← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 119

Sashe 21

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M Shakur 1 Wani top dinta na Dorothy perkins white and sky blue ne shima long sleeve tazaro daga hanger tasaka, rigan yadan saukar mata dan yarufe mata bombom, wani long fashion necklace tasaka daya saukar mata kan rigan, sanan tadau veil dinta white zata yafa da sauri Mummy tace "no kiyi wanan hadadden daurin nan dakika iya" murmushi tayi harda dan gudunta takoma gaban madubi ta zauna ta shiga daurin, tsaf tai daurin dayadan bada v shape ta gaban goshinta ya mugun mata kyau, wani takalmi mara tsini sosai Mummy ta dauko mata white karba tayi tace "laaaa Mummy na ya akayi kikasan shi zan sa" dariya Mummy tayi tace "I know your dressing humor" murmushi tayi ta shiga saka takalmin Mummy sai kallonta take harta gama ta mike tsaye Mummy tabita da kallo ba karamin kyau tayiba kaman wata celebrity, ita kanta jikin Rahima na mugun burgeta batada wanan girman jikin, she looks small, batada wani tsayin kirki bata da kiban kirki but her organs are so full, bumpy and super package, tanada hips da boobs bana wasaba gatada yar karaman kafa, ga karamin jiki, irin matayen nanne da ake kirada too perfect yan charass chass, wayarta ne yay ringing hakan yasa Mummy tadauko wayan dake kan gado tana kallon screen din tace "gashinan ya iso, yi sauri feffesa turarukan ki" fesa turare ta shigayi masu bala'in kamshi sanan ta karbi wayan daga hannunta ta sa akunne. Cikin wani murya mai dadi Chris yace "Hi Beautiful, am outside" ayangance tadan murguda baki tareda juya ido tace "okay am coming" baki Mummy takama tace "Autaaaa" fashewa da dariya tayi tafada jikin Mummy, Mummy tace "kinga shida tamiki agidan nan dudda yau Abban ki baya gari amma dai kidawo da wuri kinji, muje narakaki nima naga Chris dinan da babyna ketamin maganan shi tun jiya" tana rikeda wayanta suka fito tareda Mummy, mayafi Mummy tadauko afalo sanan suka fito tare su Siddiqa na falo binsu sukayi da kallo barin Rahima dataci shegen gayu kaman zata gasan kyau tana balla musu harara, har wajen Gate Mummy tarakata da hannu tanuna ma Mummy motar Chris dake pake a gab da gate dinsu karasawa sukayi ganinta tareda wata yasa Chris yabude mota yafito yaci gayu na bala'i dan gemunshi da ajiyan tagani bakine yau taga yakoma dark blue yama gemun tiri kalan sneakers din kafarshi yasa wani crazy wando daya babbarke gawata shegen sarkan Cross awuyan shi yayi askin nan dakalin shaidan yana dan tauna cingum yana murmushi, hannu yamikama Mummy yace "watsupp Mummy, afternoon" gyadamai kai Mummy tayi ta rungume hannunta akirji kaman mai shirin salla tace "sannu Chris birthday boy, see my daughter, you guys should have maddd fun okay, but bring her back before 6" wani irin dariya Chris yayi harda dan juyawa ya kalli Rahima daketa kallonshi yace "your Mummy is a sabi woman, alright Mum we will have fun Chris promise you that" kashemai ido Mummy tayi batare da Rahima ta luraba dan kallon Chriss take, murmushi yayi ya kalli Rahima yace "let's go beautiful muje nabude miki ki shiga" gaba ta shiga yana biyeda ita hakan yabashi daman juyowa shima ya kashema Mummy ido tareda lashe lips dinshi, saida yasata ciki sanan ya zagayo yana dagama Mummy hannu ya shiga ciki ya kunna motar yaja duk sunama Mummy bye, ajiyan zuciya Mummy ta sauke sanan tajuya takoma cikin gida da Siddiqa taci karo awurin Gate idanunta sunyi jaaa sosai tsabagen fushi, babu ko alamun tsoro tace "wlh Mummy saina fadama Abba duk abinda kikeyi, keke bata Rahima bakowa ba, yanzu Mummy ba abin Rahima takawo miki katon arne, arnen ma wanan dan iska ne amatsayin saurayi ki fatattake shiba shine zaki barsu yafita kinsan inda zai kaita? Mummy mufa matane, Rahima mace ce, very fragile ma kuwa, batada hankali wat if yamata wani abu? Wat if yay raping nata? Me zaki cema Abba eh? Mummy! " takirata da karfi looking so pain, wani banzan kallo Mummy tamata tace "ki rubuta ki ijiye duk randa zaki gayama baban ku wlh wlh aranan kika fita daga sahun y'ay'ana na cikina saidai kije kinemo wata uwar" tai tsaki tawuce tabar wajen. Sundanyi nisa a hanya yajuyo ya kalleta kaman yanda itama ta kallai yace "beautiful you look very pretty today, I love every bit of this dressing" wani irin juyamai idanu tayi tace "thank you kaima kai kyau no banda wanan blue beard din" murmushi yayi yacigaba da tuki sai danne dannen waya takeyi kusan tafiyan minti arba'in sukayi suka kai wani gida dake nan kan titin kaduna express road za'ai kwana adan shiga dajin but ko tafiyan minti uku bazakayi da shigaba zakaga tafkeken gida, gidane mai white gate, parking yayi akofar gidan yabude mota yafito sanan ya zagayo ta side dinta yabude mata kofan, fitowa tayi ta tsaya tana kallon ko ina, hannunshi yamika zai rike nata da sauri ta janye tace "ni karka rikeni" dan juya ido yayi sanan ya rufe motar