Sashe 11
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page in naki ne MAMIE YUSUF DABO marubuciyar SOYAYYA DA ZUMUNTA & AMINCI KO AUNA ina tayaki farincikin haihuwa lafiya kin samo mana baby boy Allah rayashi ya baki lafiyar shayar mana dashi.Su queen fulani nadiya ibrahim beauty cigari mu ha e a gidan suna PAGE BANYI EDITING BA ----------- Da magriba Zahra ta cire yawarta a caji ganin babu missed call bare message in Mashkur abin ya bata mamaki matu a ,tunda tasan dai yau Mashkur zai zo hira kuma ma ko ba zuwa zai yi sukan yi waya ba adadi a rana saboda basa yin nisa da junansu.Amma yau gashi tunda ta dawo daga scul bai kirata ba tun tana sanya ran ganin kiran nasa har abin yazo yana damunta gaba aya ta kasa sukuni domin sun matu ar sabo da juna basa iya yin nisa da juna gaba aya sai su tsinci zukatansu cikin kewa marar misali Ajiyar zuciya ta sauke tana maida wayar caji ,ganin cajin yayi full ma sai ta cire ta wurga wayar kan gado ta zame ta kwanta akan sallayar da tayi sallar magriba,idanunta ta lunshe tana sauraron bugun zuciyarta da ke kai kawo a hankali.Hannu ta sanya a fuskarta tayi tagumi tana jin wani iri duk damuwa ta cika mata zuciya ,dan a iya zaman da sukayi da Mashkur bai ta aukan dogon awa guda ba tare da ya kira yaji lafiyarta ba ,koda kuwa tana scul ne.Shi yasa gaba aya kewarsa ta addabi zuciyarta ,gashi babu credit a wayarta kuma tana jin nauyi ta tambayi Ammi .Juyi ta yi ta koma rubda ciki ta danne irjinta saitin zuciyarta wanda anan ne take jiyo damuwar na fitowa,idanunta rufe ruf sai jin Hauwa,u tayi ta shigo akin dan dama suna waje ita da Ammi suna jin rediyo ita kuma saboda dauwar dake ranta sai kawai ta ji tana son ka aicewa ko ta samu damar yin tunanin abin so da aunar zuciyarta. "Ya Zahra " Da sauri Zahra ta tashi daga kwancen da take ,duk tunaninta Mashkur ne yazo ya aiko a mata magana wata ila ko bashi da caji a waya ne ,kai tama fi tunanin wayar fa uwa ta yi. "Na,am"Ta fa a tana kallon Hauwa,u dake neman wurin zama. " Ya kika zabura kamar wanda ta ga abin tsoro ?" Tace lokacin da ta zauna tana dariya. "Waye ke kirana dan Allah Hauwa,u?" Ta tambayeta kamar za tayi kuka dan ita ka ai tasan abin da take ji a ranta. "Waye kwa ke kiranki ba kowa kawai dai nice naga muna waje muna shan iska ke kuma kina aki ko zafi ma bakya ji shine nazo inji ko baki da lafiya" Shiru Zahra ta yi ta koma ta kwanta dan kwata-kwata batayi zaton jin hakan ba. "Bana jin zafi kuma ki fita ki bani wuri bana cikin yanayin da nake son wani ya kusanci inda nake inason ka aicewa" "Ayya su Ya Zahra masoya kodai waya ake aka kashe dan kar inji"Tace cikin tsokana ganin Zahr bata bi ta kanta ba sai ta fice tana cewa. "Allah dai ya kaimu aurenku musha shagali" Zahra ara rufe idanunta tayi ba tare da ta maidawa Hauwa,u martani ba,tabbas yau ta tsinci kanta a wani yanayi marar misaltuwa ashe haka nisa da masoyi yake bata sani ba? Tabbas soyayya tayi a rayuwa saidai zafinta da kuma yanayin da zukatan da suka kamu da so kan kasancewa shine wataran soyayya ta sanyaka farinciki wataran kuma akasin haka dama haka rayuwa take! Tana a haka sai jin muryan Ammi tayi tana tashinta ashe ma har barci arawo ya saceta bata sani ba. "Har anyi sallar isha,i kina nan ashe barci ma kike" "Eh wlh barcin ne ya aukeni" Ta ce tana tashi zaune tana murtsuka ido. "Ai dama wannan makaranta da kuke tafiya dole akwai gajiya ki tashi kiyi