← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 62

Sashe 2

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Page 2
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
---- Jiki a sanyaye Zahra ta
auki anbirella (lema)
akinsu ta nufa domin
akko kayan da za ta canja.
akin Abbansu ne a da kafin ALLAH ya masa rasuwa,can ta nufa wanda acan ne kayanta suke ita da
anwarta Hauwa,u amma basa kwana cikin
akin a
akin Ammi suke kwana dan yanzu ma haka Hauwa,u na kan gadon Ammi tana barci abinta yarinya ce
ar kimanin shekaru shida.
Bayan ta canja kayan ne ta
an zauna jim ka
an a
akin nasu tana tunanin yadda za a kwashe da wanda Ammi ta ci bashin su dan tasan duk ranar da aka samu akasin biyan bashi ko da kuwa Ammin ta biya ku
in wani ku
in ne bai cika ba to sai fa Hajiya Rabiya ta shuka mata rashin mutunci. Mace ce mai son abin duniya kuma bata
auki yin rashin mutunci wani abu ba musamman akan ku
inta.
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta taso ta rufo lemar akanta,da sallama ta shigo
akin na Ammi amma shiru Zahra ta ji Ammi bata amsa sallamar ba.Kuma lokacin ma ruwan ya
an tsagaita bare ta yi tunanin ko
aran ruwan ne ya hanata jin sallamar.A hankali ta
araso gaban Ammi da ke zaune bakin gado ta yi tagumi da hannu biyu tsugunnawa ta yi a gaban Ammin ta sanya hannuwanta duka biyu ta
ora akan gwiwoyin Ammin.
"Ammi" Ta kira sunanta cikin muryarta me sanyi da da
in saurare kamar sarewa.Amma abin mamaki Ammi bata ma san Zahra tana yi ba duk da hannayen Zahra dake kan gwiwarta ,tayi nisa sosai cikin tunani
ura mata idanu Zahra ta yi tare da jijjiga gwiwoyin na Ammi firgigit Ammi ta yi tana saurin goge hawayen da ke fuskarta dan bata san da zuwan Zahra ba.
"Fatina har an canja kayan" Ammi ta ce cikin wayancewa dan kar Zahra ta fahimci damuwarta bata san cewa Zahra ta gama ganin komai ba.
"Ammi dan Allah ki yi ha
uri wlh ba da son raina haka ya faru ba wani ne ya bigeni da machine doyar ta
are" Zahra ta fa
a cikin muryan kuka hawaye na zuba daga idanunta kamar an kunna famfo.
Hannu Ammi ta sa ta kamo hannuwan Zahra ta dam
e a cikin hannunta,sannan ta ce
"Haba Zahra kar ki manta ni ce fa na haifeki duk duniya babu wanda zai fa
a mn halinki kuma nasan babu yanda za ayi ki min wani abu wai dan raina ya
aci ko kuma dan ki sani cikin damuwa kawai dai ina tunanin yanda za ayi na biya bashin ne kin san ba dan ruwan saman da ake ba da tuni ta zo gidan nan kar
ar bashinta in ta ji shiru ba a kai mata ku
inta ba"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji,un"Zahra ta ce wasu hawayen na zuba a idonta.
"Ammi kukan me Yaya ta ke yi?" suka tsinci muryar Hauwa,u da farkawarta kenan daga barci tana tambaya.
"Kanta ne ya ke ciwo"Ammi ta bata amsa tana kallonta.
"Sannu Yaya kinsha magani ko babu?"
"Yawwa
anwata ,eh nasha" Zahra ta ce cikin kawo
arshen tambayoyin Hauwa,un saboda shegen surutu ne da yarinyar kamar ta ci bakin aku.
"Ammi cinikin nawa Yaya ta yi a doyar da ta tafi talla?"
"Ta siyar" Ammi ta ce a ta
aice.
"yeeee yau Yaya ta yi kasuwa"Ta ce tana sakkowa daga kan gadon.
"Maza ki je ki yi alwala kiyi sallar magriba da isha,i tunda ruwan ya tsaya" Zahra ta ce cikin bata umarni dan ta san ta dinga damunsu da tambayoyi kenan idan aka jima ma tasan cewa za ta yi a bata cinikin ta gani.
