← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 119

Sashe 79

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sunanta dawata raunanniyar murya ita kanta Ummi tasan tai kewan danta but Sameer go against maganan ta tanunamai batason yarinyar nan amma ya aureta saisa ta sallama shi haka akema yara marasa jin magana da taurin kai. Ganin taki kulashi yasa yadaura kanshi saman hannunta yay shiru itama kasa korashi tayi duk sukai shiru, lumshe ido Ummi tayi kafin tabude su ahankali jin saukan hawaye kan hannunta, cikin wani yanayin bakin ciki tace "Sameer kanuna min niba komi bace, ban isa dakai ba, Baffan ma da matarshi basu nunamin komiba amma kowa na family nan yasan yanda Asiya ke sonka dudda kuwa bata fadiba, dataji batun aurenka bakaga rashin lafiyan datayi ba kaman zata mutu, yau dataji za'azo nanne ma tasami kuzari haka, har kunyan kallon iyayenta nake sabida abinda kayi ka gwammace ka auro yar shaye shaye daka auri kanwar ka da aka haifa agaban ka kasan kalan tabiyan ta , yarinya natsassa mai hankali" ayanda ta karashe maganan zakasan abin yamata ciwo sosai, ahankali Sameer yadago kanshi bayan yagoge hawayen dasuka zubomai kanshi akasa yace "Ummi kiyakuri kiyafemin, wlh bazan iya auren kanwata bane saisa" "ai naga wanan yayarka ce" girgiza matakai yayi yace "am sorry Ummi, kinji please nasan namiki laifi banmasan mezance ba, please kiyakuri Ummi, am dying inside kidena fushi dani kinji"._BIN ABINDA ZUCIYA KESO_ _How to subscribe_ _zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO, Marasa bank can also send MTN card 300_ "p....ls Ummi.....na" yay maganan muryan shi na breaking sosai, sosai Ummi taji she can not longer go on with this fight, tai missing Sameer dinta bana wasaba sauran yaran basa wani kula da ita kaman yanda Sameer ko tarinta yaji sai yace me kikeso Ummi, Sameer always put her first, dagokai tayi ta kallai ahankali irin kallon nan nayaya zanyi dakai hakan yasa Sameer yakama hannunta yakai kan fuskarshi ya lumshe ido, sharrr wani hawayen yazubo daga idanunshi, wani irin jawoshi Ummi tayi tasashi ajikinta ta rungume tana kokarin hana kanta kukan datakeji tace "sabida kaga ina sonka ina dagama kafa Sameer saisa kakemin duk iskanci da kaga dama, kanamin kashi da fitsari akai, for 39yrs kaki yarda kai aure sabida yanda nake sonka nakasa maka dole dan banson kayi rayuwa da abinda bakaso saisa koda kanunamin bakason Asiya ban zafafa abinba dan nasan ba'ama namiji dole, ya auri macen dabayaso wahala zatayi, shine zakaje ka auromin yar shaye shaye listen I might, might forgive you but I will never accept yar shaye shaye as my daughter in law nagayamaka, and stop crying, you are my Soja crying is for the weak men and my boy is not weak right?" gyadamata kai yayi ahankali yana dago kanshi daga jikinta, hannunta tasaka ta sharemai fuskan tass tai murmushi ganin kaman bashiba tace "is alright nahakura amman as far as am concern baruwana da yar shaye shayen daka auro" hannun Ummi yakama ahankali yana kallon fuskanta he don't know why but anytime aka kira Rahima da yar shaye shaye he feels bad, zuciyar shi batamai dadi, ahankali yace "tadena Ummi, am changing her bazata karaba, ko damaba badan kanta tayiba...." tabe baki kawai Ummi tayi tadan tureshi alamun batason maganan batare data cemai