← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 62

Sashe 29

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aki suka shiga suka bar su Zahra na arasa wankin,,, Sun gaggaisa ckn mutumci da tambayar bayan saduwa,,, Ammi sai jin babu da i ta ke na in sanar da Umman Mashkur halin da ake ciki ba. "Haba Ammin Zahra ya kuma na jiki shiru,,, babu labarin zuwa wajen Baffan na Zahra bayan kuma kinsan Babansa yana jiran jin amsa daga gareku" "Wlh Umman Mashkur ina jin nauyi ne shi yasa ki ka jini shiru,,, yadda abun ya kasance ne babu da in ji amma yanzu tunda Allah ya sa kin zo dole in fa a miki gskiyar abinda ya faru d... "Haba Fa'iza ya za ku mana haka,,, duk da ban yi zaton wani abu marar kyau daga gareku ba,,, amma tun da na ji shiru jikina ya bani akwai abinda ke faruwa,,, sai gashi yanzu ma na ga mutanen nan a ofar gidan nan" "Ya za ki min furucin daga gareki ba,,, haba Umman Mashkur,,, ko wani zai fa a miki wannan maganar ai bakya yarda ba,,, Zahra ta Mashkur ce insha Allah Zahra ba ta da mijin da ya fi shi,,, abinda ya faru shi ne... Tiryan -tiryan Ammi ta bata labarin zuwanta gidan Baffan Zahra da abinda ya faru,,, kawo zuwan Mubarak da ku a zuwan iyayensa maza da suka zo yanzu da abinda su ka tattauna. "Allah sarki ni dama ina dai jin ba da i a raina amma nasan ba za a ta a hana Mashkur Zahra ba,,, kuma tsakanin na da ke ya wuce hkn ai da kin min bayanin komai da tuni an yiwa tufkar hanci.Mu ai duk aya ne babu wani oye- oye tsakaninmu,,, da kin fa a min ma da tuni ansan abin yi,,, ba wai lallai sai Baffan nata bane za a nemi aurenta a wurinsa ba,,, su ma wa an nan un son zuciya ne yasa suka zo" "Wallahi kawai jin nauyinki ne yasa na kasa fa a miki,,, ace anin mahaifinta ya kasa bada aurenta ai abun da kunya wlh" "Babu wani abin kunya,,, ai a duniyar nan babu abinda ba zaka gani ba indai kana raye,,, wasu mutanen watsi da zumunci ba komai bane a wurinsu" Sun tattauna abubuwa da dama daga arshe dai suka yanke shawarar zuwa a fa awa Baban Mashkur in ya san yadda za ayi tunda dole dai maganar maza ce dole Baban Mashkur in ne zai yanke hukunci. Daddy a dai - dai ofar gidan Malam Abdullahi su ka faka motocinsu,,, sun fito mai machine in sai washe musu baki yake. "Ranka ya da e nan ne gidan"Yace cikin girmamawa. "A toh babu komai Nazeer fito ka je ka mana iso"Daddy yace tare da fiddo ku i kimanin 50k,,, hannun mutumin har rawa ya ke ganin ku in da Daady ya mi o masa.Rabon da ya ri e ku i mai yawa haka har ya manta,,, bai fi ya ri e 5k ba amma gashi ckn lokaci ani da yayi rakiyar da bai fi man machine na naira 100 ya ona ba amma an bashi ku i me yawa haka.Godiya har da tsugunnawa,,, daga arshe ya hau machine insa ya tafi cike da murna,,, ya bar Daddy da fargaba da tunanin yadda za ta kaya tsakaninsu da wanda aka ce anin mahaifin Zahra ne. Mairamu tana ta fama da Malam Abdullahi da ke zazza i akan ya tashi ya sha magani,,, amma ya i sai jan bargo ya ke yana rufe jikinsa har kansa,,, dan sai karkarwar sanyi yake,,,zazza in ne ma ya hanashi zuwa kamfani wurin aikin gadin da ya ke sai yana jaraba akan abi ci komai ba ba zai sha magani ba.Ita kwa Mairamu ce masa ta ke ga umamen safe nan da bai ci ba ya tashi ya ci,,, yana cewa idan ba abu mai an da i ba ba abinda zai sa ya ci tuwo ba. Suna ckn wannan tababar ne su ka ji ana rafka sallama. Malam Abdullahi yana daga cikin bargo yana karkarwar sanyi ya ke cewa. "Wallahi ko ma waye indai ni ake nema babu inda za ni,,, da dai ma za ace wani ne ya kawo min zakka to kwa da na je,,, amma haka kawai azo a cika mutum da surutun banza,,, ke in ma kin ji masu bina bashi ne ki ce na yi tafiya" Ita dai mairamu ba ta ce komai ba ta ajiye maganin da ta allo masa,,, tare da janye kwanan tuwon gefe,,, ta mi e domin zuwa ta ji wanda ke rafka musu sallama da tsakar ranar nan.Dan lokacin sha biyu ta da e da wucewa. "Alaikumus salam,,, wai waye"Ta ce daga can cikin aki kafin ta fito,,, shiru Nazeer ya yi har sai da ta zo zaure haba wa tana ganin Nazeer yanayin shigarsa da kuma wata tafkekiyar wayarsa ri e a hannunsa,,, a take duk ta rikice ta fara washe baki. "Wa alaikumus salam,,, a toh an samari kai ne mai sallama dama?" "Eh"Yace a gadarance. "Ikon Allah,,, Allah dai ya sa nan gidan ka ke nema ba wai atan kai ka yi ba ko ku a tambaya ka ke yi ba" "Eh fa ina da tabbacin gidan nan nake nema" Sosai mairamu ta washe baki tana nuna zalamarta a fili,,, da