Sashe 47
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abba fitsari nakeji wlh tiles din bayin nan yay kal kal yau ka wanke ne?" tai maganan tana sakin hannunshi tsugunnawa tayi agaban Abba batare data cire wando ba tasaki fitsari awurin tana wakan fitsari "siiiiiiiiiiiii, fitsari futu futu, Mama da Baba suna kallona yayyyy yafitooo, agayara agayara fitsari zai shiga gidan takalmin Abba" tai maganan tana bin fitsarin datasaki da kallo dake gangarawa zai shiga takalmin dake kafan Abban ta tana washe baki cikeda mugun murna, wani irin juyawa Abba yayi cikin tsan tsan fushin daya dade baiyi irinshi ba yay ciki da sauri Mummy tabishi abaya ganin a yanayin daya juya yashiga daki tace "Alhaji kaga mezakayi eh? Kaga bakada lpy bakadade da farfadowa ba, so calm down and relax nasan duk inda Sameer yake rehabilitation centre sun riga sun kirashi, kabari ya iso ya mayar da ita please mijina karkamata wani abu, dan Allah kaji Abban su" ko kallon Mummy baiyiba tsabagen bacin rai yafada dakin Rahima yay wurin wardrobe dinta yabude kaman zai karya kofofin, babban akwatinta nasama yaciro ya yar akasa tareda budewa Mummy tabude baki tana kallonshi tace "Alhaji me haka? Koranta zakayi daga gidanne? Ina zata? Watake dashi aduniyan nan banda mu?" wajen kayan sawanta Abba yabude yadinga jido uban kayan da baisan iya yawan su ba da kalansu ba ya watsa akan akwatin haka yadin ga kwasan kayanta duk wanda hannunshi yasauka kai saiya jawo ya wurga a akwatin har akwatin ya cika yamaida akwatin yarufe yaja trolley yafito ya shiga dakinshi, drawer shi yabude yaciro wrappers din yan dubu dubu guda biyar yadauko car key duk mummy nabiye dashi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji, Abban su Abban su please talk to me my hysband dan Allah kaji, koran Rahima zakayi ne?" fitowa falon yayi yanajan akwatin batare dayabi takan Mummy ba Mummy biye dashi sukayi hanyar fita daga falon inda su Siddiqa dake gaban daki suka tsaya suna kallon Rahima, Mummy ta kwalama Siddiqa arude tace "Siddiqa kuzo kuga abinda babbanku yayi, baban ku yahado kayan Rahima a akwatin koranta zaiyi? Ina yakeso taje? Hannunka baya rube ka yanke kayar, addu'a zamu mata, addu'a makamim mumina, ka dauka Rahima itace jarabtar wanan Family namu, and I assure you babu abinda ya gagari Allah, dan Allah mijina karka korata instead ka maidata gidan Rehabilitation din" wurin kofa Abba yayi batare da maganganun Mummy sun shiga kanshi ba, da sauri Siddiqa ta tare Abban su Zeenatu ma haka duk suna kuka dan basu taba ganin mahaifin su yay fushi hakaba, ahankali Siddiqa tace "Abba mekakeyi ne ina zaka kai Rahima? Eh talk to me Abba na" cikin wani irin Kunan rai ya kalli Siddiqa yace "tashi daga gabana" yanda yama Siddiqa maganan saida gabanta yafadi da sauri suka matsamai yay wurin motarshi yabude boot ya wurga jakan ciki sanan yarufe yakoma gaba yabude motar ya kunna dantai warming sanan yadawo inda Rahima take tsugunne tai fitsari tana wasa dashi yazo wajen hannunta yakama ya finciketa ta mike tsaye tace "leave me Abba, bacci nakeji" ko takanta baibiba yajata ya wurgata a bayan mota saida kanta yabuge yamaida kofan yarufe, yakoma gaba ya shiga yatada motar gateman yabude mai yafita batare daya lura da motan su Shagali dake gaban gidansu kadan ba, wani irin fanfala uban gudu