"To " Ta ce tana ficewa tsakar gidan domin
auro alwala,can suka jiyo ta tana ta surutu akan anyi ruwa da yawa tana barci.Tana fita Zahra ta mi
awa Ammi cinikin 350 da ke hannunta wacce ta gama yin laushi saboda ruwa da ya ta
ata.
"Wannan fa?" Cewar Ammi cikin sigar tambaya.
"Shi ne cinikin da na yi " Ta fa
a kamar bata so.
"Allah sanya musu albarka" Ammi ta ce tana warwaresu ta irga yawansu, wanda bai fi ta biya ku
in icce ba ,dan hatta man data soya doyar bashi ne dan dai ma ita mai man bata da matsala ta san halin rayuwa sa
anin me doya da
wan nan da bata bi ko da ta hanyar da mutunci ya bi ba.
Bayan Hauwa,u ta idar da sallah dan ita Zahra tana hutun sallah,Ammi ta
akko musu doyar da ta ajiye musu a matsayin abincin dare ,Zahra dai kasa ci ta yi sai da Ammi ta matsa mata sannan ta
an ci ka
an shima ba dan ranta ya so ba.
Bayan sun kammala Zahra ta je ta rufe gidan dama Ammi ce ta ce ta dakata idan me doya da
wai bata zo kar
ar ku
inta ba, sai su rufe gidan gudun kar su rufe ta zo ta musu tijara dan cewa za ta yi dan kar su bata ku
in suka rufe gidan.Haka dai suka
an ta
a hira suka kwanta Ammi da Zahra da sa
e-sa
e ya cika musu zuciya ba su samu damar yin barci da wuri ba sai daga bisani barci
arawo ya yi awon gaba da su.
Wajen
arfe biyu Ammi ta tashi ,ta tashi Zahra suka yi alwala Ammi ta gabatar da nafilfili ita kuma Zahra ta zauna taje lazimi tunda tana faahin sallah ,haka suka kai kukansu wurin me sama wanda ko gyangya
i ko barci baya kamashi akan ya kawo masu mafita cikin halin da suka tsinci kan su a ciki.Haka suka gama addu,o insu har sai da suka ji a ransu addu,arsu ta kar
u sannan Zahra ta koma ta kwanta Ammi kwa anan kan sallayar ta zauna tana lazimi dan har
arfe hu
u ta gota lokacin shi yasa take jiran a kira sallar asuba tukunna.
********
angaren Mashkur kwa tun da ta sanya machine
insa a cikin gidansu ,alwala ya fara yi sannan ya shiga
akinsa ya canja ji
un kayansa ya gabayar da sallar magriba.A nan ya zauna yana ta tunanin yarinyar da ya
ararwa da doya yana jin mugu mugun tausayinta na ratsashi,yana fatan kar a mata duka a gida akan
arin da ya mata.
Yana nan zaune yana sa
a da warwarwa bayan ya shiga
akin Babansa acan ya tarar da Umma suna
an ta
a hira abinsu cikin kulawa sosai mahaifansa ke burgeshi a yadda kullum cikin nunawa junansu so da
auna su ke.Sa
anin gidan wasu ma,auratan da ya kasance kamar filin mahawara kullum cikin fa
a da cacar baki ake,kai wasu ma sun maida gidansu kamar filin dambe a ringa doki in doka a gaban yara.Basa tunanin komai yana iya ajiyuwa a
walwar yaran hkn kuma ba dai dai bane.Amma ga nasa iyayen suna zaune shekara da shekaru a iya saninsa bai ta
a gani sun yi ko da sa,insa bane kai koda suna yi ma basu ta
a yi a gabansa ba.Shi ma
an zaunawa ya yi aka yi dashi a ransa yana fatan samun mace kammar Ummansa dan shi a nashi
angaren bashi da burin sanya matarsa cikin damuwa indai zatayi masa biyayya to zata samu yadda take so zai zame mata ra
umi da akala ,za su yi rayuwa me da
i fiye da yadda ya ga mahaifansa na yi.
SANADIN*
*KISHIYA* *NE

*Na*

*Mmn Afrah*
Chapter 2 · 0% Book details