Sashe 59
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa naji haushi nace yakara cemin yarinya saina marai shine Yaya Siddiqa ta daddakeni ta fizgoni ta yardani akasan wajen" tafashe da kuka, mugun kallon daya mata yasa tahadiye kuka tace "Ya Siddiqa tacema direba yatafi yakaisu Ya Luba tunda rashin kunya nakemai nai trekking to department dina kumafa duk yafi nasu nisa chan karshen school dibfa muke, shine tai tafiyanta tabarni natashi ina kakkabe jikina saiga Chris ya tayani daukan jakana yace nazo muje da kyar na shiga damuka je har an shiga lecture shine saiyaga Codeine ajakana saiyace......." tabashi labarin tsaf harda yanda Mummy saida tamaga Chriss din tace su tafi, Sameer baice komiba harta gama yana sauraronta yace "Rehab Dr ki ya sanar dani you have been taking drugs 8yrs ago, jikin ki yabasu dat record" ya kalleta kaman yanda take kallonshi yace "your Dad told me baki dade da shiga 20yrs ba, bari namiki simple mass, subtract 8 daga 20" da sauri tace "12" gyadakai yayi yace "you've been into drugs tun at the age of 12, yaran 12yrs bama susan me drugs ba, basusan akwai wani abu shaye shaye aduniya ba, children of 12yrs ko balaga basuyi ba basu mallaki hankalin suba, bama Susan menene duniyan nan ta kunsa ba, listen Girl" ya gyara zama yace "idan kika kawomin any gargada akan wanan tambayan zan baki mamaki, I need answer tell me ya akayi kika fara shaye shaye at the age of 12, ranan farko and everything" faduwa gabanta yakeyi bana wasaba Mummy tasha fadamata kar wanda yaji tsakanin su, koma menene karta sake ta kira sunanta mutane da society sun dauka shaye shaye is bad but is actually fun, da dadi su basu sani bane. "Rahima!" Sameer yadaka mata tsawa tareda kai wukan kasan wuyanta yasa tafara wani nishi kaman mai shirin mutuwa duka jikinta moving yake yawani zaro red eyes dinshi yace "tell me how did you start doing drugs, who the hell introduced you to drugs at 12yrs old, who! Yasaka mata wani mahaukacin tsawan da batasan lokacin datace "Mummy! Mummy na! Mummy nane!!" kallon kwayan idanunta Sameer yayi kafin yadan koma baya saikuma ya zauna yana kallonta bai bari yanuna mata anything ba, hawaye ta share da sauri saikuma tafashe da kuka tace "Ya Sameer dan Allah karka fadama Mummy, wlh tace duk randa nafadama wani daga ranan zata dena sona tunda ni ban rike sirrin ta amana ba please kaji, dan Allah wlh zan fadamaka amma karka fada kaji" wani mugun kallo yamata shiru tayi tace "kaga ko Ya Sameer duk duniyan nan wlh babu mai sona kaman Mummy tana sona dama dasu Ya Siddiqa data haifa, kaga su Ya Siddiqa kullum suyi ta dukana da ina kwana a dakinsu Mummy tacireni daga dakin tasa home decor tazo aka tsantsaramin dakina yafi nasu kyau, kuma kullum da daddare a dakinta nake kwana dan bana iya kwana ni kadai, kaga bayan Mama na ta karyani tabar gida nadinga ciwo zafi ko ina yakemin anata karyani ana mayarwa mummy in anamin dauri harsai Abba yakoreta dan kukanta harya kanfi nawa sabida yanda take tausayina mu dawo gida inta kuka bana iya bacci wata rana tazo da Abba yafita sallan magrib su Siddiqa basa daki ta zauna tareda rugumeni tana tofama hannun karyan addu'a tacemin zata bani wani abu dazaisa nadaina jin zafin hannun amma karan fadama kowa inaso na gyadamata kai tace kuma abin zai dinga sani farin ciki na manta da mamana muguwa my mum is wicked but she is here now, she is my Mum she loves me more than her banga bata taba dukana ba kuma bata tababa so ma manta da ita zatamin komi, tasa na kulle idona nabude baki ta naji dai wasu kwayoyi guda uku tasamin sanan ta zubamin wani ruwa mai daci nasha, ta kwantar dani ajikinta tanamin tatsubiya nai lamo ina jinta ahaka nai bacci sai washe gari natashi aiko hannuna babuma inda kemin ciwo I was so happy nadinga murna ina tsalle ina rawa itama ta tayani, dazaran naji zai fara zafi zanje dakinta nace tabani abun tacemin nabari da magrib kullum da magrib take Bani lokacin kuma saina rufe ido nadena rigima harnazo na girma, tacemin nai browsing uses of weed nayi, kagako Ya Sameer Mummy duk wani abu dazai amfaneni takemin bamatama yayanta, naga weed na bude brain hakama shisha dan akwai nikotin aciki tundaga ranan tace kullum zata dinga samin a abinci saisa in babu shi a abinci ban iyaci danna saba kuma ko nafi duka su Ya Siddiqa brain because of weed 9As nafito dashi a Waec jamb kuma naci 362, Mummy ko tsinke bata bari na daga anything dazaiban wahala bata bari nayi bana aiki nan shara ban wanki ban girki kuma insu Ya Siddiqa sunkai karana ta dakesu, su kadai keyin aikin suyi abinci su kawomin har kan gado, ran Saturday da Sunday kawai take sani nabisu islamiyya shima sai in Abba na nan sabida karya mata fada amma inhar bayana van zuwa sabida duka akeyi, su Ya Siddiqa kadai ke zuwa, in kanwar Mummy taje dubai ni kadai zatasa ama tsarba kaya dan nine autan