Sashe 50
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
inda take baya zuwa dan haka da ita da babu duk ubansu aya. Duk da daman gaba ayan su sun san junansu a waje amma haka bai hanasu farincikin kasancewar su ma'aurata ba, sun sha soyayya kamar ba gobe.A daren har kyautar wani aton zobe na gwal Mubarak ya yiwa Zee-zee dan dama ya tanadi zoben ne saboda ita amaryarsa.Kan Zee-zee ya fashe sosai tana jinta ita in wata ce aya tamkar da dubu a wurin mijin nata. Zahra kwa ko da ta san wacece Mubarak in ya auro hkn bai wani tayar mata da hankali ba dan dama ta kanta take, daga Mubarak har amaryar tasa basa gabanta.Dan a washe garin da aka kawo Zee-zee da yamma suna zaune a falon Zahra, Hannatu, sai Hauwa'u ofar kawai suka ga an turo ba tare da neman izini ba gaba aya su Zahra kallonsu suka maida kan masu shigowar Zee-zee Neesa ai wasu an mata guda biyu da Zahran bata san su ba. Sai da suka gama shigowa su duka kafin Zee-zee ta samu wuri ta zauna ta ora afa aya kan aya tana musu kallon wula anci sai taunar cingam take kamar wata akuya na cin ciyawa.Falon ta shiga arewa kallo tare da ta e baki sai kuma tace. awayena ku duba da kyau ku gani meye zai tadda kayan akina a ku i ko kyau daga ckn wa annan azaman kayan duk da ba tsohonta bane yayi anan aka tarar da su" Tace tana fashewa da dariyar izgilanci. "Ke ma da wani abu kike awata ya ma za ayi ki ha a kayanki da wa annan kayan, ba ma wannan ba ai idan miji yana yi da ke baya ta kishiyarki wannan ka ai riba ce mai tarin yawa"Neesa tace tana yatsina fuska. "Wannan haka yake"Sauran awayen suka ha a baki wurin fa Duk cikin su Zahra babu wacce ta furta wani abu, domin Ammi ta garga esu akan duk abin da za su musu matsawar ba tarkar dukansu suka yi ba kar su tanka musu, su nuna musu, su suna da tarbiya domin kowane tsuntsu kukan gidansu yake. Haka suka gaji da habaici da maganganu mararsa amfani suka gama yiwa Zahra dariyar she iyanci akan urajen jikinta wai wane namiji ne zai zo kusa da ita abu kamar aljana.Bayan sun gama suka fita ta inda suka shigo Zahra murmushi tayi mai ciwo sannan ta koma ta kwanta akan kujerar da take zaune, Hauwa'u kwa wallar takaicin abin da aka yiwa ar uwarta a gabanta amma Ammi ta hanasu babu damar ramawa.Hannatu kwa ha uri ta shiga baiwa awarta ta dan ita ma gaba aya ranta a matu ar dagule yake da halin da Zahran ta samu kan ta abin ba a cewa komai sai dai addu'a. _BAYAN SHU EWAR WATANNI BIYU_ Zee-zee ranta na matu ar suya da zugi idan ta kalli angaren Zahra tana jin takaicin cewa wai kishiyarta ce a ciki wannan abin na matu ar sosa mata ranta bare kuma idan awayenta suka zo gidan suna mata ku ubar banza akan ba girmanta bane ta zauna da kishiya a cikin wannan gidan aljannar duniya.Gidan kamata yayi ace ita ka ai ce a wurin mijinta.Dan haka ta aura amarar samo mafita akan hakan ga wani abu dake damunta shine har yau bata yi ko da atan wata ba, a son samunta ta samu ciki har ta haihu ko dan ta cigaba da untatawa Zahra amma sai gashi har yanzu shiru kake ji wai malam ya ci shirwa. Ta samu Antyn ta da maganar dan haka ta fa a mata cewa za su je wurin Malam da maganar, washe gari kwa ta sake shiryowa ta zo suka tafi, an rattabawa Malam bayani dan haka ya basu za i akan abin da suke so a yiwa Zahra tun da bata son ace tana da kishiya dama dai auren ne dole sai anyi, amma yanzu za a iya rabawa.Antyn ce tace kar a raba auren sai ya kuma tambayar ko suna so a haukatar da ita ne ta shiga gari ko kuma ta bar garin ko asar ma baki aya, Zee-zee tace ita duk kar ayi wannan kawai dai tafi so a yiwa Zahran abin da zata zauna a cikin gidan tai ta unsar ba in ciki! Ra awa Auty aikin da zai yiwa Zahran ya yi, cikin jin da i Aunty ta shiga gya a kai tare da ra awa Zee-zee abin da Malam in ya fa a mata itama dariyar farinciki ce ta bayyana akan fuskarta.Dan haka Malam yace su bar komai a hannunsa za su ga aiki da cikawa, batun haihuwa kuma yace za asan yadda za ayi za ta samu ciki.Haka suka fitar da ku i suka biya shi suka baro wurin cikin murna da farinciki. _BAYAN KWANA UKU_ Da asuba kamar kullum Zahra ta tashi domin tashin Hauwa'u su gabatar da sallar asuba, dan yau sun sha bacci ko iyamul laili ma basu tashi ba, da addu'a a bakinta ta tashi zaune wani duhu take gani sosai hakan ya sa ta yi tunanin rashin hasken akin ne ya sa ta ga hakan.