yake akan titi, ikon Allah ne kawai ke tafiya dashi saida yawuce zuba tawajejen hanyar Suleja ya tsaya awani babban farm house dinshi ya kashe motar ya fito ya shiga Rahima na cikin motar tana yaren da baiji, shiga cikin gidan yayi babban gidan gona ne dake daukeda bishiyoyi kala kala, ana kewan kifi da kaji masu kyau ciki, daga Gate ya tsaya ya shiga kwalama wani mutumi dake cikin dakin kaji kira cikin fushi. "Habu, Habu, Habu" da sauri wani dan mutumin dake cikin dakin kaji yana dubasu yajuyo jin ana kirashi ganin Abba yasa yafito da sauri yakaraso gaban Abba ya tsugunna cikeda girmamawa cikin hausan shi da bata fita da kyau tafi kaman da fulatanci yace "barka da zuwa Alhaji" cikin kunan rai Abba yace "Habu kataba bani labarin garinku dakace mini kauyen kayayau ne ko gwamnati batasan da itaba hakane?" gyadama Abba kai Habu yayi yace "kauyenmu asalin kauye ne aradu, ba wuta ba ruwa, ba waya, arafi muke wanka muyi wanki, adaji muke zuwa muyi bahaya, yawancin yan garinmu bama susan da akwai wani abu wai binni ba, wayanda kuma sukasan da binnin tsoron zuwa sukeyi wai cinye mutane kukeyi anan binni, konima wanan kaddaran nanne yafito dani daga garin dahar yau bansan akwai binni ba, sanan mutanen binnin nada kirki" ahankali Abba yace "gud, matarka nachan ko da yaranka guda tara daka fadamin?" da sauri ya gyadamai kai yace "I, duk suna chan taki yarda tadawo binni wai tanaso ku mutuwa ya kamata ta mutu a inda aka yanke mata cibiya, kudi albashina nakan raba biyu nakai mata rabi, tana saida su gyada dafaffiya, mascara, sanan baban d'ana jauro mun sayamai shanu ahirin da biyar yana kiwansu muna sayar da hura da nono a kauyen mu" gyadakai Abba yayi cikeda gamsuwa da bayanin shi yace "Habu kasan mesa nakemaka tambaya kan garinku yau?" da sauri Habu ya girgiza kai, Abba yace "kasan shaye shaye?" da sauri Habu ya gyadakai yace "nasani ba giya ba ahai ai tatil aita hauka ana layi akan hanya" gyadakai Abba yayi cikin wani irin bakin ciki yace "to Habu y'ata na shaye shaye, an kaita wurin magani tagudu, sonake kazo kashiga motar nan ka kaini garinku inaso nabama matarka rikon y'ata, inaso nakaita kauye, inda bazata tataba samun access to shaye shaye bane, bazata ga inda zata sayo abubuwan shaye shaye ba, danko namaidata Rehabilitation centre sake gudowa zatayi dan tariga tasan hanyan guduwa, kauyenku kauyen kayayau ne kuma irin wajen nake son mata harsai tayi wata ni shiddan nan tabar shaye shayen, tahakura dan kanta sanan zan koma na dauko ta, Rahima needs iron hand tana bukatan abu haka, by the time tai rayuwa irin wacce bata saba da itaba hankali zai shigeta dan kanta, zata gane gata ake mata a rehab datake samun gado ta kwana, tasamu shawa tai wanka, lokacin dataga batada wani option dayarage ta shiga rapi tai wanka, kokuma tasha ruwan rapi, kokuma ta kwanta tai bacci akan gadon kara ko kasa, tasha nono tai hamdala ta goge baki, tai kwadayin shaye shaye ta nemi inda zata samu tarasa, tai kewanmu takasa ganinmu wlh zata natsu, I believe tahakane kadai Rahima zata natsu tabar wanan mugun dabi'an na tir" da sauri Habu ya kalli Abba gabanshi nafaduwa dim dim yace "tooofah, saidai wani hanzari ba gudu ba garinmu akwai wani......." da sauri Abba yatare shi yace "zaka rikemin y'a ko ba zakayi ba na nemi wani wajen Habu?" Abba yay maganan