Sashe 62
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sameer kanshi akasa yana zaune kawai shikadai yasan me yakeji, Mu'az yakawo sweet da goro limam yadeba yace za'a rabama jama'a gobe sauran Abba yasa gateman dinshi yay gida dashi, su Siddiqa na zaune a falo sukaga gateman na shigowa dasu goro, Zeena ne tace "na menene?" washe baki yayi yace "Alhaji yace nakawo gida nabarshi masallaci dawasu manyan mutane" yay maganan tareda juyawa yafita daga dakin. Tattaunawa aka shigayi inda Abba yamasu Baffa introducing kanshi, sosai Baffa ya yaba da hankalin Abba ashe babban mutum ne kawai dai irin iyayen nanne dat are so unfortunate Allah yabasu yara marasa ji, ko kadan bai nunama Abba komiba har wajejen goma suka tashi aka shiga sallama aka tafi, ahankali Sameer ke biye dasu suka tafi Abba nadaga musu hannu, sanan Abba yakoma gida ranshi fess, kaman anmai kyautan aljanna, falonshi ya shiga yana murmushi Luba tace "Abba goron nan da sweet na miye?" murmushi yayi yace "don't worry my daughters I promise kaina sai mamanku tadawo sanan zan baku good news din" duk washe baki sukayi ganin Abba na farin ciki, yace "zan shiga study room dina, inkun gama ku kwanta" yay maganan tareda juyawa yafita yay study room dinshi, bude dakin yayi ya shiga ya zauna tunane tunane yake fall ranshi sanan ya kunna computer dinshi, wani page na italian world ya shiga kafin yadau number wajen da sauri yay dialing number da sauri yakara akunne saiyay magana. "I want full house furniture na royal Italian"...... Washe baki kawai Abba yakeyi yana wasu bayanai da banso kuji 56...... Koda suka koma gida kasa shiga falon yayi hakan yasa yawuce flat dinshi ahankali Baffa kuma ya tasa sauran yaran sukai bangaren Ummi, almost 1hr suka bata a flat din Ummi sanan suka fito Baffa da Noor da Muhammad kowannensu ya shiga motarshi dan komawa gida. Dudda irin gajiyane dake jikinshi kasa bacci yayi, wanka kawai ya iya yowa yadawo bedroom din daure da towel a waist, he is so sad he is not happy he never wish for this to turn up like this, to Yaya zaiyi, agogo ya kalla hakan yasa yabude system dinshi dake kan bed din ahankali ya shiga Skype ya shiga kiran contact mai suna Ayaan, ringing kusan hudu kafin Ayaan yadauka yana zaune a office as usual sanye da pc, yana dauka yace "1 minute buddy" tashi yayi yacire lap coat din jikinshi ya sagale sanan yakarasa gaban wash hand basin din office dinshi ya cire hand glove yasa a trash ya wanke hannu sanan yadauko wani handy yadawo yazauna yana kallon fuskan Sameer ta screen din dayaga yamai wani iri, zama yayi tareda jawo kujeran gaba yace "wats wrong buddy?" wani irin ajiyan zuciya Sameer ya sauke ya fuzar da iska mai zafi yace "I got married an hour ago" da sauri Ayaan yace "y....ou, wait are you saying you got married today ko mekake cewa ban ganeba?" cikin wani irin cool voice yace "I got married Ayaan, dazun nan" yafadi maganan tareda dafe goshin shi, shiru Ayaan yayi yana kallonshi kafin ahankali yace "Sameer you got married, yaushe kasami yarinya, yaushe akaje neman auren har aka daura, when did all of this happen batare danasani ba? So ranan nan damukai waya all you said to me akan bakada wacce kakeso u will want to marry a matured mace soja was all a lie?" girgixa mai kai Sameer yayi ahankali yace "kaima kasan your friend