← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 119

Sashe 7

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M Shakur
5
& 6
Wani babban bedroom ne hadadden da everthing looks absolutely neat dakin sai kamshin turaren wutan yan maiduguri dakin yake. Mata biyu ne sunci gayu sosai wearing wani material iri daya da aka musu irin gown dinan da ake kira da dinner gown mai ruwan gold sun daura head black shima sunyi kyau kowacce na sanye da makeup akan fuskarta. Tsaye suke kan wata magidanciyar mata dake zaune kan kujeran gaban makeken hadadden mirror kwalliyan dake dakin, daya daga cikinsu namata daurin kallabi, murmushi matar tayi tana kallon matan biyun ta madubi yanda suka dage dauri sukemata, daya daga cikinsu ne dake left side din matar tace "Ummi kinyi kyau wlh sosai" murmushi matar da aka kira da Ummi tayi cikin natsassiyar calm voice dinta irin na kamilallun manyan mata tace "nagode Nabila" karasa daurin dayan tayi ta kalli madubin tana kallon fuskan Ummi ta mirror tace "yauwa angama Ummi" murmushi tamata tace "angaida Yusra sarkin iya daura kallabi" dariya Yusra tayi cikeda farin ciki compliment from Ummi kaman kyautan kudi ne dan Ummi bata fiye surutu ba ko kadan, tashi daga kan kujeran Ummi tayi ta kalli kanta a madubi ba karamin kyau tayiba wani mahaukacin lace tasa mai bala'in tsada mai ruwan gold dakeda tiny zanen flower na Black, tasaka wani sarkan zinare daya dace da shape din wuyanta da warwaron shi a right wrist dinta, ta daura fine agogo mai kyau a left wrist dinta, purse dinta tadauka Black tazura takalmi na vinci irin mara takurawan nan mai dadin tafiya tadauko wani hadadden mayafin ta yafa tadaga kai ta kalli babban agogon bangon dakin cikeda dan masifa tace "me suke bata lokaci haka ba 9 za'a faraba this is past nine shine har yanzu basu fitoba, bari naje na tattaro su su fito mutafi" tai hanyar kofa harzata fita saita juyo ta kalli matan guda biyu tace "Nabila kun tabbatar kun fadama Nani komi banson jikokina suyi kuka, makesure you set everything and tell the Nani all she needs to know" gyadamata kai sukayi atare, Nabila tace "to Ummi, ba zasuyi kuka ba matar ta iya kulada su sosai, yanzun nanma na dubosu har sunyi bacci kuma basa tashi cikin dare in sukai bacci sai gab da asuba dinan" gyadamusu kai tayi batare datace komiba tafice, fita daga flat dinta tayi tai wani flat dake bangaren wanda tafito daga ciki, shiga tayi bayan tai sallama babu kowa a falon hakan yasa tai bedroom kai tsaye tun kafin ta shiga takejin hayaniya, muryoyin maza suna surutu, bude kofa tayi ta shiga da sauri, tsit sukayi kaman basu ke uban surutu ba da akejin hayaniyar su har falo, maza hudu ne adakin, uku ne atsaye duk suna sanye da Black suit da bakaken cover shoe sunyi masifan kyau da covers kaman wanda zasuje dai wani babban occasion, sai dayan dake zaune kan gado yana sanye da wani green wando dakeda layi jaa tagefe kafarshi sanye da farin safa sai jikinshi sanye da singlet. Agogon hannunta ta kalla kafin ta kallesu duka one after the other tace a"hiranku kawai kuke tayi daman ba shiryashi kukeyi kuda kuka cemin zakuzo tayashi shiri, kunsan karfe nawa? Oya kuwuce kufita kuje falo matan ku najiranku kufito dasu kuwuce mota gamunan zuwa" ta matsa daga jikin kofan ta nuna musu kofa alamun suzo su fita, sadaf sadaf sukazo suka fice one by one har dukansu ukun suka fita sanan ta maida kofar tarufe tayo inda dayan yake zaune yana kallonta murmushi shimfide kan fuskarshi, karasowa gaban gadon tayi tasa yatsa ta dungure mai kai tareda zubamai harara tace "biyema kannenka kayi kunata surutu instead of kashirya gashi lokaci yayi" murmushi yayi batare dayace komiba hakan yasa tasake watsamai harara taja ledan dake gefenshi wanda rigan sojoji ne keciki, hannu tasa ta zaro rigan tana balle maballin tace "oya stand up" tashi yayi ahankali dogone sosai dan yamafi mahaifiyar tashi tsawo, murdadde ne bana wasaba, ga wasu shati shatin six packs dayafito ta white singlet din dake jikinshi, baki ne shi very dark, yanada wani irin bright white idanu da gashin ido sosai bakake gasu dogaye yanada cikan gira gawani siririn hancin shi dogo dayakara ma fuskar nashi kyau, bottum lips dinshi is so so pinkish sai upper lips dinkuma baki hakan yabama bakin nashi wani irin alluring kyau baida gemu ko daya hakama saje baidashi kodan sabida anhana sojoji ajiyewane saisa oho. Yanada cikan jiki dan ko kadan he is not skinny one element dayasa aka dauke shi a soja shine tsayin shi dake karamai kyau koyana cikin mutum dubu zaka ganeshi sabida cikan haibanshi da kwarjini.