komiba, kwantar da kanshi kan cinyarta yana sauke ajiyan zuciya sosai taji yabata tausayi ahankali ta shiga bashi head massage tana tunane tunane ahaka bacci yay awon gaba da shi awurin. Nabila data shigo daukan ma princess apple daga fridge din Ummi ne taga Rahima ita kadai afalon tana share hawaye da bayan hannu tausayi tabata sosai, Apple din tadauko tadawo inda take tace "Amaryan mu tashi muje shashin mu duk muna chan" ta dauketa ta tafi da ita chan flat din Noor dasuke ciki da ita, su Noor ne a falo da Muhammad da Mu'az sai Asiya duk suna buga game da sabuwar ps6 din da Sameer yasaima Mu'az, suna ganin Rahima duk suka natsu wani natsu suna wani murmushi adole ga matar yayansu ta shigo, Daki Nabila tai da Rahima inda Fadila ke tare da yaransu tana musu wasa, zama duk sukayi sukahau hirada ita suna janta da magana amma takasa amsasu sai kallon kyawawan yaransu take dudda yaran duk Black beauty ne dan iyayensu bakake ne amma sunada wani irin kyau da kiba da kana ganinsu sai sun baka sha'awa, har azahar daga bayama bacci ne ya kwasheta ganin tana gyangyadi yasa Fadila tace "ki kwanta mana Rahima kin zauna kinata gyangyadi" gayamata kai tayi tacire katon gyalen daya isheta taijiye a gefe ta kwanta ahankali tareda daura kanta afilo sai bacci, dauke kai Fadila tayi daga kallonta ta kalli Nabila dake rikeda Princess datai bacci tace "wlh ina bala'in sonta, ni yarinyar burgeni take gashi batada magana shiru shiru, I trust Ya Sameer nasan komi yazo karshe tunda dai ta shigo hannunshi" Nabila tace "hakane, ga kyau kaman ita tai kanta kinmasan menene Fadila, anytime inna kalleta sai naji tana tunamin da Ummi, sai inga kaman tana yanayi da Ummi intai wasu abun saikuma inga kaman idanuna ne kemin gizo hala sabida ina tausayinta ne" dan dariya Fadila tayi tace "nikuma kinga bangani ba, bari kiga naje wajen Baby tun dazu bansashi a ido ba" hararanta Nabila tayi tace "wato yanzu kinsaba babu zancen kuka da tsoro kuma ko" kyalkyacewa da dariya Fadila tayi tace "wuce nan, ai tunda na haifo Amra nasan kar harkan shi kanshi Baby yanzu mamaki yake wai ashe zan taba dena kuka" dariya Nabila tayi tace "adaiyi ahankali Amra is just 2month plus kafin kije kiyo mata kani ko kanwa jarabatu" dariya Fadila tayi tafice daga dakin falonsu tayi daidai dukansu ukun na shigowa dan masallaci sukaje wajen Muhammad tayi ta mikamai Amra tareda kama hannunshi tarike tana kallonshi, murguda baki Mu'az yayi yana kunkuni yace "akama anata lalatamu ana soyayya agaban yara" da sauri Muhammad yace "mekace?" washe baki yayi yace "ni ba dakai nakeba" murmushi kawai yayi ya kalli Fadila yace "muje flat dinmu I want to sleep" ficewa sukayi, Noor ya kalli Asiya dake kallo abinta yace "Asiya je ciki kicema Nabila ta samen in my bedroom" tashi tayi da sauri cikeda girmamawa tace "to Yaya" dakin tabude ta shiga kallo daya tama Rahima dake bacci tadauke kai ta kalli Nabila tace "Anty Ya Noor yace kisamai in his bedroom" murmushi kawai Nabila tayi tace "ganinan" tashi tayi ahankali gudun kar Princess ta tashi ta kwantar da yarinyar kusada Rahima sosai sai sukai kwanciya kaman uwa da y'a na bacci sanan tai murmushi tajuya tafita daga dakin tareda maido musu da kofa tarufe. Wuraren la'asar Rahima ta farka daga bacci tana dan mika ganin yarinya a kusada ita tana bacci hankali kwance yasa tasaki murmushi tana kallon yarinyar kafin tamika hannu ta taba kuttubeben kumatun yarinyan tana dan murmushi sanan ta janye hannunta ta tashi ahankali tazauna, idanunta ne suka sauka kan wayan Nabila dake ijiye kan side drawer, wani irin faduwa gabanta tayi ahankali tace "Mummy na" waigawa tayi ta kalli kofar dakin ganin a kulle babu kowa yasa dasauri tasauka daga kan gadon, wayar tadauka tana kallon kofa saikuma tayi kofan data tabbatar cewa na bayi ne ta shiga, maida kofar tayi tarufe tasa sakata sanan tabude wayan tana addu'a Allah yasa ba password aiko taga babu, number Mummy ta shiga sakawa hannunta har rawa yake tai dialing number saidai harya gama ringing ba'a dagaba, sake dailing tayi akaro na biyu wayan na gabda tsinkewa aka daga kafin Mummy tai magana tace "Mummy nine Auta, call me please kar agane nakiraki in kudin wayan yakare" jin muryan Rahima yasa da sauri Mummy tace "to to" katse wayan tayi takirata back da sauri Rahima ta dauka muryanta narawa sosai tace "Mummy na ya jikin ki kinji sauki?" murmushi Mummy tayi tana shiga daki ta maida kofar ta tarufe harda saka key gudun karajita ta shiga bayi tace "awwwn don't worry about me naji sauki, I have to be strong 4 u Rahima na, ni kadai ce on your side in this whole planet I need to help you, ya kike" kasa amsawa Rahima tayi tafashe da kuka sosai tana tuna yanda jikin Mummy yayrudu rudu tace "Mummy na are you sure kinji sauki? Narasa yanda zanyi nakiraki banda waya I've been so worried bama na iya bacci da kyau, Mummy nagaji da komi ke kawai nakeso nagani, Mummy please help me wajenki nakeso nadawo am not happy at all Mummy, kaman ina cikin keji tareda aljani nakeji am so scared of him sabida karya zaneni, Mummy nima ranan saida yazaneni sosai sai jiya jikina yadena ciwo" tafashe da sabon kuka, cikeda damuwa Mummy tace "Rahima Rahima, Autana" ahankali Rahima tace "uhm" cikin kuka, cikin makirin voice dake kara dulmiyar da Rahima tace "listen to me Autana inhar ina rate aduniyar nan wlh babu wanda ya isa ya wahalar min dake, ba dukana ba ko kasheni Sameer zaiyi I must come and get you kuma gobe da shirina zanzo kema ki shirya kinji" da sauri Rahima tace "to Mummy" ahankali Mummy tace "anya kinsha abubuwan nan kuwa dan inda kinsha daban jiki da mugun sanyi hakaba, Auta na danasani dakeda tsiwa bata tsoron akwana balle tai yami, bakida energy, babu inspiration bakida vibe u sounds so dull, anya kinsha kuwa?" girgixa mata kai Rahima tayi tasa hannu ta goge hawayen daya zubomata ahankali tace "nakasa sha Mummy, inya kamani nasha zai iya kasheni wlh, Mummy mugune shi sosai gashi katoto, ko karkashin gadon banma kara lekawa ba tundaga ranan" sosai Mummy taji badadi ko kadan bataji dadin rashin shanta ba dan wanan mix din ko kaffara bazatayi ba in Rahima tasha sai kwakwalwanta yajuya irin mix dinan ne da yan shaye shaye nasha shikenan kuma saiya taba brain dinsu su haukace combination of crack ne da indian herm saikuma wasu kwayoyi da ake kira _Tsigai tayi yami amma sai bala'i aiki_ tun ranan data kawo take kasa kunne taji an kwantar da Rahima a hospital amma taji shiru rasa yanda zatai tai magana da itane yasa kawai tai shiru ta zubama sarautan Allah ido, danne zuciyarta tayi tace "yamiki wani abune ya sadu dake?"
Chapter 79 · 0% Book details