never tell lies" da sauri Ayaan yace "yes I know buddy, the news hit me ne kawai with shock kagane, talk to me Sameer wats happening? Besides you don't look good at all" dan lumshe ido Sameer yayi kafin yabude ahankali yashiga bashi labarin tun ranan da yahadu da Rahima harzuwa yau da aka daura musu aure yanzun nan. Ajiyan zuciya Ayaan yasauke yace "Lord! What a story, buddy in this world akwai evil people, and your worse enemy shine wanda kullum yanama dariya yana nunama yafi kowa sonka nan ko he is killing you, wlh I pity yarinyar like sosai ta mugun bani tausayi, ka burgeni da you know the father nothing akan halin matarshi kaiba munafuki bane koba komi darajan 3 children dinta masu hankali but tasani Allah baya bacci kuma wlh saiya sakama yarinyar da looks at her as mahaifiyar ta, yarinyar dake sonta tsakani ga Allah, yanzu tunda kadauke Rahima daga gidan shikenan sai muga inda zata kara ganinta tadinga bata kayan shaye shayen, and karka damu yanda Ummi ke reacting is normal every parent will act like that, ka lallabata kaita bata hakuri trust me zata sauko, kacire damuwa aranka yanda kaga abun nan yafaru haka Allah ya tsara you can't escape okay" gyadamai kai Sameer yayi taredayin dan murmushi hankalinshi ya kwanta, Ayaan yace "to yanzu wats your plan with Rahima?" dan lumshe ido yayi yabude ahankali yace "I don't have any plans, but inaso dazaran tagama rehabilitation din tadena shaye shaye ta chanza zan rabu da ita, taje ta auri mai sonta kota cigaba da school" wani mugun kallo Ayaan yamata yace "wat do you mean by kasake ta? Baxaka zauna da ita karufa mata asiri ba, kasan inta koma gidansu me Mummy zata cigaba dayine ko daga ina zata bullo" dan jim Sameer yayi saikuma yace "okay, zan nema mata wani mijin inhar tasamu tsayayye saina aurama ta shi" wani irin murmushi Ayaan yayi baicemai komiba yace "ok, yanzu dai ka lallaba Ummi, poor Ummi tagama planning how she's going to celebrate her first son marriage amma yazo ya lalata komi" hararan shi Sameer tayi yace "get back to work bye" ya katse wayan tareda kashe system din ya kwanta yay addu'an bacci yay shiru yana tunane tunane ahaka yay bacci. Da asubahi yatashi as usual wanka yayi yafito ya shirya cikin farin jallabiya yafito yatada gateman yawuce masallaci dan yasan Ummi zata tada Mu'az. Wuraren 6:30 shida Mu'az suka shigo gidan, Mu'az dukya wani koma kaman mara lafiya ganin Sameer is not happy, ganin yay falon Ummi yasa Mu'az yace "Ya Sameer yau bazaka fita jogging ba?" gyadamai kai yayi yana shiga dakin, falon babu kowa sai yar aikinsu dake goge goge tagaidasu Sameer bai amsaba yayi hanyar dakin Ummi shikuma Mu'az yasami kujera yay zaman shi a falo baiso yanishi suje gaida Ummi tare dan ko kadan baiso anama Ya Sameer fada agabanshi bashi kadaiba harsu Ya Noor ma, sun tsani suga anama babban yayan su fada agabansu wani iri sukeji he can't explain the feeling, but the feeling is uncomfortable. Sallama Sameer yayi ahankali yatura kofar dakin, hadadden dakin dake dauke da bban gado da hadaddun labulaye, Ummi na zaune kan wata Royal kujera ja dakenan ita kadai ce adakin one sitter tai relaxing bayanta tana sanye da hijabi hannunta rikeda charbi tana lazimi hada ido datayi da Sameer yasa ta lumshe ido bamatason sashi a idanunta, mugun haushin shi takeji bana wasaba, ahankali