Sashe 41
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da muka baki, mahaifinki ya killaceki yahanaki zuwa school, yahanaki fita ashe jira kawai kike yabar gida na sakan daya kiyi abinda ranki keso, dama baccin karyane eh Rahima? Ban taba dukanki ba amma yau kinyi kuskure wlh saina zaneki Auta, saina zaneki auta" Mummy tai maganan tana rufeta da duka tako ina Rahima na tureta tana turo baki kaman ma batajin dukan, Sameer na kallonsu baice ko uppan ba ko kyafta ido bayayi Rahiman yake kallo, daddaggewa Rahiman tayi ta tura Mummy cikin maye Mummy tai baya da gangan tawani irin fada kan jikin Sameer dake shafama Abba ruwa a goshi, unexpectedly yajita kanshi before you know it Mummy tafashe dawani mahaukacin kuka sosai tana kara shiga jikin Sameer din, tunda take aduniya tsawon shekaru hamsin da hudu zuwa hamsin da biyar kenan bata tabajin kamshin turare mai dadi kaman irin kamshin da Sameer keyiba, chusa kanta tayi awuyanshi kaman sabuwar vampire tana kuka tana goga fuskarta a thick neck dinshi tace "zan mutu Sameer Rahima zata kashe iyayenta da bakin ciki, innalillahi wa innailaihi raji'un" tureta Sameer yayi daga jikinshi da sauri cikin wani irin yanayi yatashi tsaye da sauri yana kakkabe jikinshi hakan yasa Mummy kaman wacce hankalinta ya gushe ta kwanta warwas akasa tana kuka harda birgima kaman irin bama tasan me tayiba dinan, fashewa dawani mahaukacin dariya Rahima tayi tafara rawa tana juya jiki kaman wacce taje dancing school, motsin da Abba yayi yana kokarin bude ido yasa da sauri Sameer ya tsugunna akanshi yarike hannunshi tareda kiran sunanshi. "Abba, Abba am right here open your eyes" tsagaita kukan Mummy tayi ta taso da sauri tazo dayan side din Abba, hannunshi takama tace "Alhaji gani nima katashi kaji" ahankali Abba yabude ido tareda sauke wani irin ajiyan zuciya, idanunshi ya sauke akan Rahima dake rawa sosai kaman an kunna disco, da yatsa yanuna ta cikin muryanshi da bata fita sosai yace "s....s......son t.....a" yakasa karasa maganan yay shiru sabida yanda numfashi kemai mugun wuya duk wanda ya ganshi yasan yana bukatan oxygen, cikin kokartawa da jarumta yace "he......her......take......her t......to.....re.....hab....." ganin yakasa karashe maganan yasa Sameer ya girgiza mai kai yace "stop talking Abba you need rest, nakaita rehabilitation centre?" gyadamai kai Abba yayi ahankali yace "n.....n..." da sauri Sameer yace "now?" gyadamai kai Abba yayi da sauri, ahankali yace "okay calm down" tashi yayi batare daya kalli Mummy ba yace "Mama stay with him har Dr shi yazo, bari na kaita" yana maganan yay kan Rahima dake rawa kaman an mata wahayin rawa, fizgo hannunta yayi cikin fushi ihu tayi. "ahhhhmmmm, saken maye, saken" tadaga dayan hannunta zata bugamai ya hada biyun yarike azuciye jijiyoyin kanshi na fitowa ya fizgeta, ganin ko dan kwali babu akanta ga jelar kitson gashinta dake lilo yasa yasake ta hijabin daya gani tare da dadduma gaban mirror yaja yasake fizgota da hannu daya tana kokawa dashi yasaka mata sanan yajata tareda bude kofa, kafa bakinta tayi kan hannunshi cizonshi tayi ya fita daga dakin da ita amma ko gexau baiyiba yay falo da ita su Siddiqa duk suna zaune sunyi zuru zuru, tausayi suka bashi hakan yasa yace "kuje ku zauna da mamanku am coming" yabude kofa yafita da Rahima dake ihu tana tirjewa tana fada dashi sosai, ganin turjemai takeyi yasa yawani dauketa kaman yadau kara yadagata sama yay motarshi da ita bayan motar yabude ya jefata ciki ya maida kofan ya kulle ya shiga gaba yarufo motar duka yaja motar gateman yabude mai yafita daga gidan, ihu kawai Rahima take a motan tana tsalle, hijabin ta zare ta yar a kasan motan ta shiga tsalle, saikuma tafara hauka takama kan kujeran gana tace "pitttt pittt pitttt, motana motana mai take kawunan kunkuraye, jiiinnnn, burundun dudundundun vuuuuuuuuwwuuuuuu" tana haukan tana tsalle cikin motan tana wasu yare na mahaukata.34. Bayan Dr sukabi har zuwa wani daki datake cikin ward din, dakin gadaje guda biyar ne ciki anbata wani gado dake kusada windo, tsayawa yayi akanta yana kallon karin ruwan da ake mata tana sharban bacci Dr dake kusada shi yace "tai bacci sabida amayar da komi na cikinta damukasa tayi dazu, as for visit dinta tunda kaika kawota signature dinka mukedashi you can come anytime kaduba ta, banda kai kuwan babu wanda zai iya zuwa dubata unless ita tai requesting wani nata yazo, saikuma idan tana 5th phase na treatment dinta zamu gayyaci yan uwanta suzo su ganta, karka damu in sha Allah sister ka ta kusan dena shaye shaye har abada" hannu Sameer ya mikamai yace "thank you so much Dr, zan wuce dare yayi" gyadamai kai Dr yayi yace "yeah, gud night Lieutenant" gyadamai kai yayi yajuya batare daya kalli patients din wajen ba yawuce yafita, marfin motarshi yabude zai shiga wata nurse daya daga cikin wayanda suka gungurata zuwa ciki tafito da sauri tace "Sir wait please" harya bude kofan motan ya tsaya juyowa yayi da sauri ya kalleta, karasowa wajen tayi