cikin bacin rai, da sauri cikin kuma damuwa sosai Habu yace "zanyi wlh Alhaji, kaida kamin komi karufamini asiri, kabani ci, sha, tufafi da abin kwashewa na gagara maka wanan, wlh zanyi wlh" "gud rufo gidan mutafi banson jin wata magana" komawa yayi ciki da sauri yadauko key yafito yarufe gidan sanan yazo gaban mota Abba yabudemai ya shiga yarufo kofa Abba yakoma ya shiga motan yana kallon Rahima dake hauka sosai har lokacin tana wakoki, girgiza kai yayi hawaye yataru a idanunshi da sauri ya hadiye su yatada motan yaja, koshi kanshi Habu saida yaji tsoron irin gudun da Abba keyi, tun Rahima na haukanta hartai bacci. Awa takwas yadauke su suka shigo garin Gombe, Habu nata nunamai hanyar kauyensu, suka dau wani hanya wacce itace hanyar kauyen, kauye da yadauke su kusan awa biyar sanan sukakai wani daji, ahankali Habu yace "dole zamu ajiye motan anan Alhaji mu karasa da kafa dan babu hanyar motar kuma, kauyen mu chan bayan dajin nanne saisa bama asan damu ba a Nigeria nan" saukowa Abba yayi batare daya damuba Habu ma yafito boot Abba yabude yaciro akwatinta yabama Habu yace "rike wanan" akai Habu yadaura sanan Abba yabude baya yajawo kafafun Rahima dake narka uban bacci, kuka tahauyi cikin Bacci tace "sakeni" kota kanta Abba baiyiba ya kulle motar yarike hannunta gam yahau janta bacci take dan taki bude ido bin Abba kawai take luuu kaman zata fadi tsabagen karfin mix din data sha tafiya kawai suke, har dare tamusu ahanyan nan amma ko darr Abba baiji aranshi ba, sunyi tafiya kusan na awa daya akafa sanan Abba yafara hango haske hasken fitilu Habu yace "mun iso, ga kararkaran mu chan" karasawa sukayi dudda darene amma all abubuwan da Abba ke gani shine bukkoki kusan hamsin ko dari azagaye, baiga ginin gini ba saidai ginin kara dasu bukkoki, sai gaishe gaishe Habu yake dayan kwararrun mutanen dake waje kafin yakarasa chan gaba wurin wasu bukka guda biyu da bishiya ke tsakanin su, sallama ya kwada. "Assalamu Alaykum mutan gidan nanan" daga ciki aka amsa. "muryan wa nikaji kaman mai gidana" dan dariya Habu yayi saiga wata mata tafito da daurin zanu a kugu babu riga ajikinta sai wani yaro agwai data rike akan cikinta yanshan dogon nonon ta dayakai cikin ta tsabagen tsawo dayan kuma yaron na wasadshi da hannu yana surutu irin na dadin nonon nan da yara keyi, bata da kiba sosai sai tsayi da gashin kanta data tufke kaman na yar bararoji, an kitse na gefe da gefen gaban kanta guda biyu jelar gashin har wajen kirjinta, saiga wata yarinya dazata fi Rahima tsayi itama rikeda fitila tana dagawa tana haska fuskokin su ganin Habu yasa matar da saka uban tsalle nonon na lilo da sauri dan karamin yaron ya saki nono ya juyo jin maman shi ta daka uban tsalle yana kalle kalle, matar tace "wayyo Allah na mai gida kadawo, Mairo kufito ga babban ku yadawo" wasu yarane suka dinga fitowa daga bukkan Abba ya saukar da kanshi kasa ganin babu riga a jikin matar, dudda baya ganin fuskokin su da kyau sabida darene bai hanashi ganin yaron dake shan mama ba, tsalle sukahau yi har wasu mutane suna fitowa daga bukkoki su suna lekowa, ganin haka Habu yace "bamu asabari muzauna magana zamuyi ba dawowa nayiba" da sauri ta kalli yarta tace "Mairo dauko as abari babbanku yazauna" da sauri yarinyar ta shiga ciki ba'a jimaba tafito da asabari ta shimfida Abba na kokarin