sallar sai ki ci abinci ki kwanta saboda kar ki makara gobe"Ammi tace mata tana aukan kwano. "Bari dai inyi sallar sai in kwanta dan bama jin yunwa azu naci abinci"Ta fa a tana mi ewa.Fita Ammin tayi,Ammi na fita Zahra ta akko wayarta daga kan gado a tunanin zata tarda masoyinta ya kirata da barci ya auketa ,tana akkowa taga 2 missed call da sauri ta bu e dan gani amma sai taga Hannatu ce ta kirata.Cikin sanyin jiki ta ajiye wayar ta fita ta auro alwala ta tada sallah. Bayan ta idar net ta aura ta shiga ta kwanta tana jiyo Ammi da Hauwa,u suna hira abinsu.Ganin barcin ya i zuwa kuma da alama dai ba zuwa zai yi sai faman tunani da sa e -sa e take.Tashi tayi ta fito daga akin ta zauna kusa da Ammi tace "Ammi dan Allah ki baiwa Hauwa,u 100 ta siyo min kati zanyi amfani dashi.Murmushi Ammi tayi dan dama tana lura da Zahran kamar akwai abinda ke damunta,duk da tasan zancen gizo baya wuce na i amma yanzu ai ga abin oye ya fito sarari. "Ya Zahra kodai Ya Mashkur zaki kira?"Hauwa,u tace cikin zolaya lokacin da take saka takalminta.Banza Zahran ta mata Ammi ce ma ta bata amsa da cewa "Kedai bakya rabuwa da neman magana". Hauwa,u na kawo mata katin ta kar a ta shige aki ,hannunta har karkarwa yake lokacin da take loda lambobin ,tana sa hash ta ga katin bai shiga ba,sake loda lambobin tayi amma dai katin bai shiga ba.Sai da ta sanya sau uku sannan ya shiga ,da sauri ta shiga dialing call ta kamo number Mashkur in amma sai ta jita a kashe. aya layin nasa ta kira shima dai a kashen aka ce mata,a wurin ta zame ta zauna tana mai jingina sa jikin gado dan wannan ya ara tabbatar mata da zargin da zuciyarta ke mata akan cewa ba lafiya ba.A take ta fara amabaton Allah ,tana addu,ar Allah sa lafiya idan kuma wani abune ya faru Allah Ubangiji yasa abin yazo da sau angaren gidansu Mashkur kwa Ibrahim ne abokinsa yaje ya kai musu labarin abinda ke faruwa,sun shiga tashin hankali sosai na jin abinda ya faru dan sun san yanzu sai dai su fa awa Allah ya shige musu gana dan sunji cewa yaron an gidan masu hannu da shuni ne kuma ynzu al,amarin asarmu Nigeri,a sai a hankali dan kana ji kana gami za a danne maka ha inka saboda kai ba kowan kowa bame ma,ana baka ajiye ba baka baiwa wani ajiya ba. Ibarahim in ne ya musu jagora zuwa police station in dan an fa a masa police station in da aka kai Mashkur in.Napep suka shiga Baba da Umma a baya sai Ibrahim in ya ahiga gaba kusa da me napep in.Yana ajiyesu suka nufi cikin police station in nayan sun gaisa da an sandan da suka samu a wurin sai Ibrahim in ya musu bayanin abin da ya kawosu ya kuma gabatar musu da kansa a matsayin aminin Maahkur da kuma su Baba a matsayin mahaifansa. "Tab i kuce wurin makashi kuka zo" aya daga cikin an sandan ya jefa musu wannan tambayar "Makashi kuma?" Su duka suka jefa masa tamabayar a tare cikin ki ima da kuma tsantsan tsoro da fargaba da ya bayyana a fuskokinsu. "Ai kun ji abinda nace amma sai kun nuna cewa ku an Nigeri,a ne wato in aka tambayeku maimakon ku bada amsa sai ku ara maido da tambaya" an sandan ya ara fa a yana wani hura hanci shi ala dole an sameahi akan aikinsa. "Mu dai an ce mana sunyi fa a da wani amma ba mu san zancen kisan kai ba"Baban Mashkur ya fa a yana kallon an sandan ,amma ko a ransa bai yarda cewa ansa Mashkur zai yi kisan kai ba, tunaninsa ma ba zai bari ya kai can ba. "To da kake ha ancewa wurin yin bayani menene marabar dambe da fa a? