← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 119

Sashe 48

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaunar da Rahima ta kwanta tana bude idanunta tana kallon kowa, zama matar tayi takalli yaran dasuke tsaitsaya suna kallon baban nasu duk maza gabaki daya kansu daya kaman yan shidda ta haifa, sai wani babba da yake sanye da kayan fulani da tsayinshi daya da Mairo wacce take itakadai ne mace ayaran, sai wanda ake bama nono shima namiji yakama yara Tara cib cib, yaran kaman bakwaini, anatse Habu yace "kinga wanan shine Alhajin danake fadamiki daya bani aiki a binni" da sauri takama baki tace "laaaaa shine baka gayamin ba ke Mairo kawoma Alhaji fura dan Allah yasha" da sauri Abba batare daya dago kai ya kalleta ba yace "a'a kibarshi nagode, magana nazo nayi dake dan yanzun nan zamu koma" da sauri ta gyara zama tace "to to ina jinka" Ahankali Abba yanuna Rahima dake kwance kusadashi databude idanu tarr tana kallon kowa awurin yace "nakawo miki y'ata ki rikemin ita na tsawo wata shida ne, kisamata tsaro bana wasaba, banda haka zan biya ki kinji, sanan zan aiko muku da kayan abinci gobe, dan Allah zaki rikemin ita?" da sauri tace "Alhaji harda su biya? Nawa zaka biyani to dan kaga yar bukkan mu tamana kadan nida yara Tara gakuma ta goma ta kawomana, dole sai....." da sauri Habu yace "Ladi" hannu Abba yadaga mai yace "barta, nawa ake Gina bukka anan?" ahankali tace "sun karamai kudi da muttala hudu ne yanzu muttala goma ne wlh wasuma har muttala shadaya suke karba" bandir din yan dubu guda biyu Abba yaciro yamika mata yace "ga dubu dari biyu agida bukkan na block amuku ginin sanan sauran kudin ki rike, ki kulamin da ita, gatanan gakuma kayanta intai ba daidai ba ki gyara mata, amana nabaki ita dan Allah kar wanda yanuna mata hanyar barin garin nan nasan ko zata shekara bazata taba ganewa ba" rudewa kam Ladi tarude karshen rudewa ma ganin uban kudaden da Abba yabata kaman a mafarki, dama sune yan gayun kauyen nan sabida Baban su Safara dake aiki a binni yanzu kuma ga wayan nan kudin ga yarinyar binni ai bakanta, da sauri tace "wlh, wlh, wlh na dauka zan kula da yarka na rantse da Allah, amana na dauka halak" ta kalli Habu tace "kagayamai komi kan kauyen ko?" kafin Habu yay magana Abba yace "ya sanar dani kuma dama irin kauyen nan nakeso ta zauna aciki, kome yataso ayi badamuwa wlh nan da wata shidda zanzo na dauketa" murmushi tayi tace "masha Allah, Allah yakusan bamu jika kenan" murmushi Abba yayi dan baigane hausan nata sosai ba yace "to mun tafi, Habu tashi mutai" wani irin zabura Rahima tayi ta tashi tsaye tana kallon Abban daya tsaya yana kallonta tace "Abba ina zaka ka barni anan? Su waye wayan nan?" ko kallonta Abba baiyiba dan baimaso yay magana da ita tsabagen haushin ta dayakeji yace "Ladi ariketa karta biyomu muntafi" mikama Safara yaron hannunta matan tayi takama Rahima gam tarike hakan yasa Rahima ta shiga kokawa da ita amma takasa koda fizge hannunta dan kashin Ladi yafi na rodi karfi, ganin takasa kwatan kanta yasa ta fashe da kuka tana kwalama Abba kira. "Abba meyakawo ni nan? Su waye wayan nan? Abba ina zaka ka barni eh? Ina mummy na Abba? Abba kaima ka tsaneni kaman mamana ko? Ka kaini chan wani wuri da bansan su ba yauma