← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 119

Sashe 112

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bala'in kyau kaman ba itaba, murmushi Ummi tamata tace "har an shirya kenan sudai Siddiqa sungaji da jiranki sunyi tafiyan su a binsu" murmushi tayi tace "Ummi sune sun fiye iya saurin shiryawa barin ma Ya Luban nan" dariya Ummi tayi daidai zatai magana sukaji an danna uban horn da sauri Ummi tace "yauwa tashi ga direban da Soja yaturo miki chan shizai dinga kaiki sanna yadawo ya dauke ki" gyadama Ummi kai tayi ta nannada gyalen akanta looking so decent tace "to Ummi bye" hannu Ummi tadaga mata tace "Allah kiyaye hanya" Ameen tace tawuce tafice tako tarar da direban yana sanye da kayan sojoji yana tuka wata hadaddiyar mota, yana ganinta yafito da sauri cikeda girmamawa yace "good morning madam" yay maganan yana bude mata kofar baya, ahankali tace "good morning" sanan ta shige yamaida kofar yarufe ya shiga gaba yajata sukabar gidan har zuwa school, har gaban department dinta yakaita ita abinma yabata mamaki yanda yasani tasan hala Ya Sameer ne yafadi mai. Saukowa tayi ahankali tana kallon ko'ina tana tunani rabon ta da school harta manta, ahankali tashiga tafiya har zuwa gaban department dinsu. Ajinsu, bude kofa tayi ta shiga duk an zazzzauna kaman lecturer ake jira duk an kafeta da idanu chan karshen class tayi tai zamanta tareda sauke ajiyan zuciya dan tafiyan nan datayi jitayi ta bala'in gaji, ko 3min batayi da zamaba wani lecturer ya shigo ajin, lectures yamusu na 2hrs 30min sanan yay using sauran 30min din yamusu test, tadanyi kokari a test din ba laifi sanan ya karbi scripts din tatas yawuce yafita, yan ajinma suka shiga fita yatsine fuska tayi jin tawani irin gaji kafafuwantama kaman kumbura sukayi, tashi tayi ahankali ta kalli kafafunta ganin sunyi suntum yasa abin yabata mamaki tadauki jakarta ahankali tafara takawa sosai taji tagaji komi nata ciwo yake bamatason taje department dinsu Siddiqa har zata fita taga students suna dawowa hakan yasa takoma itama takoma chan kujeran ta ta zauna danta lura wani lecturer ne yazo, zama tayi ahankali tawani irin bala'in gaji shigowa lecturer yayi yamusu 40min test sanan yashiga ymisu lectures danso yake yay covering, almost 3hrs yadauka tanaji musu lecture tun tana ganewa hartazo bata ganewa gabaki daya jitayi ma zazzabi zazzabi na rufeta da kyar suka samu lecturer yafita shima sabida yanda dalibai keta cemai zasuje suyi salla ne wuraren 2:30 yafice sanan tadauki jakarta ta mike da kyar ta iya ta tsaya jikinta wani shegen ciwo yake mata dabama tasaba dashiba haka tafito tana tafiya ahankali kaman wacce kwai ya fashewa aciki, masallacin department dinsu ta lallaba ta shiga, sanan tai bangaren bayin mata, wani irin wari dataji yasa cikinta yawani murda tahau kwarara amai a corridor bayin kafin ma tashiga ciki sai sannu ake mata, amai sosai tayi sanan wata sister ta taimaka mata tabata pure water ta karba ta kuskure bakinta sanan tafito ahankali tana nishi alwala ta daddage tayi sanan tawuce ta shiga bangaren mata zama tayi ta jingina da bango tana nishi inda tanada waya data kira Ummi, kuma yau dinma mantawa tayi data taho da wayar Ummi dan da wayar Ummi take wuni a wurin ta, wani irin mugun zazzabi takeji bana wasaba, almost 3min tayi sanan ta gyara zamanta tai salla azaune sanan tadan kwanta tana lumshe ido ko minti biyu batayiba wani irin bacci mai