ta, kaga yawan kayana yacika wardrobe dina some kayana ma a wardrobe dinta suke, takaini saloon kullum dani take fita, in Abba yadaken taita fushi, insu Ya Siddiqa suka daken takamatsu tace inzo in rama kaga bata bari aci zaluna, batason ta ganni cikin bakin ciki duk wani abu dazai cireni a damuwa zata bani, Mummy na bala'in sona tacemin that my wicked Mother ta taba sata tai bari bayan ta haifi Luba wai mamana tasata tai barin cikinta na boy amma bata riketa da hakaba yasa taci zaluna ba kota lalatamun rayuwa ba saidai ma tasoni sama da yanda taso nata yaran, kuma bata taba bari Abba kosu Siddiqa sun gane ba da daddare take bani nasha nai bacci, kuma Abba shi yawanci a studyroom yake kwana yana aiki sai tsakar dare yake dawowa kuma wani zubin a sati baufi yay 3daya a gida ba sauran yay tafiya saisa duk basu saniba sai ranan shima nasan Mummy ta ijiyemin ne kawai dantaga bana cikin farin ciki to tazaci da daddare zansha shine nikuma na dauka nasha alokacin nai mistake" tai shiru tana kallonshi kaman yanda yake kallonta, jikinshi yay mugun sanyi jikinshi yay sanyi, all he sees a idanun Rahima is yarinta da mugun rashin wayau, akwai yaran 20 da hankalin su is intact but Rahima kam Mummy tai brainwashing yarinya da bama tasan different between right and wrong ba, tadawo da brain din Rahima a fool, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yan abubuwan dayagani couple of times dayaje gidansu nadawo mai, maida wukan yayi cikin box din yarufe box din yana kallon Rahima dake kallonshi har lokacin gabanta na faduwa tace "ai ba zaka fadaba ko" gyadamata kai yayi yadau box din yatashi yafita daga dakin binshi tai da kallo saikuma tafashe da kuka takoma kan gado ta kwanta duk zuciyanta yaki natsuwa. Tunda Sameer yahadu da Rahima yauce rana ta farko dayaji rayuwanta da ita kanta Rahiman ta mugun bashi tausayi, a mota ya zauna yana tunanin me zaiyi dudda dai bai basani ba for now abu daya dayasani shine zaman bazai kara bari tazauna da Mummy ba, and duk inda maman Rahima take aduniyan nan he will find her kiran magrib da aka fara yasa yafito yatafi masallaci, wuraren sha biyu ya shigo dakin yaga tadade daya in bacci bayan tasha fruits salad ta koshi. Ranan bacci sosai tai da daddare bata tashi ba har sauda yatada ta da safe yace tai salla tai wanka zasu koma yau faduwa gabanta yayi shikuma yawuce ya sauka kasa dan zaiyi checking out and clear his bills, wuraren nine yadawo yaga tao wanka tana sanye da dayan doguwan rigan tai kyau dudda har yanzu da muguwa raman nan datayi hijabi yanuna mata yace "saka mutafi" dauka tayi tasaka tadau kayanta data hada a ledan suke suka fito sai kallon hotel din take tunda sukazo sai yau tasake fitowa sukai mota, gaba ta shiga shima haka hakanan saita tuna abinda tayi ranan wani kunya yakamata tada motan yayi sukadau hanya sai faduwa gabanta yake kaman akwai abinda zai faru da ita ahaka har bacci ya kwashe ta. Saida sukai parking a hanya lokacin azahar yatada ta suka shiga wani masallaci kan hanya dudda na maza ne yasa ta koma chan baya tai salla shima yay nashi agaba sanan yasaya mata snacks suka koma mota bamata iyaci ba bacci yakara awon gaba da ita. Horn dataji yasa tabude ido ganin suna kofar gidansu yasa ta gyara zama tana zaro ido gabanta nafaduwa Gate gateman yabude musu Sameer yaja motar ya shiga da ita ciki sai kallon motar Abba dayake a pake take sanan yay Parking yafito tareda kallonta, bude wa tayi tafito ahankali gabanta nafaduwa sosai sanan yafara tafiya tana biyeda shi, labewa tayi abayanshi yay knocking kofar sitting room dinsu, Zeena ne tafito tana sanye da atampa da dan kwali bamata lura da Rahima dake labe bayan Sameer ba dayake yanada tsayi, cikeda girmamawa tace "ina yini ya Sameer, Abba na nan amma Mummy taje sunan wata kawarta a Suleja gobe zata dawo...." "wa kika cikada surutu haka Zeenah" cewan Abba dake zaune a falo, da sauri Zeenah ta matsa tace "Abba Ya Sameer ne yazo abokin ka" da sauri Abba ya kalli kofan ganin Sameer yasa wani sahihin murmushi ya bayyana a fuskanshi yace "Lieutenant, bismillah, son shigo" ahankali Sameer yadaga kafa ya shiga dajin da murmushi kan fuskan shi hakan yabama Abba dasu Siddiqa daman ganin Rahima dake tsaye bakin kofan takasa shigowa kanta akasa sai rawa kafafuwanta suke sabida muryan Abba dataji, wani irin mikewa Abba yayi tsaye idanunshi kan Rahima saikuma ya kalli Sameer yace "are you together with this g irl?" gyadamai kai Sameer yayi yace "Abba ka zauna is a long story" cikin fushi Abba na danne zuciyarshi yace "wani irin long story Sameer?" ganin yanda Abba ya harzuka he is not even ready yazauna and listen to him yasa yace "Abba sarkin garin dakakai yarinyar nan tried to molest her, he tried rape her, and she called naje and rescued her" cikin wani irin fushi Abba yace "try to rape her?" gyadamai kai Sameer