kasake kawoni wani wuri daban San kowa ba? Abba waime namuku da babu wanda kesona? Abba katafi ka barni kuma? " Abba yanajin duka kalamanta dudda sun mugun tabashi amma yadaure ko juyowa baiyiba har suka bace mata daga gani yanaji tana kuka tana kwalamai kira har suka shiga daji yadena jin kukan ta. Saida sukaga sun bace bat sanan Ladi tasaketa ta kama hannunta gudun karta gudu tace "kinga muje daki dare yayi kiyi bacci yarnan" fashewa da kuka Rahima tayi tace "dalla chan kisaken ni" janta Ladi tayi tai cikin yar bukkan da ita yaran suka biyosu duk suka shigo ciki, dakin babu komi sai kwanuka da aka jera irin kwanukan da dinan masu kama da langa tuwo da miya, sai asabari da aka shimfida akasa, sai buhun simenti da taga lodi lodin kaya aciki kaman kayan sawan sune, dakin zarnin fitsari, washe baki Ladi tayi ta zaunar da ita kan as abari mai kyau tace "sannu da zuwa yar binni" ta kalli Mairo data zauna kusada ita tana kallon Rahima kaman zata hadiyeta tace "kawo ma yar binni fura da nono tasha" make musu kafada Rahima tayi tace "baza'a sha kazamin fura da nonon ba" da sauri Mairo ta kalleta tace "kika karama Maman mu rashin kunya saina fasa miki baki aradu" babban namijin ne daya shigo da akwatin Rahima yana wasa da tayoyin kafan trolley yadago kai ya kalli Mairo yace "dalla to dake tayi ki wuce kakawo mata furan akace" kwafa Mairo tayi tai wajen randa shikuma saurayin yataho kusada mamansu ya zauna yana washe mata hakora yace "mama dan ban wani abu man cikin kudin" hararan shi maman tayi tace "to sannu tunda ina tsoron kane Maccido, kaga gobe da safiyan Allah Mairo zataje saro mini gyada da masara, su Tasallah zataga nariga nafita ne wlh, na kece raini, sari zanyi na kece raini na azo agani, saina siye amfanin gonan tass saidai suzo suna siya awurina" furan Mairo takawo ta ijiye mata a gabanta Rahima tasa kafa ta shure furan yazube da sauri Ladi tace "ke yar binni zanci miki kaniya fa, huran kika zubar, yasin zan batamiki raifa, Ke kauyen nan ba'a haka mai wulakanta abinci kyalli madam na zuwan mai da daddare wlh barina kiga yanzun nan zaki gansu sunzo, munada dodanni kala kala, akwai abubuwa agarin nan da inhar zaki kwantar da kanki muyi zaman lpy zan kareki inkuwa kince a'a barinki zanyi, dama kin ishi ubankine daga gani yakawo minke riko" hararanta Rahima tayi tana share kwalla kafin tawani irin kife kanta akan guwiwa tajuya musu baya tana kuka sosai dan bamatason ganinsu, tagaji dakomi da kowa, tun tanajin su sama sama suna lissafi abubuwan da za'ayi da kudin gobe har tajisu shiru sunyi bacci, kasa bacci tayi ta tashi ta zauna tana kallonsu, dukansu chakure akasa adan tsukukun dakin nan sai uban minshari suke barin ma wanda taji an kira da Maccido dake minshari kaman wata katuwar tirela nazuwa, Mairo ce abayanta sanye da kayan jikinta tana bacci tana surutai da dafarko bataji danji tayi kaman tana wani yare. "Wadugaga u'uhm, wayyo, zafi Wadugaga, kamin rai kaji, Mama!" ta kwala karan dayasa ta tashi zaune a firgice tana waige waige tana kallon dakin kafin ta juyo ta kalli Rahima dake zaune tana kallonta tana zaro idanu dan tsoro taji, ajiyan zuciya Mairo tasauke tasa bakin dankwalinta ta share zufan daya fito a goshinta sanan takara dagakai ta kalli Rahima