Ahankali yamika hannushi ya zura cikin hannun rigan kaman yanda Ummi tabashi sanan yamika dayan hannun yasaka yana kallon fuskanta yanda take rufemai boturan rigan, Murya chan kasa yace "Ummi yaushe zaki dena treating dina kaman baby wai?" batare data kalleshi ba tana sakanmai boturin tace "inka girma"
Dan turo baki yayi kaman zaiyi kuka yay exclaiming. "Ummi!" irin shine yaro dinan, murmushi tayi batare datacemai komiba har saida takarasa saka boturan rigan sanan tadago kanta ta kallai yanda yay da fuska yasa tadanyi murmushi taja hancin shi tace "inhar namiji baiyi aureba is always considered as yaro wanda bai girma ba bakaga yanda nake baka kaida Mu'az special attention ba why because bakuda mai kula daku, ni idan katambayeni wani zubin gani nake su Muhammad da Nuru sun girmeka dan sunyi auren su harda y'ay'a" tana karashe maganan tawuce abinta, wani clean takalmin sojojin shi dake kan shoe rag tadauko mai tana kallonshi yanda yadan bata rai tace "sa takalmin muje" tsugunnawa yayi yasanya takalman ahankali tareda kulle igiyoyin sanan yatashi yay gaban mirror shi yana takun nan daidai irin tafiyan maza dinan yaje yadau hadaddun turarukan shi ya fesa, sanan yadau wani black beret na sojoji yasaka ya gyara tama fuskarshi bala'in kyau, Ummi na tsaye sai kallonshi take tana murmushi juyowa yayi hakan yasa tai murmushi tace "har angama yaron kirki?" "Ummi!" yakara exclaiming sunan nata sabida baiso Ummi nakiranshi yaro, dariya Ummi tayi tace "to nadena sojana, mutafi" atare suka jera suka fice daga flat din nashi, ganin sauran har sun shiga mota already yasa suma suka shiga dayan motan kirar jeep, jeep din dayake ciki dagashi sai Ummi sun zaune abaya sai wani saurayi da shima ke sanye da suit baki kaman sauran mazan baikaishi girma ba amma sunyi kama yaja motar yana tuki yana tauna cingum. "yarda cingum dinan tunda kaiba mace bane Mu'az" Ummi tafada anatse kaman yanda tasaba magana, turo baki yaron datakira da Mu'az yayi yacire cingum din ya manna kan glass din motar yace "Ummi me cingum dina yayi? yau promotion night din Yayan mu amma am not still allowed to have fun, oh am tired Allah kaimu gobe nakoma wana school nabar muku gidan" bata kara kulashi ba dan rigiman Mu'az daban ce cikin yaranta, kodan yaga baida kani ne shine auta oho, tunda dai yacire shikenan aje ahaka. Hankalin shi nakan tuki yace "Yayan mu, Yayan mu" dagokai sojan yayi ya kallai yace "wat is it Mu'az, u are driving u need to be focus" kaman zaiyi kuka yace "ni dama nasani danabar Ya Muhammad ya tukoku this car is so boring duk kunyi shiru kuma nima sainai shiru, kullum kuyita shiru shiru kaida Ummi magana namuku wuya I don't know why, and magana is fun u know kasan mezan fadama ne" girgixa kai sojan yayi irin whatever dinan yacigaba da amsa sakonnin da aketa turomai na fatan alhairi da congratulations ta waya, agaban tangamemen checking point din Sani Abacha Barrack dake Asokoro Mu'az yay slowing down dan akwai motoci dayawa dake gabansu da ake dubawa kafin abarsu su shiga ciki, har aka kawo kansu, saukar da glass din motar kasa Mu'az yayi harda na baya ya kunna wutar motar hakan yasa motar tai haske wanda suka gani zaune abayane yasa suka wani irin kame mai tareda saramai. "Sir" gyada musu kai yayi yamusu alamu da hannu cewa su biyu ne da wanan motar data bayan su, da sauri sukama Mu'az alamu da yatafi motarsu Ya Muhammad ma haka tabiyosu abaya, agaban wani tangamemen Hall sukai parking inda aka tanada dan parking motoci sanan suka fiffito daga motar, da sauri Ummi ta shiga gyaramai kwallan riganshi kafin tai murmushi ta kalli sauran yaran nata tace "kumuje" Allah kadai yasan iya farin cikin datake yi yau, Ummi da shi sai Mu'az ne agaba, sai sauran yaran nata maza biyu da suma ke sanye da suit ko wanen su yarike hannun matar shi sunadan hira kasa kasa gwanin ban sha'awa suna biyeda su abaya, Ya Muhammad matar shi Nabila, sai Ya Nura dasuke cema Ya Nuru shine nabiyu agidan matarshi Nabila sai Ya Muhammad matarshi Fadila sai Mu'az auta yanzu yana 400 level mechanical engineering a ABU Zaria.
Gaban Hall din kadai zai shaidamaka cewa koma menene na manya ne, wajen yasha ado sojoji kota ina rikeda bindigogi, ga different families and friends na mutane sunata shigowa tundaga gaban Hall din aka shimfida wani hadadden red carpet da aka rubuta Nigeria is proud of you akai, shiga cikin Hall din sukayi looking compose sai kallonsu ake.
Babban Hall ne da mutane ke cike makil aciki, sojoji, Family, friends, government officials, and Media personalities.
*_CHASING THE HEART CRAVINGS_*
_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_
Doesn't favor you always
Chapter 7 · 0% Book details