta yace "tashi kiga bar kukan hakanan, yi shiru" ya zaunar da ita gefenshi, hannunshi yasa akan fuskarta ya share mata hawayen tasa kafin yakama hannayenta yahade su waje daya, cikin wani yanayi na damu yace "you are getting me wrong Maryam, baki fahimce magana taba, listen I appreciate irin son gaskiya na tsakani ga Allah dakike ma autan mu, nima inason Rahima sama da tunanin ki fadan danake mata danta gyara dabi'un tane, yaro bazai dinga kuskure ba kadinga mai dariya kana nunamai yay daidai ba, inkai hakan cutar da yaron kake, I know daman u as the mother yakamata tadinga samin kwanciyan hankali da happiness a wajenki wanan bakiyi karyaba, abinda nake kokarin nunamiki anan shine ki dinga sata tanayin the right thing, Rahima tadena fita babu hijabi, babu mayafi, haramun ne a musulunci tana bayyana surarta, idan wani abu yasameta fa? Idan surarta ya burge wani da baida niyya mai kyau yay mata fiyade fa? Kinyi wanan tunanin? Ki hanata rashin kunya, sanan kidinga sata tana salla akan lokaci, aduk lokacin dasu Siddiqa zasuyi girki kidinga sasu dukansu ba ita taje ta kwanta ba suje suyi girkin tare, gyaran gida tare, wanki tare, su dinga all house chores tare, yarinyar nan babu abinda ta iya kinga hakan bai daceba kin gane nufina yanzu?" yay maganan yana shafa kumatun ta yanadan murmushi, gyadamai kai tayi itama tana murmushi tace "hakane zan gyara i promise you dan zinare na zakaga chanji" dan dariya yayi yace "ina sonki sabida kina daukan gaskiya, am sorry namiki ihu gaban yaranmu kinji, kiyakuri I was angry then ne yar Zinariya ta" girgixa mai kai tayi tace "bakomi yawuce" motsi dasuka ji yasa suka waiga Rahima ce tafito sanye da wani dogon pink hijabin ta da dadduma a hannu idanun nan sunyi jajir fuskarta duk ruwan alwala, daure fuska Abba yayi yace "shimfida dadduman kihau kiyi sallan kigama kizo" wasu sababbin hawayen dasuka zubomata ta share tana kallon Abban tace "dan Allah Abba karka dakeni kaji dan Allah, please Abba na" wani bakin kallon dayamata batasan lokacin data shimfida dadduma da guduba tahau kai ta kabbarta salla, ganin bamata da natsuwa yasa Abba yace "ki natsu kiyi sallan nan da kyau" kallon Mummy dake gefenshi yayi duktai wani irin kala tana kallon Rahima dake salla, hannu yasa yajuyo da fuskarta ta kallai dan murmushi yamata yasan ta damune yace "kawomin abinci naci, kiramini yarana sufito muci tare, dazaran naci zanyi wanka natafi study room yau zanyi kusan rabin dare achan akwai wani case danake aiki akai" gyadamai kai Mummy tayi ta shiga tai ciki dan kiran yaran shikuma Abba yamaida hankalinshi kan sallan da Rahiman keyi ganin tanayi komi da kyau yasa yadan sauke ajiyan zuciya ya shiga yimata addu'an shiriya da chanza wa a ranshi. Fitowan su Siddiqa yasa yajuya yana kallonsu kitchen duk sukayi harda Mummy suka shiga fito da kulolin abinci da tray, bajewa sukayi akasan babban falon Mummy tafara serving Abban su kafin ta zubama yaran, sallame sallan Rahima tayi ta jingina da kujera tana kallonsu duktai kalan tausayi, taba Abba Mummy tayi tace "dan Allah kayakuri Abban su aikin tubako Auta bazaki karaba ko?" gyadama Mummy kai tayi tana share hawaye tana turo baki, murmushi Mummy tayi ta kalli Abba tace "kagani bazata karaba, oya bama Abban ki hakuri" ahankali cikin muryan kuka tana kallon Abban tace "kayakuri Abba bazan karaba" murmushi Mummy tayi tana washe hakora tana kallon fuskan Abban daya daure batare dayace mata komiba tace "yauwa Auta na dena kuka Abban ki yahakura, bama yayyin naki hakuri suma" kallonsu tayi kaman yanda suke kallonta hawaye ne yazubo daga idanunta ta share sannan tace "kuyakuri" murmushi Siddiqa tayi tace "yawuce" murmushi Mummy tayi tace "yauwa oya zo wajena" kaman jira take da sauri ta tashi tazo tafada jikin Mummy tana rera kuka ahankali, Abba bai kara cewa komiba yacigaba dacin abincin shi yanajinsu yanda Mummy ke lallashinta, saida yagama sanan yatashi yafita daga dakin motarshi yaje yabude baya wani babban leda yadauko na Teems Pestry shop gabaki daya bacin ran da Rahima tasa shi yasa yama manta da tsaraban daya sayo musu sanan yadawo daki, Mummy yabamawa sanan yay corridor dan zuwa wanka ganin ana gab da kiran magrib, ice creams ne aciki Mummy tabude, murmushi tayi taciro biyu ta mikama Rahima dake jikinta tace "iyye kinga ice cream dinku jekisaka a freezer yay kankara kaman yafara narkewa anjima sai kidauko kisha" ahankali tasa hannu ta amsa ta tashi tai wajen fridge sanan Mummy ta cicciro daya daya ta mikama sauran yaran duk karba sukayi basu cemata komiba dan inda sabo sun saba kome Abba yakawo na Rahima double ne nasu dai dai, sawa a freezer tayi tadawo zama tai kusa da Mummy tai lamo akan hannunta, ahankali Mummy tace "nazuba miki rice kici" girgiza ma Mummy kai tayi tana yatsine fuska ko kadan batason cin abinci, abinci ma baya mata taste abaki yanzu, shiru Mummy tayi tana kallonta sanan tace "ankira magrib yi saikije dakina ki jirani zanje wajen Abban ku" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali tai dakin Mummy duktai wani irin yaushi. **** _*BIN ABINDA ZUCIYA KESO*_ _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favour you always