Sameer yamaida kofar dakin yarufe ya shigo yana kallonta shi kadai yasan yanda yakwshi fushin mahaifiyar shi agareshi sashi yake yaji kaman zai haukace, baida peace of mind karasowa yayi har inda take zaune ya zauna akasa, Murya chan kasa yace "ina kwana Ummi" kaman ma Ummi batasan wani hallita ya shigo dakinba haka tayi ta shareshi tacigaba dajan charbinta, jitayi zuciyarshi na kumfa Ummi maisonshi dake kula dashi kullum hakane yauke fushi dashi tamaki amsa gaisuwan ta, ahankali yasa hannunshi dakedan rawa yakama hannunta data rike charbi dashi, wani mugun kallo tamai batare data cemai uppan ba bakinshi narawa sosai yace "ki...yafemin....Ummi" dan gyaran murya yayi danji yayi muryanshi na dishashewa yace "I'm sorry Ummi, please ki yafemin" fizge hannunta tayi daga nashi tacigaba dajan charbinshi ahankali ya kwantar da kanshi kan kafafunta wasu irin hawaye masu bala'in dumine suka shigo zubomai, yakai almost 5min ahaka sanan yadago kanshi ya kawad da fuskanshi gefe yasa hannu ya goge hawayen tass, sanan ya kalleta da idanunshi dasukai ja sosai yace "kiyakuri Ummi dan Allah, zan tafi aiki karnai latti, mezan taho miki dashi inzan dawo? Akwai fruits?" ganin ko kallonshi batayiba yasa yatashi kaman wanda jinin jikinshi yakare yajuya yay hanyar kofa, hannu yasa zai bude kofa Ummi tadanyi gyaran murya da sauri yajuyo, babu alamun rahama kan fuskarta tace "in kaje dakinka ka tabbatar ka tattaro kayanka tatas ka jera a akwati kabarmin gida danyau bazaka kwanan mini agidaba, kariga kayi aure kabarmin gida kenan, and the so call yar shaye shayen matan taka koma ina kace take better go and bring her dan in mutane sunzo zasuje su ganta ba rehab zan dinga turasu ba gidanka zan turasu" tai maganan tana watsamai harara, juyawa yayi da sauri yafita daga dakin, ko kallon Mu'az dake zaune afalon baiyiba yawuce yafita Mu'az yabishi da kallo ya mugun bashi tausayi dan yaji me Ummi tacemai. Fkat dinshi yaje ya shiga sauko da akwatinan shi dan baya iya ja da maganan Ummi jiyama he regard it as kaddara ce kawai, ahankali yashiga hada kayan shi na amfani barin ma takardun shi yana tunani yagama gidan tass amma dayake aiki yatasashi agaba baibi takan zubama gidan furnitures ba, message ne ya shigo wayanshi, ajiye kaya a akwatin yayi yadau wayar, ganin message daga Abba ne yasa yabude. _"Assalamu Alaykum Son, I will really like to see you in person inkasamu chance maybe koda anjima ne I ka dawo daga aiki, sai secondary, akwai interior company danai contacting dan kayan dakin Rahima, they called sunaso suzo suyi taking measurement din dakunan dan yau zasu fara kawo kaya, I don't know how you will go about it thanks_ Dan jim yayi dan baiwani so Abba ya wahalar da kanshi shizaisa komi besides bawai auren dindindin bane yarinyar dazai rabuda ita, reply kawai yama Abba da address din gidan dan baisan mezaiyiba, hada kayanshi yayi daga bayama Mu'az ya shigo yatasashi suka hada tsaf a akwatuna guda hudu tsaf sanan ya shiga wanka agurguje yazo ya shirya cikin uniform Mu'az sai kallonshi yake, yana gamawa yatasashi suka gunguro kayan yasaka a Boot sanan ya shiga mota yatafi, hawaye Mu'az ya share na bakin ciki. Wuraren karfe goma Mummy ta shigo gidan, parking tayi tafito taci gayu sosai har wata yar kiba yakara tasa wata dog uwar atampa dayasha stone work, jakanta