← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 62

Sashe 61

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana yanzu ba su da wani sauran buri da ya wuce a sanya rana ayi bikin, wannan shi ne babban burinsu. Ammi ta sanya su Zahra suka shirya suka je gidan Baffa Abdullahi suka duba jikinsa, sun sameshi zaune a ofar gida a maina ya yi tagumi duk abin duniya y ishe shi dan yanzu hatta Mairamun ma ba ya jin da in zama da ita gashi ko gidan ya shiga sai take harararsa tana yatsina fuska kullum cikin neman takardar saki take wau ba za ta zauna da mai afa aya ba. Sallama uku suka yi amma bai san suna yi ba, dama can gidan da ya siyar suka je dubashi da yake ba su san ya siyar sa gidan ba dan afar ma ba su san an yanke ba sun dai san yana ciwon afa Sai da suka je gidan aka kwatanto musu inda suka koma da yake ba wani nisa tsakanin shine suka araso. "Baffa!" Zahra ta ce tana an tafa hannunta kusan fuskarsa, sai kallon mamaki da tausayi suke binsa da shi, dan ganin babu afar an yanke kuma ga sanda a kusa dashi duk ya yi ba i ya rame, amma banda Hauwa'u da dariyar ke neman ku uce mata dan ta san ba komai bane illa alhakinsu, sai da Ammi ta doka mata harara sannan ta danne dariyarta ta. A an firgice ya ago yana kallonsu, dan kwata-kwata bai san da zuwansu ba gashi ba dan ya san su farin sani ba da ba zai gane su ba aun canja sosai ga sutura mai kyau a jikinsu sannan kana ganinsu kasan suna cikin kwanciyar hankali dan babu alamar damuwa a tare da su gashi uwa uba ma da ya ga Zahra ta warke babu urajen babu makantar, sai ya ji gaba aya wani nauyi fa kunya sun kama shi. "Fatima, ku ne haka anan?"Ya tambaya idanunsa na cikowa da wallah, tabbas bai yi halacci ba da ya maida an uwansa ba komai ba ya wofintar da su amma duk da abubuwan da ya sha musu da korarsu da yake idan sun zo wajensa hakan bai sa sun biye wa halinsa ba. "Mu ne Baffa ya na muka gan ka kai ka ai anan ka yi tagumi?" "Babu komai Zahra" "Baffa yanke maka afar aka yi na ga sai afa aya?"Hauwa'u ta ce cike da izgilanci tana unshe dariyarta. "Yanke wa aka yi Hauwa"Ya ce yana share hawayensa. "Ke ki kiyaye ni"Ammi ta ce tana harararta. "Yi ha uri Ammi na daina" "Bismillanku mu shiga gidan"Ya ce yana kallon Ammi cike da jin kunyarta. Sandarsa ya auka tate da dogarawa ya shiga gaba suka bi bayansa har cikin gidan, daker Mairamu ta amsa musu sallama, sai wani yatsina take tana musu kallon raini babi wanda ya ya kulata haka suka zauna akan tabarmar da ta shinfi a musu.Sun gaisa tare da tambayarta mai jiki ta amsa gaisuwar batun mai jiki kwa ta bi banza da maganar.Baffan suka shiga gaisarwa da tambayarsa jikinsa ya amsa musu kan sa a sunkuye saboda nauyinsu da yake ji. Ammi ta shiga fa a masa cewa su je gidan duba sa aka kwatanto musu nan shi ne suka zo domin su masa sannu. "Nagode nagode sosai, sannan dan Allah ina ro on da ku yafe mini, nasan duk alhakin ku ne ya kamani "Ya ce cikin sanyin murya. "Lah ba komai wallahi duka duniyar ma nawa take"Ammi ta ce tana kallonsa cike da tausawa. "Nagode sosai, ke ma Zahra ki yafe mini nasan na cutar da ke na aura miki wanda bakya so na sannan da ki ka ha u da lalura ma tun sau aya da na je ban ara zuwa ba amma ga shi ku kun zo dubani baku ri eni a zuciyarku ba" "Ba komai Baffa ni dama ban ri e ka ba kuma dan Allah ka daina neman afuwata kai fa tamkar mahaifi kake a wurina" "Nagode Zahra Allah muku albarka ya baki mijin da ya fi wanda ya saka ki" "Amin "Suka ha a baki wurin fa a, ban da Mairamu da tun da ewa ta koma aki ta bar su. Haka suka an jima a gidan sannan suka yiwa Baffan sallama Ammi ta kawo 2k ta bashi, suka masa fatan samun lafiya, dan ita Mairamu suna mata sallama ma ta yale su, Baffa godiya kamar ya goya Ammi dan ji yake kamar miliyan biyu ta bashi. _Bayan sati biyu_ Mashkur ya ha a kaya na gani na fa a set biyu kaya masu kyau da inganci dai-dai arfinsa, haka matar kawunsa da ma otan ta suka ciko mota guda suka zo kawo kayan, dan dama sati hu u aka sanya bikin yanzu saura sati biyu. Zahra murna kamar me dan ita gani take kayan Mashkur in sun fi mata na Mubarak dan sosai take jun da in kayan da aka kawo mata, kuma ko da aka bu e kayan sun yi mamakin ganin kayan maau tsada ne sosai ya yi ari wajen ha a lefen. Mummy Daddy Mubarak, haka suka yiwo ayari suka zo gidan Ammi domin su basu ha uri akan abubuwan da