Sashe 64
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Barrack dinan?" da sauri Mu'az yace "cha musu mukayi we are lieutenant Sameer Simran Sameer family and today is your birthday we are giving you a small surprise" girgixa kai yayi suka shigo gutsuro cake suna bashi har yasamu da magrib ya tarkatasu suka tafi. Washe gari! Daren jiya bakaramin fada Mummy da Abba sukayi ba, tun yana ganin abin nata shirme harsaida yace mata waito me danna auramata Sameer me eh, shima yamata kacha kacha ganin ya shareta hakan kuma zaifi jawo mata olla dan tanason jin information daga gareshi yasa tasameshi safiyar yau tabashi hakuri sanan ta tambayeshi ya ake ciki yanzu, yace mata kampanin interior sungama saka mata kaya duk wani kayan bukata data sani tundaga kan kitchen dining labulalye da sauran su sun saka, dama quotation din dasuka min nakomi was 11.9m, nabasu 8m, to inaso anjima zan basu sauran kudin, Sameer yacemin zaije Rehab Centre yadauko ta da daddare zanje gidan nafadi mata dakaina na aurar da ita" da sauri Mummy tace "zamuje tare nai kewan yarinya na" dan shiru yayi kafin yace "no tafiyan namiji daban naku na mata daban, idan uba yatashi zaije gidan yarshi shi kadai yake zuwa" shiru Mummy tayi kafin ta gyadamai kai tace "shikenan gobe ni naje naduba gida idan da gyare gyare nayi" kudi Abba yaciro dayawa yabama Mummy gashi kimata siyayya sanan yafito tareda kwallama Siddiqa kira tafito yace "yauwa kije dakin Rahima ki tattara yan kayanta zan kawo miki babban trolley na, da school books dinta kihada komi kikai motana, make sure u pack anything dakikasan tanaso fa" da sauri Siddiqa tace "to Abba" ta shiga dakin shikuma Abba yashiga dakinshi yafito dawani babban jakan Lv yashiga dakin yabama Siddiqa tahau aiki, ganin batasauri yasa yashiga tayani gwanin ban sha'awa Abba is just so happy, jiya harda sallan dare dan gani yake Allah gata yamai daya bama yarshi dake shaye shaye kamilin namiji irin Sameer. Wuraren 11 na safe yay parking motarshi agaban rehab din batare da security sun bari yay parking acikiba ya leko yace "Sir sorry, we are celebrating 20yrs anniversary yau saisa kowa anan yake parking you can come in sir" kashe motar yayi yafito Mu'az dake taredashi shima yafito yana sanye da kananun kaya, shikuma Sameer na sanye da uniform yay wani irin asirtaccen kyau ko mesa oho, sai kamshi yakeyi, rufe motar yayi suka shiga ciki shida Mu'az dake biyada shi, compound din yagani an gyara anyi decorating da balloons black and golden, ga tables da chairs da aka zuba awajen all patient dinsu maza da mata zazzaune suna shan drinks wasu nacin abinci wasu kuma nacin snacks gawani soft music natashi, all the patients looks very happy sai hira ake, dan the only thing dake joining maza da matansu is sport randa za'ai sport other than that kuma babu saiyau da aka fitoda kowa sabida 20yrs anniversary da Hope Rehabilitation centre ke celebrating, ahankali yake tafiya yana kallon koina kaman eyes dinshi is searching for someone, chak ya tsayar da tafiyan dayakeyi hango Rahima dayayi dake zaune itada wani fair guy da naman idanunshi kenan so black tsabagen shaye shaye, tana sanye da uniform dinta na rehab saidai kanta babu kodan hulan nan data saba sawa kuma anbata taki sawane sabida an mata tsifa an wanke mata kan dama ance mata yau za'a kawo mai kitso tamata, an mata parking gashin