← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 119

Sashe 12

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaki dayan goran tsumin ta shanye sanan tadawo daki tana kallon yar kyakyawan yarinyar ta dake baccinta hankalinta kwance bayi ta shiga tayo wanka tafito salla tayi tana idarwa princess itama natashi daga baccin, daukarta tayi ta shiga bata nono tana azkar saida tasha ta ture sanan ta dauketa wanka tamata tafito ta shiryata kafin ta dauketa suyi kitchen golden morn tahada mata tabata, yarinyar ta shanye sanan tadawo ta shirya cikin English wears gabanta sai faduwa yake tana fargaban ciki, sau hudu jiya Baby na releasing a ciki, in ciki ya shigafa innalillahi baby na neman mata iskanci wlh yanzu yazatayi kuma yahanata planning, bude kofa dataji anyi yasa tadago kai dan ganin ko waye, yarinyar na ganin baban ta ta daga hannu sama alamun yazo yadauke ta tace "daaaa daaa" cikin gwarancin ta daukanta yayi yace "yes my gurl oyoyo, Dady is here" fita yayi da ita daidai Ya Sameer da Muhammad da Mu'az sun shigo gidan dukansu sanye da fararen jallabiyoyi, da sauri yakarasa wajen su Ya Sameer yamikama princess dahar tafara tsalle tanaso tafita daga hannunshi taje wajen Ya Sameer dan tagane shi tsaf hakanan yanada farin jinin yara, karbanta yayi anatse yace "oyoyo princess" murmushi Muhammad yayi harda sauke ajiyan zuciya yace "Please ku kaima Ummi ita, bari naje nayo wanka nazo" hararan shi Muhammad yayi irin kar tasan kar dinan dariya yayi yajuya bayan yama Muhammad wink da ido, Sameer na ganinsu yayi kaman bai gansu ba yajuya yawuce abinshi rike da princess a hannunshi, ganin Yayan su yay tafiyan shi yasa Muhammad yadubi Mu'az yace "bisu mana kutafi wurin Ummi nima bari naje na daukoma Ummi little" makemai kafada Mu'az yayi yace "a'a wurin Mum Little zani akwai abinda zata bani" zaro ido Muhammad yayi saikuma ya zubamai harara yace "bacci suke yanzu kadaisan jiya we came back late, bi Ya Sameer" yajuya da sauri tsaki Mu'az yayi yajuya yay flat din Ummi abinshi yabude kofa ya shiga, Ya Sameer yagaji zaune kusada Ummi data karbi Princess daga hannunshi yana rike da karamin cup na lip tea da aka dafa da na'a na'a yana sipping yana kallon news da ake nunawa a channels television news gabaki dayan hankalin shi na wurin, zama yayi kan kujera ranshi abace Ummi data bishi da kallo tace "kagama shirya kayan naka Mu'az bayau kace zaka koma school ba" tashi yayi yace "Ummi nisai anjima zan hada, zan jira sai Baffa yazo sanan zan tafi, Ummi am hungry angama hada breakfast?" "a'a ba'a gamaba saidai in zakasha tea yayanka gashi chan dining kaje kadebo" turo baki yayi yatashi yaje kan dinning din ya zauna yazuba a cup yana sha yana satan kallon yayan nashi dayaga his eyes are so fix to the telivison. Takwas na safe aka gama news din hakan yasa ya ijiye mug din ya mike yace "lemme go and shower Ummi" gyadamai kai Ummi tayi hakan yasa ya fice Ummi tabishi da kallo intace bata cikin damuwa she's lying akan batun Sameer. Wuraren 10 gabaki dayansu suna zaune afalo ana hira banda Sameer da tun dazu dayabar dakin bai dawoba sanin ya kwanta bacci safe ne kasancewan yau asabar yasa Ummi bata tura Mu'az yataso shiba tadau killace abincin shi akula gudun karyay sanyi, sosai ake hira gwanin ban sha'awa, horn dasukaji anyi yasa Nabila tace "Ummi su Baffa ne halan" Bude Gate Mai gadi yayi wata sienna ta