← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 62

Sashe 55

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ko zaki kasance na RAYUWA" Jin kalamansa take suna shigarta ta ko ina, ji take tamkar ta yi ta kuka dan murna da farinciki tabbas a halin da ake ciki yanzu ba kowane namiji bane zai iya maka haka har ya ri e maka al awari. "To me ya hanaka zuwa?" "Nauyin ubangiji nake so ki gama saukewa" "Ban gane ba ?" "Idda nake so ki gama Zahra, tun ranar da Umma ta sanar da ni mutuwar aurenki nake oki da murna in zo in ganki, ga kuma larurar da ta sanar min ta sameki sai na ji kamar in zama tsuntsu in ganni a Zariya, amma daga bisani sai na yi tunanin bai kamata na zo gurinki ba kina idda kamata ya yi in bari ki kammala idda a lokacin ne zan ji da in kasancewa da ke domin kin gama sauke nauyin ubangiji shi yasa na fara lissafi a jiya ne kika gama iddar ki shi ne ni kuma na zo yau domin na san ko a yau za a iya aura miki aure!" Ikon Allah Zahra ta ce a cikin zuciyarta lallai Mashkur da ban ne, tabbas halayyarsa da zurfin tinaninsa ya ara duk inda mutum zai yi tunani. "Allah sarki lallai ka cika mai dogon nazari da hangen nesa, dama ina ta shakku da tantama akan cewa za ka gujeni " "Allah sarki Zahra ai babu wani abu da zai sa na gujeki" "Nagode warai da gaske, ina alfahri da kai a matsayin masoyi" "Ni na fiki alfahri da kasancewarki abar aunata" Shiru ne ya an biyo baya yayin da ya kar i sandar ya ri e a hannunsa ya zuba mata kyawawan idanunsa tamkar yau ya fara ganinta. "Kallona ka ke ko? Duk da cewa a makance nake kuma fata ta babu yan gani amma a haka kake kallona, ai da idanun nawa a bu e suke suna iftawa ma amma bana gani daga baya ne suka rufe ruf" Tun da ta fara bayanin yake kallonta cike da tausayawa. "Duk matan duniya babu macen da zan iya kallo sai ke sannan ban damu wai baka gani ba ni kawai abar aunata nasani ke nake so duk yadda ki ke" Kai ta sunkuyar tana ji a ranta bata da kalaman da za ta yi amfani da su wajen gode masa.Ganin ba ta ce komai ba ya ce "Ina su Ammi suka je?" "Sai yanzu ka lura basa nan?" "Ke ma kina gwada halin asarmu ko, a maimakon in an yi tambaya a baiwa mutum amsa amma sai a ara masa tambaya" Dariya ta an yi har ha waranta wanda suke jere tamkar masara suka bayyana suna walwali. "To kai in ne da baka tambayi su Ammin ba sai yanzu,sun je gidan suna su dawo" "Ai kin san hankalina gaba aya a kan ki, kuma dai na lura ma basa gidan da ace suna nan da na gan su, Allah dawo da su lafiya" "Hakane kuma, amin ya rabb" Ta ce tana murmushi Haka su ka cigaba da hirar su cikin farinciki da kwanciyar hankali da kalamai masu taushi da da in sauraro ga masoya tabbas su kan su sun san sun yi kewar junan su.A haka har aka fara kiran sallar magriba, yana shirin tafiya su Ammin su ka dawo sun gaisa sosai da tambayar bayan saduwa, sannan ya tafi daga nan ma amsalllaci ya wuce domin gabatar da sallar magriba. _Zee-zee_ Rayuwa gaba aya ta juya mata baya kullum tana cikin damuwa da fargabar zamantakewarta da mijin nata Mubarak, domin gaba aya ya birkice mata ban da wula anta ta babu abin da ya yake ha a su na arzi i dan gaba aya ynzu ji yake kaf duniya babu wacce ya tsana sama da Zee-zee. A wurin iyayensa ne ma take samun an salama to su ma tun da suka fahimci cewa babu wani ciki da take dashi dama sharri ta yiwa Zahra sakamakon jin ta da Mummyn Mubarak ta yi tana waya tana sanar da cewa duk abin da ya faru har aka saki Zahra ba kowa bane silar yin hakan sai ita, sai da Mummyn ta gama jin komai wannan yasa gaba aya suka dawo daga rakiyarta.Dan Mummy har gida ta je ta ara baiwa su Ammi ha uri. Da ka an-ka an Mubarak ya dawo hayyacinsa daga dogon suman da su Zee-zee su ka jefa rayuwarsa na kawar masa da hankalinsa.Tun da ya fahimci abubuwan da ya yiwa Zahra tun daga washe garin tarewarta a gidansa daga bakin Mumuynsa wannan yasa ya ji duk duniyar ta fita a ransa, sannan ya yi matu ar yin da na sani akan abubuwan da ya yiwa Zahra duk da ya fahimci ba a hayyacinsa ya yi komai ba amma dai tabbas ya yi ba inciki musamman da ya ji labarin babu wani aure tsakaninsa da Zahra har sai idan ta auri wani mijin. Ya matu ar tausayawa Zahra hakan ya sa ya ke jin kunya da nauyin tunkarar gidan su domin zuwa ya basu ha uri da duk abubuwan da ya mata. Zee-zee ba su daddara ba ita da Auntyn ta wajen bin wasu malaman dan suna ganin wanda ke musu aikin kamar ya gaza amma duk yawon da su ke a bamza dan al'amuran Mubarak in kullum gaba su ke basa baya, hakan yasa su ka dawo suka zubawa sarautar Allah ido domin ko da wasa ya hana Zee-zee ta ji da in rayuwarta. SANADIN KISHIYA NE NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE3
Chapter 55 · 0% Book details