← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 119

Sashe 68

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itace mai hankalin yace "am going to the office zan dawo kafin kudawo" atare dukansu su ukun banda Rahima harda Luba sukace "saika dawo Ya Sameer" gyadamusu kai yayi yawuce yafita. 61.... Dariya Siddiqa tayi ta tashi takalli Rahima tace "muje mu dauko plates muci abinci bamuyi breakfast bafa" washe baki tayi ta ballama Luba harara sukai kitchen tareda Siddiqa suka kwaso plate suka fito pepper soup tadeba tadawo falo tafaraci itakuma Luba ta debo rice da stew da katon chicken tanaci, saida Rahima ta shanye pepper soup dinta tatas sanan ta tashi tazo kaman zata wuce ta dumbuzo naman Luba ta arce aguje tai sama aguje Luba tabita tace "wlh kibani kayana" tsaki Siddiqa tayi dan tagaji da rabasu, Zeena uwar zigi ta daga murya tace "karki raga mata Luba ki karairayata" kukan Rahima sukaji daga sama saiga Luba rikeda namanta tana dariya Siddiqa ya kalleta cikin fushi tace "saina fadama Abba tunda biyema Auta kike kuna hauka" zama tayi kaman zatai kuka tace "ita tafara ai" Siddiqa batace mata komiba tacigaba dacin abincin ta. Office dinshi ya shigo yana kokarin bude office dinshi da ID dinshi wani soja yazo ya saramai yace "Sir Marshal na kiranka" fasa bude office din yayi yay office din Marshal, shiga office din yayi tareda saramai. "Sir" yakame, murmushi Marshal yayi yace "mekake yi a office ango?" kasa magana Sameer yayi kanenshi duk sun gama bazashi aduniya, murmushi Marshal yayi yamikamai wani envelop yace "ga wanan gift dina kenan sanan kabar mana office dinmu mun baka hutun kwana talatin aje asha amarci lpy, bye bye" Marshal yafada cikeda tsokana yana kallon fuskan shi akunyace Sameer yay dan murmushi yace "thank you Sir" gyadamai kai Marshal yayi yace "oya bye bye nace don't keep madam waiting" juyawa da sauri Sameer yayi yafita daga office din yasauka kasa yay wajan motarshi, wacce yagani jingine da motarshi yasa ya daure fuska yawuce yazagaya yabude motan ya shiga da sauri tazo tawajen tarike kofan kaman zatai kuka tace "wait Lieutenant please" tsayawa yayi batare daya kalleta ba, ahankali tace "naji ance kai aure" key yasoka amota yace "and??" irin tambayan nan nakidana matsala dahakanne, girgizamai kai Aliyah tayi gwanin ban tausayi tace "came all the way here just to say congratulations, agaida madam" gyadamata kai yayi kawai batare daya bata amsaba ya ja motar da sauri tasaki kofar ya maida yarufe a binshi, shifa mutum ne da inbaiso baiso Aliya kuma takasa gane hakan, gida yaje dudda Ummi bata kulashiba haka yakaraci zamanshi agidan yabar gidan around 5, tunda yy parking yakejin hayaniya girgiza kai yayi cikeda takaici yawuce yay ciki bude kofa yayi ahankali hakan yasa duk sukai shiru Rahima na share hawaye, tana ganinshi ta nemi waje ta zauna gaisheshi dukansu sukayi Siddiqa tace "zamu tafi Ya Sameer yamma tayi" murmushi yasakin mata ita kadai ne mai hankali cikinsu yaciro kudi daga aljihunshi yamika mata kin karba tayi yamata mugun kallo ya harareta yace "thanks for coming, muje nasa amaidaku gida" da sauri tace "a'a wlh Bala direba yakirani yana waje wai yana jiran mu" gyadamusu kai yayi ya kalli su Zeena dake kallonshi yadaga musu hannu yace "bye" washemai baki sukayi sukace "bye Ya Sameer" sukai hanyar fita fashewa da kuka Rahima tayi ta tashi zata bisu dan