shigo gidan, parking motar tayi wani magidanci sosai dan duk gemunshi furfura ne yafito daga motar yana sanye da manyan kaya, wata mata itama tafito sanye da wani hadadden lace, bude motar matar tayi wasu yara haka guda hudu suka fito yan mata guda uku duk suna sanye da dogayen rigunan atampa iri daya, sai namiji da bazai wuce 8yrs Bilal ba yana sanye da shadda, babban su at least zatai 22 Asiya, sai mai binta da zatai 19 Yusra, saita uku dakenan 15 Amra, suna fitowa daga motan duka yaran suka kwasa da gudu sukai flat din Ummi kafin ma sukarasa Ummi tabude kofa cikeda murna aiko saikan Ummi barinma Bilal yace "oyoyo Ummi" sun kusan kada Ummi, rungume su tayi tace "oyoyo yarana" ku shiga ciki ga yayyunku chan ciki, sakinta sukayi suka shiga ciki da sauri daidai lokacin matan da mijin sun iso rungume juna sukayi da matar tace "barka da zuwa Maman Asiya" cikeda farin ciki Maman Asiya tace "barkan mu, congratulations fa promotion din Sameer Allah yasa mucigaba da daukaka haka, Allah kuma yay albarka" Ameen Ummi tace daidai lokacin su Muhammad da Nuru da Mu'az sun fito dan dukawa sukayi cikeda girmamawa suka gaida tsohon. "Baffa barka da zuwa, ina kwana" kansu yashafa cikin muryan wanda yadan manyanta yace "kutashi, kutashi" tashi duk sukayi yay murmushi yace "Nura ya wurin aikin naka da iyali dafatan bawani matsala ko" murmushi yayi ya girgixa kai yace "babu Baffa" Muhammad ya kalla yace "kaikuma fa Muhammadu" ahankali yace "Alhamdulillah Baffa komi lpy lau" Mu'az ya kalla yace "dan yaro ya makaranta" jin ya kirashi da dan yaro yasa ya kumbure yace "lpy lau" kwashewa da dariya akayi sanan Baffa yakama kunnenshi yace "kumu shiga ciki" shiga falon sukayi har Yusra da Asiya sun dauki su Princess su Nabila suka gaida Baffa da matar su sanan hayaniyan yadan lapa, dan gyaran murya Baffa yayi bayan ya kalli kowa sanan ya kalli Ummi yace "ina Sameer?" Mu'az Ummi ta kalla tace "jeka taso Yayan ku Mu'az kacemai Baffan ku ya iso" Falonshi yabude ya shiga babu kowa a falon sai TV dake aiki, bedroom dinshi Mu'az ya shiga da sallama, babu wani haske sosai a dakin but yana iya ganin yanda yake baccin shi peacefully, babu riga ajikinshi sai wani kwantaccen Black gashi dake kwance akan huge kirjin nashi yabude kaman zai fashe tsabagen gyming, karasowa gaban gadon Mu'az yayi murmushi kwance yadan bubbuga gadon ahankali yakira sunanshi. "Yaya Sameer, Ya Sameer wake up" ahankali yabude ido dan baida wanan mugun nauyin baccin, ganin Mu'az yasa yabude idanu da kyau da hannu yamai alamu menene? Ahankali Mu'az yace "Baffa ne yazo ya tambaye ka shine Ummi tace nazo nakiraki" dan lumshe ido yayi kafin ya yaye bargon jikinshi hakan ya bayana gajeren wandon dake jikinshi daya fito da murdaden kafafunshi, tashi yayi yazauna tareda daura hannayenshi akan fuskarshi almost 1min yay ahaka sanan yazare hannu ya kalli Mu'az dake kallonshi yace "lemme shower, kace musu ina zuwa" gyadamai kai Mu'az yayi yajuya yafita shikuma yatashi yay bathroom, wanka yayi yasake brush sanan yafito ya shirya cikin wani milk yadi mai shegen laushi anmai dinki jumper, sabida mugun respect dun dayake bama Baffa ne yasa bazai iya zuwa wurinshi da kananun kayaba, links din hannun riganshi ya makala sanan yadau agogon shi yadaura a wrist, yadau manyan turarukan shi kusan kala 9 ya feffesa nan dakin yadau kamshi mai shegen dadi tazura3 takalmi, bakaramin