son abin duniya. "Me gidan yana nan" "Eh wlh ya...na...nan" Ta ce cikin rarraba kalamanta,,, duk ta rikice tana fatan dai Allah sa su sami ku in shinkafa a wurin mutumin nan dan da ganinshi akwai amshin mai o mai o,,, ga me gida dama ba lfy idan aka samu shinkafa ai an warke. "Ki sanar da shi alhazai ne su ke sallama a waje"Ya ce yana ha iye dariyarsa ganin duk ta ru e da jin ana nemansu da ganinta irin mutanen nan ne masu son abin duniya. "Alhazai! A ofar gidan wannan?"Ta ce tana an zaro ido tare da ha iye wani yawu,,, shikenan kakarsu ta yanke sa "Eh suna waje a manyan motoci,,, in... Ai kafin Nazeer ya arasa magana Mairamu ta yi ciki da mugun sauri har tana ha awa da gudu. "Malam! Malam!! Malam!!!"Tun daga falon ta ke rafka masa kira da uban arfi. Cikin rawar sanyi har ha oransa na ha uwa da juna ya ke cewa "Wallahi babu inda zani,,, sai ki koma ki ce na tafi gona" Hannu Mairamu ta kai za ta yace masa bargon aikuwa ya dage ya danne bargon. "Ta...shi...maza...attajirai na kiranka a waje,,, da manyan motoci da a... Kafin ta kai arshen bayanin Malam Abdullahi ya wangame bargon,,, kafin ta ankara sai ganinshi ta yi ya yi wata adungure mai ha e da shala ya wuntsilo daga kan gadon. "Attajirai masu mota???"Ya ce yana aukan hularsa tashi da wawa ya sakata,,, ko daidaituwa hular bata yi ba ya fara goge furkarsa da wani tsumma. "Hankali dai kai da baka da lfy" "Wane bani da lfy ai na warke,,, kina sanar dani na ji na warke,,, Allah sa su bani dubu uku wlh yau da shinkafa da taliya zan siyo mana" "Amin ya Allah"Tace lokacin da ta rakoshi ofar aki yana saka takalmi. Yana fitowa ya ga abin da ya so auke masa hankalin ckn walwarsa,,, manyan motoci da mota mai lodin kayan abinci ga alhazai dai duk da sun bashi baya amma ya san tabbas sai dai wani gdn su ke tambaya ba gdnsa ba.Dan Nazeer in ma fitowa ya yi lkcn da Mairamu ta shige ckn gdn. "Sannunku bayin Allah"Yace ckn ari- ari yana an lelle a fuskokinsu,,, suna juyowa ya yi tozali da Alhaji mai kamfanin da ya ke gadi. "Yawwa sannu"Su ka ha a baki wurin fa "Alhaji"Malam Abdullahi ya ce yana kallon Daddy.Daddy da bai shaidashi ba sai yanzu da ya masa magana tabbas wannan mai gadin kamfaninsa ne,,, lallai abu zai zo da sau "Malam Abdullahi"Ya ce wani murmushin farinciki yana su uce masa,,, ganin kazarsa za ta kama tarko,,, saboda sanin Malam Abdullahi da ya yi da son ku i da kuma son abin duniya. "Na 'am Alhaji in ce dai ko wani wuri ku ke nema"Yace ckn girmamawa,,, dan dai yasan bashi da matsayin da mutane kmr wa annan za su zo gidansa. "Wurinka mu ka zo"Daddy yace yana baiwa masu motar kayan abinci umarni akan su fara sauke kayan nan su shiga da su ckn gdn Malam Abdullahi. Idanu Malam Abdullahi ya zaro kan murna yana godiya har afafun Daddy ya dur usa ya kama yake godiya. ago dashi Daddy yayi yana nuna masa wannan ba komai bane. Mairamu tana ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye,,, sai sallamar samari ta ji suna shigowa da kayan abinci,,, sakin baki ta yi ita dai ta rasa bakin magana sai idan Malam ya shigo ya bata bayanin daga inda wannan zakka mai dimbim yawa take Haka suka shige da kayan abinci sai lodawa sukayi wasu kan wasu. "Da magana mu ka zo fa"Daddy yace dan ya ga duk Malam Abdullahi ya rikice ya san yanzu da wuya ya i amincewa da bu atarsu. "Mu shiga daga ciki bismilla"Yana fa a ya fara yin gaba ya fito da tabarma ya ajiye musu a zaure duk da zauren ba wani girmane da shi ba.Da ya shiga sai son jin labari Mairamu ta ke yace ta bari su tafi. Bayan sun zazzauna Daddy ya fara gabatar da bu atarsu,,, Malam Abdullahi da ke kan takalmansa zaune dan cewa ya yi ba zai zauna tabarma aya ba da su Daddy ba.Tun da Daddy ya fara magana Malam Abdullahi ya saki baki jin irin abinda Ammi ta musu lallai matar nan ta samu matsala yanzu mutane kmr wa annan ta yiwa haka. Babu ata lokaci,,, ya ce ai aure kmr anyi an gama domin yarinyar ba ta da uban da ya fishi,,, dan Daddy na cewa da a yau ma za a aura auren,,, a take Malam Abdullahi ya amince,,, Daddy ya fito da kudin nan miliyan aya ya ajiyesu a gaban Malam Abdullahi,,, Malam Abdullahi kmr ya yi aramar hauka dan rikicewa da ganin tsabagen ku Goro da alawa masu mugun yawa Daddy yasa su Nazeer suka fito da su daga boot na motarsa.Ma ota Malam Abdullahi ya shiga ya kirawo ma otansa guda uku,,, a wurin a take su ka shaida aka gabatar da aure tsakanin Zahra
Chapter 29 · 0% Book details