shegen dadi ya kwasheta awurin, har akai la'asar bata tashiba dayake bangaren matane ba'a wani cika shigowaba, har akai magrib bacci take bacci mai bala'in nauyi da dadi danko kiran sallolin da akeyi bata jisuba. Tun 4 Soja direban da Sameer yaturo mata yake gaban department dinsu, dan Sameer yacemai by 4 zai dinga zuwa yana dauko ta kullum, ganin har 5 tayi yasa yafito daga motar yataka har zuwa ajinsu dan saida ta shiga ajinsu yaga shiganta dazu sanan yawuce yatafi wanan kuma order Sameer ne, har gaban class dinsu yaje yaga babu kowa aciki, mamaki abin yabashi yace to tuntuni suka gama lectures ne tawuce ta tafi gida kokuma taje siyo wani abu ne, tunanin haka yasa yace bari yakara mata another 30min. Ganin 5:30 baiganotaba yasa ya dannama Oganshi kira, ringing daya biyu Sameer ya dauka, cikeda girmamawa ya sarama Sameer kaman yana gabanshi yace "Sir hudu daidai tamin a school din but banga madam ba, right now ma ina gaban ajinsu but babu kowa acikin ajin kaman sun tashi" dan jim Sameer yayi ranshi adan bace kosun tashi waya bata izinin bin motar haya bayan tanada mai zuwa daukanta, akufule yace "am coming" katse wayan yayi yakira Ummi, ahankali yace "Ummi ahhhh tadawo?" da sauri Ummi tace "wacece kuma ahhh?" ahankali yace "Rahima tadawo?" da sauri tace "a'a bata dawoba, su Siddiqa sun dawo suncemin dasuka gana saida suka biya ta department dinta sunga wai ana musu lectures" cikin dan fada yace "babu kowa a ajinsu yanzu, wayace ta biyo Public transport ni matata bazata dinga hawa public transport ba, wayace ta......" tsareshi Ummi tayi tace "ni kake ma bala'i dannan ko matar taka?" murya chan kasa yace "ni bada ke nikeba" ya katse wayan, saiyau yake dana sanin rashin bata waya, dama sabida shaye shayen yasa yaki siyamata waya dan zata iya takira Mummy ko wani yabata, tashi yayi azuciye yadau car keys dinshi tareda danna ma direban kira yace yatafi kawai maybe tana hanyan dawowa ne sanan ya shiga mota yafito daga Barrack din yana neman hanyar gida yana isowa gida ana sallan magrib, masallaci ya shiga yay sallan magrib. Kaman an tsikareta da allura firgigit tafarka tana kallon ko ina ganin yanda gari yay duhu yasa taji wani irin tsoro yakamata tunda tafara school dinan bata taba kaiwa ware haka a makarantar nan ba, ga zazzabi dataji tanaji sosai kotakan tayi la'asar da magrib ma da akayi batabi ba ta sunkuci jakanta tareda rikewa a hannu tana gyara dan mininin gyalen ta aka tafara tafiya ahankali tafito gajiya takeji sosai kaman wacce tun safe ke aikin dako, fitowa tayi tana tafiya ahankali tana kallon ko'ina harta karasa gaban department dinsu inda ake parking motoci ta nemi wani dan dakali ta zauna jin bazata iya kara tafiya ba koda nan da chan ne dan tagajin bala'i, gashi department dinsu shine karshen makarantan kodaga department dinsu Ya Siddiqa zuwa nata a lafiya lau ma bata iya trekking sai wanan dabamata da lafiya, ajiyan zuciya tasauke tana sauraron yanda jikinta ke daukan zafi tama rasa mezatayi yasa kawai tafashe da kuka, ita gashi ba lafiya ballema tacigaba da tafiya har gate tasami abin hawa yakaita gida, daga masallacin su zuwa parking space kaman an mata dukan tsiya, ga shegen zazzabi dake nukurkusan ta tana rasa takamaimen abinda ke mata ciwo ita kawai ta bala'in gaji komi na jikinta ya sage saikuma zafin jiki sosai. "Assalamu Alaykum lafiya baiwar Allah kike kuka?" da sauri tadago jajayen idanunta