kyau kayan sukamai ba dan cup cip sukamai sun mugun fito da surarshi dakuma tsayin shi that is the first thing dake attracting you to him, bude kofar falonshi yayi yafito yana kallon tsakar gidan yanda ko ina looks so neat, anatse nan yake tafiya irin ta maza har falon Ummi da sallama ya shiga falon Ummi daya cika da mutane sai cin snacks ake, ganinshi yasa duk kannenshi suka shiga gaidashi da matayen su amsasu yayi da murmushi kan fuskarshi kafin ya tsugunna yadauki Princess dahar ta rarrafo da gudu tazo gabanshi murmushi yamata yaja kumatun ta hakan yasa ta kyalkyace da dariya sanan ya shigo dakin yakarasa gaban Baffa cikeda girmamawa yadan duka yace "barka da zuwa Baffa" sanan ya kalli Maman su Asiya yace "Mummy ina yini" cikeda so tasakar mai murmushi tace "dana naji abin farin cikin dayasameka Allah ya sanya alkhairi, Allah ya shiga tsakanin ka da makiya, congratulations kaji Sameer yanzu abinda yarage maka kawai shine aure" gyadamata kai yayi kawai batare dayace komiba, glass cup din ruwan Swan dake hannun Baffa ne ya ijiye kan dan stool din gabanshi ya mike tsaye yana gyara babban rigan jikinshi yace "come with me Sameer" yana maganan yay hanyar stairs, tashi Sameer yayi kafin yabama Ummi daketa kallonshi Princess yace "am coming Ummi" gyadamai kai tayi bayan ta karbi Princess data sandara ihu sabida batason ya ijiyeta, murmushi yadanyi ya shafa kanta yace "sorry am coming okay" tashi yayi yay hanyar stairs Asiya tabishi da kallo kaman idanunta zasu fado kasa. Upstairs yayi yabude wani daki dakenan a gyare tsaf saiga hoton wani tsoho da Sameer ke kama dashi sosai da alamu dakin marigayi mahaifin sune, riganshi yadan daga zai zauna akasa Baffa yanuna mai kujeran dake facing nashi yace "zauna anan" yanda Baffa yamai maganan yasa yagane Baffa is very serious today hakan yasa ahankali yazauna kan kujeran kanshi akasa, gyara zama Baffan yayi yadanyi gyaran murya cikin wani irin yanayi na kamala yace "Sameer" anatse yace "na'am Baffa" dan ajiyan zuciya ya sauke yace "ina matukar farin ciki da wanan karin girman daka samu awurin aikin ka, sanan ina maka addu'a Allah yacigaba da kara daukaka ka Sameer Allah kuma yama albarka" ahankali yace "Ameen Baffa" shiru dakin yayi Baffa ya tsareshi da ido yana kallonshi tundaga kai har kafa yanda kanshi ke kasa ya natsu yana jiran yaji mezaice, ahankali yace "Sameer dago kanka ka kalleni yau magana nakeson nayi dakai sosai" dan dago kanshi yayi ya kalli Baffa nashi, cikeda natsuwa Baffa yace "da ace tayaka murnan saban matsayin dakasamu kawai nazoyi da tun afalo zan maka gaban kowa amma banyi ba nasa muka shigo nan dakin mahaifinka" dan shiru Baffa yayi sanan yace "Sameer kasan duk duniyan nan bakada wani mahaifi daya wuce niko" gyadamai kai yayi hakan yasa Baffa yacigaba "dukanku hudun nan kome zai sameku aduniyan nan dole nine zan tsayamuku, Sameer da mahaifinka yarasu da wayanka da komi kuma kaga yanda ya dinga maimaitamin narike ku amana narike ku amana" yasakeyin shiru yana kallon Sameer din dayasake maida kanshi kasa sanan yace "Sameer shekarunka talatin da takwas(38), kokuma namace sheakrun ka talatin da Tara (39) dan watan jibi zaka cika shekaru talatin da tara, shekarun ka arba'in babu daya Sameer amma bakama maganan aure, bamaka da niyyan aure, bamaka da sha'awan aure, sa'oin ka da kuka taso tare sunada yaran
Chapter 12 · 0% Book details