tana murmushi tace "Sir actually naga baka kawo sister ka da komi ba, and normally I am the one incharge of kayan su da abubuwan amfani su" anatse yace "I tot kuna basu uniform me kuma take bukata?" yay maganan da zuciya daya dan baisan me kuma suke bukata ba, murmushi nurse din tayi tace "actually yes bama bukatan kaya dan uniform suke sawa, but yakamata adan taho da jaka dake dauke dasu pants, bra, singlet, pad kasan mace ce she needs all of this" dan lumshe ido yayi dudda maganan yazo mishi bazata amma saiya danne yace "ohh kuna sayarwa ne anan?" wanan karan kyalkyacewa da dariya nurse din tayi ta girgixa kai tace "a'a bamu sayarwa, but in kafita across the street akwai wani super market that sell all ladies wear hakanan, sai ka karo mata hardasu toothbrush da cream dinta da toothpaste, sabulon wanka, sponge da kuma hijab sabida salla, but most importantly karka manta da pant and bra sai pad this 3 things she can't get them here" dan gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba ya shiga mota yatada yaja aka budemai Gate yafita daga gidan yafita daga Street din har zuwa shagon datamai kwatance, parking yayi agaban shagon ya shigo yana kalle kalle, breziyoyi ne da panties kala kala ashagon, tsayawa ma yayi chak batare dayasan wani abu zai daukar mata ba this is the first time in his life dayake sayan pant bra da pad toshi baida kanwa ko Yaya bama ataba aikanshi irin abun nan ba, ganin yanda ya tsaya chak yasa madam din shagon wacce take bayerabiya ta taso tazo inda yake tace "what can we get for you young man?" ajiyan zuciya ya sauke yace "aahhhmmm" yama kasa magana dan for real sunan kunya yakeji inzai fada, ko gane hakan matan tayi tace "we have different breziya for your wife, sisters, cousins and girlfriend, we also have panties, normal pant, g-string, lace and shorts, we have disposable pants you know, ladies use it during their monthly period is easy" da sauri yace "give me normal pant and bra, and the last one you mentioned, disposable pant" da sauri matan tace "okay okay, what size kakeso?" dan kallonta yayi to shi wani size zaice mata yay shiru ganin haka yasa matan tace "okay I get baka san size dinba, what's the age of the lady?" ahankali yace "20" da sauri tace "okay oka, is she bobby? Ko batada girman nono sosai hakan nan?" dan kauda kai yayi yama rasa mezaice mata da kyar ya tattaro yan kalaman bakinshi yace "ammm Big, I.....g...guess" da sauri matan dake kallonshi tace "okay manyan nono kenan takedashi?" gyadamata kai kawai yayi batare daya kalleta ba, section din breziyoyi tawuce tana surutu tace "nagane irin yaran nanne dasuka taso sunada girman nono" tai maganan tana ciro wasu fine manyan breziya masu bala'in kyau lace dinsu hadaddu ta dagomai su tace "kaman wanan zasu mata ko dan kace she is 20, wanan ne daidai size din irin yara yan 20 dinan masu manyan nono" da sauri yadauke kai batare daya sake bama bra din second look ba tareda gyadamata kai, hakan yasa tace "gudanawa zansa?" rasa mezaice yayi yace "just put plenty" dariya matan tahau yi dan tasan wanan bakon siyan breziya ne hakan yasa tasaka dozen guda 12, pant kuma due to age datai amfani dashi tasamata yan daidai 2 dozen guda 24 kenan, tasaka different design na singlet 7, sai disposable pant tasaka 30, tasa mata short guda hudu, saida tagama hadawa tace "Sir i have pad o in kanaso oyinbo pad, daga kasan waje aka kawosu no matter yanda sister ka keda heavy flow this pad zai jure, is very fine, and cotton ne to make mai amfani dashi more comfortable" batare daya kalleta ba yace "add it also" saka kwali bakwai tayi sanan ta kawomai, ya kalleta yace "do you have cream, shower gel da toothpaste da sauran su?" da sauri ta gyadamai kai takoma tahado duka sanan ta kawo tamai bill almost 55k dan pant da bra masu tsada ne tasaka mai komi aleda ya karba tareda biyan kudin yafito yana kalle kalle ko akwai shagon dazai samu yasai jaka, ganin babu wani shago yasa yabude boot din motarshi wata babban bagpack na sojoji ya ciro ya ijiye ledan kayan agefe, zage zip din jakan yayi ya zazzage abubuwan ciki wanda suke yan tarkace ne sanan yadau ledan kayan yatura ciki ta shiga sanan yazage yadau jakan ya rataya a kafada ya rufe boot din sanan yadawo motar ya ijiye jakan adayan kujeran yatada motan yakoma wajen yana shiga a reception yaci karo da nurse din bata jakan yayi yace abata tamai godiya sanan yajuya yafito ya shiga mota yabar wurin saida yahau kan titi sanan ya kalli agogo karfe shadaya da kusan minti shabiyar, wayarshi yaciro yay dialing number Abba dan bazai iya komawa gidan ba dare yariga yayi saidai da safe ringing biyu aka dauka muryan Mummy yaji tace "Lieut ka kaita kana dawowa ne?" batare daya bata amsaba anatse yace "ya jikin Abba Dr yazo yaduba shi?" cikin sheshekan kuka Mummy tace "yazo anamai karin ruwane bacci yake har yanzu" gyadakai yayi yace "alright will come in the morning kafin nawuce office, gud night Allah kara sauki" da sauri Mummy tace "Lieut"