tadago kanta, wani dan saurayi ne yana sanye da normal jeans da riga sai wasu manya manyan text book a hannunshi, ganin ta tsaya kallonshi tana kuka sosai yace "I said lafiya kike kuka?" cikin kuka sosai tace "banda lafiya tun dazu naje mosque sai yanzu natashi dare tayi, bansan tayaya zan koma gidaba kuma bazan iya doguwar tafiya ba" jin yanda take kuka yasa tabashi tausayi, ahankali yace "gashi nikuma shigowa na makarantan kenan nazo nai TDB ne sabida exams din dake gabanmu, tashi to na rage miki hanya kona kaiki sick Bay ne?" da sauri ta girgiza mai kai tana share kwalla tace "ni gida zani" "to tashi muje" ahankali tafara yunkurin tashi ganin kaman ma jakan littafan nata nauye sukemata yasa yamika hannu ya karbe jakan daga hannunta sanan ta iya sauka daga kan dakalin tana biyeda shi har zuwa yar motarshi mai kyau ba laifi, bude mata gaba yayi ta shiga da zauna ahankali tareda lumshe ido, ganin ko kofar takasa ja yasa yarufo mata kofar sanan yakoma mazaunin direba yazauna yace "inane gidanku?" ahankali tana sauke ajiyan zuciya sabida dan tafiyan nan datayi tace "GRA" ita har mamaki take saikace wacce zata mutu ai dazu agida ba haka takeba daga dan wahalan nan datasha na zaman lectures a aji shine ko tafiya na neman gagaranta komi tayi ta gaji. Sosai gaban Sameer ke bugawa, ita kanta Ummi tun abin baiwani dameta ba dan acewanta keke napep tabi har abin yadameta ganin ana kiran sallan isha'i ba Rahima babu alamunta. Kasa natsuwa Sameer yayi dudda Ummi nacemai hala keke napep din baya gudune yawuce ya shiga motarshi kawai soyake yabita school din yasake duddubawa da kyau, tada motar yayi yay reverse yazo daidai bakin anguwarsu zai fita kenan wata mota na danno kai, bin motar yayi da kallo sai yaga kaman Rahima yagani ciki tana dan murmushi, hakanan yasami kanshi dayin kwana yabiyo motar abaya, adaidai kofar gidansu yaga motar tai parking, wani irin bugawa yaji kirjinshi nayi hakan yasa yay parking anesa da gidansu ya kashe motar yana kallon motar datai parking agaban gidansu. Ahankali guy din yabude mazaunin shi ganin zazzabi nukurkusan Rahima take sosai dan batada karfi ko kadan, rike da jakanta a hannu yafito yamaida kofan yarufe, sanan ya zagayo ta bangaren Rahima, ganin kofa zai bude tasa ya rataye jakan nata a hannu kaman yanda mata keyi sanan yasaka hannu yabude mata kofar cikeda tausayinta yace "fito, zaki iya fitowa?" gyadamai kai tayi ahankali tanadan kakalomai murmushi sanan tadaddage ta daga kafarta tafito da guda daya, kafarta kawai Sameer yahango yagane Rahima shine dan bai kashe wutan motarba, innalillahi wani irin tafarfasa kirjinshi ya shigayi kaman zai mutu, ganin wani kato yakawo mai matar shi gida harda rataye jakarta a hannu cikin wata irin zuciyan bala'in bala'i yabude motarshi yafito ko tsayawa maida kofar yarufe baiyiba yana tafiya kaman irin lion King dinan dayay fushi sosai ya tunkaresu daidai lokacin Rahima takarasa fitowa ta tsaya tana murmushi ahankali tace "nagode, Allah saka da alhairi" murmushi shima yasakin mata ya salubo jakarta daga kafadar shi zai mika mata kenan yaji an fizgoshi before yamasan me yake faruwa yaji saukan mari din gomasha kota ina akan fuskarshi, wani irin razanannen ihu guy din yasaki da karfi da saida yaja gateman dinsu yafito da gudu tace "kai lafiya, waye nan" Azuciye yasa duka hannayenshi ya shakemai wuya kaman zai kasheshi yace "uban
Chapter 112 · 0% Book details