aka bata wani pink ribbon takama gashin dashi tasaki jelan gashin dayakai har tsakiyan bayanta bakin dukya kanannade abinku da coily hair, bakaramin kyau tayiba sabida gashin mutane dayawa maza da mata anata mata magana sabida yanda tai kyau tai kaman wata little angel irin yaran yan gayun nan, tai mugun kyau, damasu biyune kadai a table dinsu tana rikeda cocktails a cup da straw keciki tana zuka shikuma yagama cin rice yana goge baki yana kallonta dan yarinyar ta masifan burgeshi kaman yasace ta yakeji yasakin mata murmushi yace "finally yau munsami normal food munci, amma kullum aita bama mutum abincin magani ewwww" yatabe baki, kyalkyacewa da dariya tayi ya mugun bata dariya dudda batasan guy dinba ita kadai ke zaune yazo yasame ta yazauna ya ijiye abincin shi yana shi yahau mata surutu. Wani irin abu Sameer yaji yadaki kirjinshi ganin yanda take hirada wani daketa kallonta kaman zai hadiye ta kanta ba hula iska na kada gashinta, ahankali yashiga dunkule hannu kirjinshi namai wani irin zafi. Agurguje Da sauri Mu'az yakama hannunshi yarike gam yana kallon inda Sameer din ke kallo yace "Yayan mu itace Rahiman?" gyadamai kai Sameer yayi ahankali batare dayabar kallonsu ba, baki Mu'az yasaki yana kallonta baisan lokacin dayace "wow! My Godddd! She is so beautiful wlh" wani haushine Sameer yaji yatasomai da sauri yajuya yay cikin office din Dr dan inyaje wajen zai iya abinda he might regret yashiga yamai bayani zaidau Rahima zasu dinga dawowa as an out patient, gyadamai kai Dr yayi sanan yabashi katin next appointment din Rahima ya kwalama Asabe kira da sauri ta shigo, yace "bring all Rahima's things, and come along with the Rahima" gyadamai kai tayi yajuya tafita Dr kuma yacigaba da hira da Sameer dake amsa shi dai dai dan jiyayi ranshi yawani yi masifan baci, almost 8 minutes suka bata sai aka turo kofan dakin Asabe ne rikeda katuwar jakar Sameer na sojoji da kayan Rahima ke ciki sai Rahima dake bayanta ganin Sameer zaune kan kujera a office din yana magana da Dr dawani mai kama da Sameer din saidai ba sosai ba yasa taji gabanta yafadi da sauri ta saukar da kanta kasa, hannu Sameer yamikama Dr tareda tashi yace "thank you Dr saimunzo" sanan ya kalli Asabe yace "where is her hijab?" yamata pointing Rahima da yatsa batare daya kalletaba, hannun Rahima Asabe takama tace "wanan ko anbata hijabin bata yarda tasaka hakama hula duk suna cikin jakan nan" dagokai ahankali Sameer yayi ya kalleta kaman tasan kallonta yake itama tadan dago kai ta kallai hada ido sukayi da sauri ta sunnar da kanta, ahankali ta tsugunna tabude jakan hijabin dake saman kayan ta dauka ta zage zip din tareda zura hijabin, hannu Mu'az yasa yadau jakan ahankali yace "let's go" juyawa tayi tafita tareda Mu'az shikuma Sameer biyeda su, hakanan gabanta ke faduwa ganin a dawo ansake daukan ta again ina za'a kaita, bayan motan Mu'az yabude nata yana kallon fuskarta yace "shiga" shiga tayi ahankali tazauna batare data kalleshi ba ya maida kofan yarufe shikuma ya shiga ciki yazauna already Ya Sameer harya tada motan Mu'az narufo door dinshi yaja motar, tafiya sukai sosai sai kallon hanya take tai shiru har zuwa wani anguwa dabama tasan anguwanba duk zaman ta a Abuja, anguwan na yan gayune gidajen hadaddu, agaban wani gida Sameer yay horn mai gadi yabude musu ya shiga gidan, awajen parking taga sunyi parking, Mu'az