suka faru, sun sha mamaki ganin Zahra ta warke tsaf, Mubarak sai satar kallonta yake ganin ta dawo Zahra ta asali har ma ta fi da kyau da cikar haiba dana halitta, amma ya san Zahra ta masa nisa kuma ma ai da kunya ya kalli idon su ya ce yana son ta sai dai yana fatan Allah bashi ko da wacce bata kai Zahra ba ce. Dan yanzu ya fi bu atar ma mai tarbiya da sanin ya kamata akan kyakkyawar mace duk da ya san cewa Zahra ta ha a komai. Ammi ta nuna musu babu komai wallahi ai komai ya wuce Daddy ha uri yake bata kamar ya ari baki, amma Ammi ta ce komai ya wuce dama can haka Allah ya tsara sosai suka ji da in karamcin da ta musu, haka suka tafi da nufin Mummy za ta halarci bikin nan da sati biyu duk da ta so ace Zahra ta su ce amma ga yadda Allah ya yi. _Bayan shu ewar satika biyu_ Allah sarki biki bidiri bire e, yau ya kama alhamis su Zahra amarya an sha gyaran jiki, jikin nan sai she i yake ga gyaran kan nan ya sha gyara, su Hauwa'u ma kamar ita ce amaryar ta sha gyara ita da awayenta su Hannatu ma ba a bar su a baya ba babbar awar amarya, sosai su ka gane wannan ne biki wancan myna biko ne domin kpwa yana so aure ne na soyayya da aunar juna. Tun ana saura kwana uku a fara bikin Mashkur ya ha o kayansa ya taho, dan cewa ya yi su Kawun nasa ma sa taho daga baya. Alhamis auyawa, juma'a kamu, asabar aka yi yini amarya da ango sun sha kyau kamar ba gobe an sha shagali. Ranar lahdi aka shirya aka auki amarya daga garin Zariya zuwa garin Kano domin acan ne za su zauna, a unguwar Nasarawa gida ne madaidaici mai akuna uku kowanne da bayi a ciki, sai falo guda biyu da kicin gidan ya ha u dai -dai wa dai da sannna an sanya kayan aki madaidaita amma kuma gidan ya ha u iya ha uwa.A gidan kawun Mashkur an kai amarya suka sauka domin kwana za su yi sai washe gari ne za su wuce Zariya. A da daddare ango ya nufo gidansa cikin shiga ta alfarma, ransa fari tas kamar jariri bashi da wata damuwa sai farinciki da annashuea da suka baibayeshi.Lullu e ya samu amaryar tasa, da sallama ya shiga ta amsa masa asa- asa cike da jin kunya. Sun gabatar da nafila tare da addu'o i na neman tsari tare da zama lafiya mai orewa, bayan nan ya dafa goshinta ya yi addu'a.Bayan nan suka an ta a abubuwan kusa da baki Mashkur ke bata tana kar a cike da jin kunya shi kuma sai kallonta yake cike da soyayya yana jin aunarta na mamaye zuciyarsa. Haka suka raya daren su na farko wato first night wanda suka tsinci kan su cikin jin da in tare da farinciki, auren soyayya ya yi domin komai kanaso shi ma masoyinka na so. Washe gari an kai amarya sun zo sun yiwa amarya sallama suna ta mata tsiya, sannan suka musu fatan zama lafiya da zuri'a ayyiba. _Bayan shekara biyu_ Abubuwa da dama sun faru ciki har da auren Hauwa'u da Ibrahim abokin Mashkur, da suka kamu da soyayyar junansu bayan Ibrahim in ya sanar mata yana aunarta. Mubarak ma ya samu wata yarinya a bayan layinsu mai suna Hadiza ya aura suna zaune lafiya.Shi kwa dama Nazeer yanzu yaransa biyu shi ma duk ya watsar da shirmen yanzu ya rungumi iyalinsa. Mashkur ya ginawa Ammi gida mai kyau domin yanzu sosai ya zama hamsha an kasuwa dan tun da ya auri Zahra yake ganin bu i a al'amuransa hakan ya ara tabbatar masa da cewa Zahra alkairi ce a wurinsa.Ammi ta samu wani Malam Manniru ta aura yana da mata aya da yaransa dan haka amma a gidanta take zaune. Zahra na auke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe murna wajen Mashkur da iyaye ba a magana.Zahra ta sauka lafiya ta haifi a namiji aka sanya masa Bilal suna kiransa da Bilal insa. Rayuwa ta yi kyau komai na tafiya kamar yadda ya kamata duk da dama ita rayuwa ar ha uri ce idan ka yi ha uri wata rana sai labari. Hauwa'u ma ta haifi arta mace mai suna Fauziyya suna kiranta da fauzy. Mairamu zama ya i da i har sai da ta sanya Baffa Abdullahi ya sake ta, yanzu wata ce ya aura mai suna Abu gurguwa dan gutguwa ce amma haka ya aureta dan shi ma afa aya gareshi. *BAYAN SHEKARU BIYAR* Mashkur da Zahra zaune suna ta a hira sai kuma Mashkur in yana nunawa Bilal home work, Zahra na ri e da Labiba yarinya ar kimanin watanni biyu, dan sai da Zahra ta kammala karatun ta a B.U.K sannan ta sake haihuwa suna zaune cikin farinciki da baiwa juna kulawar da ta dace. Yau ya kama Asabar dan haka su Zahra suka shirya domin zuwa shooping bayan sun fito
Chapter 61 · 0% Book details