ganin har lokacin kallonta Rahima take yasa ta balla mata harara tareda murguda mata baki tace "naci miki bashine?" watsa mata harara itama Rahima tayi tace "kindai cinma aljanin daya biyoki amafarki kina ihu kin hana mutane bacci bashi" tsaki Mairo taja tamika hannu tadauko fitilan zata kashe da sauri Rahima tace "karki kashe tsoro nakeji" hararanta Mairo tayi tace "fitilan ki ko namu rasai" ta kashe fitilan takoma ta kwanta tareda kankame jikinta, ahankali Rahima ta kwanta tajuya mata baya tana kallon bango ta runtse ido sosai hawaye na fitowa daga gefen idanunta, jikinta ciwo yake, gawani irin tsoron mutanen nan datake ji, banda ma haka kawai wani tsoro taji tanaji tarasa dalili, haka ta dinga kuka takai kusan rabon dare sai bacci yay awon gaba da ita. Wani kara kaman na busa algaita ana bubbuga ganga dataji a kunnenta gakuma karan kuka dataji tanaji yasa tabude idanunta ahankali cikin bacci batare data juyowa tana kokarin wassakewa daga baccin, daga chan waje taji ana bubbuga gangan taji ana fadin. "Wadugaga na jiran Mairo, Mairoo Mairoo Mairo ubangijin ki na jiranki" sai akai shiru aka cigaba da bubbuga gangan, karan kuka taji sosai da batasan nawaye ba, sai chan taji muryan matar jiya Ladi tace "kinga Mairo karki jazamin bala'i kitashi kibisu kutafi daga yau sai gobe fa shikenan yagama kema hankalin ki ya kwanta, tashi kibusu kinsan dai inhar kika bari gari yawaye kinsan abinda zai biyo baya, tashi kitafi yar kirki" muryan Mairo taji chan kasa tana sheshekan kuka tace "Mama dazafi, Mama wai mesa ake mana hakane, yaushe zaku chanza wanan al'adan eh, mama wlh nagaji yazo akashe ni din" da sauri Ladi tace "wlh, wlh zan fita nace musu suzo su daukeki, yanda akai abin nan dake haka nima zamanina akayi dani, so kike amana dariya adinga nunamu agari, ba bakon abu bane kowa yasan da hakan mahaifinki ma haka, wuce kitafi kinsan zakije yomin sari anjima kinga kina dowawa dasafe saimuje, wuce kitai" alamun tafiya taji sai taji Ladi tace "yauwa Allah ya kiyaye sai andawo" bata karajin kukan Mairo ba ko muryanta saidai ajiyan zuciyan dataji Ladi ta sauke taga an kashe fitila dakin yay duhu, tambaya kanta tayi to ina aka kai Mairo, su waye masu kidan nan dasuka zo suka dauketa da daren nanne ko asuba nema yanzu oho. Tabe baki tayi tacigaba da baccin ta. 41 & 42 Littafin nan na kudi ne duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa. _How to subscribe_ _zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting BIN ABINDA ZUCIYA KESO_ Wani bacci mai nauyine ya kwashe ta, ihun yara da hayaniya daya cika mata kunne, da kukan yaro yasa tabude idanunta ahankali tana kallon koina, dakin yay haske sosai sun daga asabarin sama gari yawaye dan har rana tafito, yaran duk suna zazzaune akasa koko sukesha sai Maccido dake kusada mamarshi rikeda sandar kewo da alamu yagama shan nashi kokon, Maman su kuma na kokarin lallashin agwai din hannunta daketa tsandala mata ihu, bin duka yaran dakin tayi da kallo da babu kaya ajikinsu dakin sai uban zarnin fitsari dayake yi, ahankali ta tashi daga inda take ta mike tsaye hakan yasa Maccido ya kalleta yace "kin tashi yar binni" dauke kai tayi tareda ballamai harara tai hanyar kofa zata fita Ladi tace
Chapter 48 · 0% Book details