yakarasa gaban Gate din bude Gate din yay ya shiga ciki tana biye dashi, babban tsakar gida ne da aka gyara ga kayan dj duk anyi setting up ga balloons ga kujerun da aka jera dayawa na baki, turo baki tayi dan yasoma dama zama jikinta yin hakan tace "ina mutanen to?" murmushi yayi yace "just few of my friends are inside with their babes chilling you know, the dj sun tafi cikin gari dauko some stuff, the main party zai fara dan anjima insun dawo let's go" binshi tayi ciki tana kallon ko ina har zuwa dan flat daya kachal dayake big compound din tun kafin su shiga sukejin warin wiwi, bude kofan yayi ya shiga yana mata alamun ta shigo itama shiga tayi wasu mazane guda uku tareda yan matan su dasukaci uban attachment suna smoking weed ga shisha pot agabansu dawasu kwalaban abubuwa, yatsine fuska Rahima tayi ta juya zata fita da sauri yakamo hannunta yace "No beautiful don't go, I promise you will have fun today, beside we we are not sitting here am taking u inside" yay maganan yana janta ahankali zuwa ciki batare daya kalli abokan ba suma suka share shi basu cemai komi ba, wani daki yabude dakin gado ne da kujera a gyare tsaf ga TV dake aiki, zaunar da ita yayi kan kujera yace "sit here, bari naje na kawo mana abubuwan mu let's have fun, don't worry I will take care of you kinji beautiful, now smile for you" dan murmushi tayi ganin duk yanda yabi yadamu sabida yaga ta daure fuska, tashi yayi yafita zuwa mota, wani babban basket yadauko dake dauke da shisha pot guda uku dawasu kwalabai ya shigo gidan, yay dakin datake, aijiyewa yayi a gabanta sanan ya maida kofan yarufe yadawo kusada ita ya zauna ya fito da shisha pot daya ya daura akan table din dake gaban kujeran dasuke kai yace "do you do shisha Beautiful" girgixa mai kai tayi hakan yasa yay dan dariya yace "what! kinyi missing, Shisha tsabagen dadinshi jizakiyi kaman kimutu barinma yanda na zuba harizona aciki hulala baby, yay maganan yana ciro wasu kwalabe guda biyu suma yadaura agabansu yace "this are mixture of codeine and a lil bit of crack, crack din just half teaspoon da kyar my guy yabarmin shi 50k" kallonshi tayi tace "menene crack din?" cikin gurbataccen hausan shi yace "Yayan Cocaine ne Crack, Cocaine elder brother kenan Beautiful in kinsha crack inspiration ne kawai zaita zuwan miki baby, wani irin dadi da murna zakiji, feeling kaman ke kadaine aduniyan nan, bakida matsala ko daya, have a sip a feel it" yamika mata kwalban daya bude karba tayi tana kallon bakinshi kafin ahankali ta kurba, lashe baki tayi tadanyi murmushi tace "laaaa dadi kuwan" murmushi yayi yace "yes da madara madara acrack din sanan ga codeine saisa kikaji yay dadi but don't take much this is your first time" sake kurba tayi, zata sake maidawa baki yace "wowowo is okay, gwara kima shisha wanan shan, this is big for you dan crack can kill you wlh, oya let's see how many kalan buso hayaki kika iya let's play a game" yay magana yana bata mouthpiece din shishan, shima ya rike nashi mouthpiece din, yace "let's do it in one, two, annndddd three" atare suka zuko shishan kafin su janye daga baki, shiya fara mata alamu ta kalleshi hakan yasa ta kallai yawani irin huro hayakin daga hancin shi in style din circle circle, ware ido tayi kafin ta huro nata hayakin ta baki yay wani irin saman dakin kaman an bude teargas tafi ya shiga mata yace "yayyy beautiful u are really smart, ya kikaji shishan strawberry flavour ne yahadu ko" murmushi tayi bamata kulashi ba tsabagen yanda shishan yamata dadi takara kaiwa bakinta, murmushi yayi ya dauko kara daya na weed yaciro lighter daga aljihun shi ya kyasta sanan ya maida lighter yakai weed din bakinshi ya zuka hakan yasa ta kallai tana huro hayakin shishan, karan weed din yamika mata yace "zaki sha?" hararan shi tayi tace "give me a new one" dauko wani yayi ya kunna mata yabata karba tayi tashaka ta fuzar sanan tasha shishan tana murmushi today is just the best day of her life, inda ace su Ya Siddiqa sundan dadin abin nan da saisun saye duka weed da codeine din duniya gaba daya, lumshe ido tayi ta wani irin jingina da bango bacci nawani neman kwasheta dan abubuwan sun soma bugar da ita tun tana bashi amsar maganan shi harta zo bamataji da kyau, zata karakai dan gutsuren weed din bakinta Chris ya karba da sauri da mouthpiece din shishan ya ijiye su kan table yace "hey beautiful, you have had enough, don't want you to pass out is okay" dan turo baki tayi cikeda rashin jin dadi murya chan kasa da bata fita sosai, very slow tace "give me the shisha" hannunshi yasa ya shafa soft kumatunta yana kallon yanda take lumlumshe ido murya chan kasa cikeda sonta yace "you are the first Muslim girl I've ever loved in my life my god u are so beautiful, so pretty" dan bude ido tayi kadan ta hararai kafin tasa hannu ta kabar da hannunshi dake kan kumatun ta, cikin magagin bacci da maye
Chapter 21 · 0% Book details