duk maganan nan da akeyi tana zaune ganin zata fita da dan rigan jikinta iya guwiwa yasa Sameer yakirata bawasa. "Rahima" da sauri tajuyo, "jekidau hijab" wani irin murmushi Siddiqa tayi aranta tace "Alhamdulillah finally Rahima ta auri wanda zai gyara ta" juyawa tayi da gudu tai sama Sameer biyeda ita dakinta ta shiga ta dauko hijabinta tasaka sanan ta sauka kasa da gudu tana kuka hargate tarakasu tana musu bye bye tana kuka, Luba dariyan mugunta ta dinga mata dama dama Zeenatu ma tadanji tausayinta koba komi akwai soyayya a tsakanin su rashin kunyanta dama kesa suji sunajin haushinta, saida taga sun bace sanan tajuyo tadawo ciki tana kwalla tai sama dakinta ta shiga ta kwanta, saida taji ana kiran magrib sanan ta tashi ta shiga bayi wanka tayi tafito daure da towel ta shirya tsaf tasa wata rigan baccinta daya tsayamata a guiwa yanada tsagu on each side, jin cikinta naciwo yasa tadau magani tasha ta kwanta ta lumshe ido, she is bored and lonely batada waya bamatasan wace duniya wayarta yakeba, babu abinda ke mata dadi gatanan gatanan ne, inhar tana tareda Mummy ta ba'a tabaji tai ciwon maraba dazaran zata fara Mummy ke bata tramadol da sauran kwayoyi ciwon yabace bat. Lumshe ido tayi ta gyara kwanciya bacci na neman kwasheta, knocking akayi da sauri tabude ido Sameer ne yana sanye da jallabiya fara da alamu daga masallaci yake, tashi tayi ahankali ta zauna tana wasada yatsunta, ahankali yace "cramps din yadena?" girgixa mai kai tayi ahankali tace "yanayi sosai, please ka kiramin Mummy na tabani maganin datake bani ins......" kasa karasa maganan tayi ganin mugun kallon dayamata ta saukar da kanta kasa juyawa yayi yafita hakan yasa takoma kan gado ta kwanta takasa bacci tarasa meke mata dadi ita kadai she feels idan da zata sami yabun nan tasha all this tsoro bakin ciki da nauyi da zuciyan ta kemata zaitafi ta tashi gobe da farin ciki, filo tarike gam gam tana kallon kofa har shabiyu nadare takasa bacci, ahankali ta saki filon ta tashi tabude kofa ahankali tafito, falon duhu harya kashe wuta, da hasken dakinta takarasa har gaban dakinshi tasa hannu tabude kofa ta shiga ciki ta mayar da kofan tarufe ta tsaya awajen tasakin mai kuka dan tarasa yanda zatayi ita takasa bacci ita kadai, kunna bedside lamp yayi dakin yay haske yana kwance ya lulluba da bargo babu riga ajikinshi, kallonta yayi baice mata komiba, saukar da kanta kasa tayi tacigaba da kuka atsaye cikin kuka tace "ni nakasa bacci, am scareddddd" wani mugun kallo yamata saikuma ya lumshe idonshi yadaura hannunshi akan goshinshi, dan dagokai tayi ganin ya lumshe ido yasa ta tahoda sauri tahau gadon ta tafi chan karshen gado ta kwanta, jin alamun kwanciyan mutum yasa yabude ido yajuyo ya kalleta harta rufa da bargo tana share hawaye, yace "ninace kizo ki kwanta, zoki fita" fashewa da kuka tayi taki tashi, tsakin takaici yayi yasa hannu yakashe wutan dakin yarinya dukta zamemai matsala, takai almost 15min kuka take amma mara sauti sanan tashare hawayen tass ahankali ta matso kusadashi sosai sanan ta sauke wani ajiyan zuciya, jinta matso kusadashi yasa yajuyo ware ido tayi atsorace tai yunkuri zata koma baya yaka hannunta yace "mesa kikeson zuwa jikina?" girgiza mai kai tayi tace "am scared haka nake kwana kusada Mummy" murya chan kasa har lokacin bai saki hannunta ba yace "am I Mummy?" girgiza mai kai tayi, ahankali yace "who am I?" murya