yafito yabude mata baya ganin batada niyyan fita yace "fito Rahima" ahankali tafito su Nabila dake jikin window itada Fadila suna leke atare sukace "woww, Baby zokaga matar Ya Sameer she is so beautiful wlh" Fitowa Rahima tayi ta kalli Mu'az cikin siriruwan muryanta tace "inane nan?" murmushi ya sakin mata yace "gidan Ya Noor ne nan" da sauri tace "Ya Noor? Wayeshi" ahankali yace "muje ki ganshi kanin Ya Sameer ne" ganin Sameer haryay flat yabarsu wajen yasa yace "muje kigani" ahankali take binshi duk tajita wani iri a daidai bakin kofan taga wasu kyawawan mata sun fito da saurinsu sukayo kanta. "Oyoyo Rahima" saiga wasu maza guda biyu suma su fito dataga suna kama da Sameer sosai saidai yafisu kyau da tsayi da cikan jiki duk antsaya ana kallonta ganin yanda ake kallonta yasa da sauri ta matsa wajen Sameer batai wata wataba takama hannunshi tarike gam idanunta nataruwa dahawaye, wani mahaukacin shewa suka shigayi ganin yanda takire Sameer shiko wani kunya yaji da sauri ya karbe hannunshi ya shiga ciki itakuma su Fadila sukai bedroom dinta da ita inda makeup artist kezuwa, karasawa wajen fridge Sameer yayi yabude yadau ruwa yabude bottle din yadan kurba sanan ya maida marfin yarufe ya kalli kannin nashi dake wani kallonshi yace "lemme go back to the office" da sauri Noor yarikemai hannu yace "wlh baxaka tafiba, boys oya" to his biggest surprise gani yayi ganinshi drag him to Noors bedroom sanan suka rufe kofa wani kallo Sameer yamusu Noor yadan sosa kai yace "Yaya munsanar da friends dinka kai aure munmayi inviting some to dinner damuka hada muku by 5 anjima sai bayan magrib mutafi gidanku, yanzu su Nabila za'a fara gyara amaryan ka" shiru kawai yayi yana kallonsu baice musu komi ba, yanaji yana gani suka hanashi fita. Rahima kawai binsu take da dara daran idanunta tana gani aka shiga gyara mata kai wani gyara dabatama san kanshi ba, mai lalle namata hadadden gaske, aka kunna fanka banda AC dakin sabida lallen yay yabushe da wuri, duk wani shirin Amarya da ba'a rasaba saida suka mata harda wankan turare sanan akasa tai salla duk sukai salla, wuraren 5 makeup artist tataho aka shiga yi mata makeup nafitina aka gama tsaf wani irin kyan datayi kaman balarabiya sanan akasa tasaka wani white gown sky blue dayasha stones yana jamata kasa sosai sanan aka mata dauri, Fadila ta jawota takai ta gaban madubi tana murmushi tace "kinga yanda kikai kyau kaman fatalwa kuwa" kallon kanta Rahima tayi kafin ahankali takalli Fadila tace "mesa kuketa min kwalliya haka?" dariya dukansu suka kwashe da sauri Nabila tazo wajen rikeda Princess tace "ki tambayi Ya Sameer, bari kiga mu shirya Fadila" shiryawa suka hau yi cikin wani hadadden kaya dasukai anko itada Fadila, sunacikin shiryawa Noor yay knocking yace "baby all set fa" da sauri tace "we are coming out yanzun nan Baby" music sukaji yana tashi daga compound shiryawa sukai tsaf sanan suka fitoda Rahima dasuka rufemata fuska da net suka fito tsakar gida da ita Ya Sameer suka gani zaune kan wani royal chair yana sanye da wata bugaggiyar shadda sky blue anko shida Rahima, ga wasu friends dinshi da su Noor sukai inviting saikuma su kannenshi da sukasha white shadda da some few friends da matayen su, basu da yawa but gwanin tsari zaunar da Rahima kusada Sameer sukayi, aka shiga party ga abinci dan masu girki aka bama kwangilan girki