← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 119

Sashe 3

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ne? Yakuri kinji zan mata magana zata dena, wuce ki koma wajen Sadiq kinbarshi shi kadai, kuma ki saki ranki karya ganki duk wani iri yagane akwai matsala, nunama saurayi ake kana tsananin son dan uwanka, tashi kitafi" tashi Siddiqa tayi tawuce tafita daga dakin deep down bata hakura ba tai alkawarin saitaci uban Auta wlh. Fitowa da Zeenatu tai daga kitchen rikeda plate da jellof rice kekai dayaji fried plantain akai yasa Mummy tace "ahaka zaki kaimata abincin kaman zaki kaima awaki? My friend go back to that kitchen ki daura abincin nan kan tray, ki dauko mango juice din dana hadamata kidaura akai da glass cup, ki kuma samata salad ki sako mata nama guda biyar kinsan tanason nama" juyawa Zeenatu tayi tana kunkuni tace "saikace president zan kaima abinci" kasan cewan Mummy bataji taba yasa ta gyara zama tacigaba da kallon datake yi, jin Zeenatu tasake fitowa yasa tadago kai ganin tayi yanda tace yasa tace "kuma wlh ko kallon banza kika mata sainaci ubanki, kina bata abincin kifito kinajina ko banso adameta bacci zatayi" gyadamata kai tayi tai corridor. Bude kofar dakin Zeenatu tayi babu kowa adakin saidai karan saukan ruwa dataji alamun tana wanka, dakin fess fess sai kamshi yake, fentin dakin off white ne sai dan gadonta dakeda girma normal normal an shimfida bargo mustard, curtains dinta kuma combination of white and Mustard kana shiga dakin zaka gane mai dakin nason this two colors white da mustard, karasawa ciki Zeenatu tayi tana kallon cookie jar dake kan bedside drawer ta dako rabi basuyiba, suma sunada cookie din dan Mummy ke ijiye musu adaki yara sudan sami kayan kwalama but su harsun cinye nasu dayake su ukune da ita sai Ya Luba, da Ya Siddiqa, itako Auta dakinta ita kadai dudda ma tsabagen rigima da fadan dasuke yi ne yasa Mummy taraba musu daki but dudda haka shegiyar bata iya kwana ita kadai dakin kawai zamanta ciki da ranane kawai dare nayi takeyin dakin Mummy, Mummy ma saitai bacci take iya sneaking out ta tafi dakin babansu in yana garin in kuma bayanan to tare suke kwana, ajiye mata abincin tayi akan gado daidai lokacin tabudo kofan bayin tafito daure da mustard towel dinta akirji daya saukan mata iya cinya tana kallon Zeenah data ijiye mata abinci tana turo baki takaraso ciki tana hararan ta tace "me kikemin adakina dakin kine eh, kifita kona hadaki da Mummy wlh" hararanta Zeenah tayi saikuma tai murmushi cikin lallabawa ta kalli jar din cookies din tace "auta indan dibi cookies dinki?" wani kallo auta tamata saikuma ta balla mata harara ta zauna kan gado abinta tareda daukan tray din tadaura kan cinya zata faraci, ahankali Zeenatu ta zauna kusada ita murya chan kasa irin muryan begi begi dinan tace "haba yar kanwata Rahima naaa, indan dauka, 2 kadai zan dauka namufa yakare ne please" turo baki tayi ta make mata kafada ashgawbe tace "ba bakusona ba Mummy kadaine ke sona agidan nan, kuyita sa Dady namin fada, jiya saida kikaja Dady yasani nai wanke wanke bansan wani gulma kikamai ba, bazan bayarba" da sauri Zeenatu tadaura hannunta kan kafadarta aranta cewa take "shegiya mai shegen kafiya wacce bata mantuwa kawai, zaki gane kurinki ne yau" cikin sigan lallashi tawani jawota jikinta tace "kai, Allahu Rahima, to kiyakuri bazan karafadamai ba kinji Autan mu, yakuri, in dauka eh Autan Mummy da Daddy mu" wani irin murmushi tayi cikedajin dadi ta gyadamata kai tana gyara zama tace "dauki 10 nabaki duka" tashi Zeenatu tayi da sauri cikeda jin dadi tai wurin jar din tace "thank you Rims Auta" tadebi cookies din tai hanyar fita daga dakin sanan ta juyo ta kalleta ganin bata faracin abincin ba tana kallon abincin tace "kici abincin mana" yatsine fuska tayi ta dago kanta ta kalli Zeenatu tace "Ya Zeenah the food smell peprish wlh" aran Zeenah tace "mayya, ba Ya Zeenah ba ko Anty Zeenah zakice min bazanji tausayin ki ba, kinsaba kirana ai gasai, hancinta kaman na aljanna hartaji kamshin yajin" murmushi tayi tace "common ai Mummy bata bari asa yaji tasan bakison yaji, ci babu yaji ko kadan, natafi" gyadamata kai tayi tadebo rice din takai baki, maida kofar Zeenah tayi tarufe bayan tafito takafa kunnenta jikin kofar tana murmushi kaman an mata kyautan makka ba'a banza Mummy ke cemata kunama slow poison ba saitayi baxaka taba cewa ita bace ko zata iyaba, su Siddiqa da Luba biyemata suke suyita hauka tana haukata su, itako cin ubanta take ta karkashi. Ahankali take tauna shinkafan dan bata iyacin abinci da sauri sauri ba, wani irin masifan yaji dataji waaaa abakinta kaman an nika attarugu buhu daya a abinci yasa tafeso abincin waje furururr da gudu, da sauri tadau mango juice din dake kan tray din ta kwankwade tana nishi da sauri da sauri, ajiye cup din tayi ganin batadena jin yajin ba yasa ta shiga hurama bakinta iska tawani irin zabura ta mike tray da abincin duka suka kifo kasa tana nishi fast fast, idan akwai one thing da her whole body baya iya tolerating in this life is pepper, wani irin ihu takurma tareda fashewa da kuka tana kiran Mummy hakan yasa Zeenah ta kwasa da gudu tana dariya tai dakinsu ranta fess, tai maganin mara kunyan. *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*
Chapter 3 · 0% Book details