chan kasa ta kuka tace "Yaya Sameer" ahankali yace "good you know, I'm Sameer and banson mace na kwanciya kusada ni today is the last day, kikazo dakina da daddare gobe saikinsha mamaki understood?" gyadamai kai tayi ahankali, hannunta yasaki yace "ki matsa" matsawa tayi baya kadan duk sukai shiru, Rahima kaman wacce keda wata cuta takasa bacci wuraren daya tasake matsowa ahankali gab dashi babu wani distance amma bata bari jikinta yataba nashiba sanan ta lumshe ido tafara bacci. Da asuba shiya fara bude ido yanda yaga yarungumota gabaki daya saida yaji tsoro kaman wata yar jaririyanshi da sauri ya saketa yakoma baya, tashi yayi batare daya kalleta ba yawuce yashiga bathroom wanka yayi ya shirya yawuce mosque sanin bata salla yasa bai tadata ba saida gari yadanyi haske yadawo har lokacin bacci take, girgiza kai yayi kawai sanin batai bacci dawuri ba ga uban kukan data dinga yi saisa bata tashi dawuri ba, shiryawa yayi tsaf cikin sport wears yafita morning jogging. Around 8 na safe Mummy tafito a shirye tsaf riga da skirt tasaka na kanti sanan tadauko wani after dress tasaka tareda saka boturan gabaki daya bazama kagane me tasa acikiba tadauko wani milk color babban gyale ta yafa, Abba tasamu a falo da yaran yanashan lip tea a cup bairiga ya shiryaba dan yau yanaso zaije aiki, ganin ta shirya yasa Abba yace "wife badai gidan Sameer zaki this early morning ba" dan kallon haushi Mummy tamai tace "saikace wata mara hankali, saloon zani kasan layi akema matan daganan kuma zan wuce gidan babban aminiyata Bara'atu saina dauketa mutafi gidan Rahima tare" ahankali Abba yace "ok okay tom shikenan agaidata inkinje" bata amsashi ba tai hanyar kitchen inda yaran ke girki hannu tamika ma Zeena tace "ke bani santana leda nan" farar leda Zeena tamika mata tana kallon fuskan maman nata tace "Mummy wai menene ke damunki bakida lafiya ne? You look somehow kuma idanunki sundan yi ja sun kumbura kaman wacce tasha kuka" dan taba idanun Mummy tayi cikin wayancewa tace "kwaro ya shigan mini ido, karku rikeni da surutu am coming" tai maganan tana bude store ta shiga ta maida kofan ta rufe, gaban jarkan manjan su taje ta bude ta tuttula a ledan sanan ta kulle ledan tabude handbag dinta ta jefa tafito tanama yaran dasuke binta da kallo murmushi tace "bye gurls ayi girki mai dadi" fitowa tayi Abba baya falo da alamu yashiga ciki yaje wanka halan, fita tayi ta shiga motar ta taja tabar gidan, tun jiya ta tambayi su Siddiqa address din gidan, tasake tambayan Bala direba, sanan ta tambayi Abba, hanyar gidan Sameer tadauka har kofar gidanshi tai horn soja yafito yace "good morning Madam please who are you? Oga bai sanar damu zawanki ba" daure fuska tayi tace "am his in-law, his wife mother, will you open the gate for me ko saina saka ya koreka you loose you job" da sauri yakoma suka bude mata Gate din ta shiga cikin gidan, kashe motan tayi tacire after dress din yarage daga ita sai riga da skirt din kantin, rigan open neck ne sosai ya bayyanar da kirjinta kana gani, fitowa tayi ta yafa mayafi da kyau sanan tadau jakanta tanabin gidan dakona shugaban kasa sai haka da kallo tai flat din, bude kofa kai tsaye tayi ta shiga daidai lokacin Rahima tafito daga dakin Sameer tana hamma, jin anbude kofa yasa tadan karasa wajen stairs dan ganin waye, ganin Mummy ce taci uban gayu tarike handbag yasa tai
Chapter 68 · 0% Book details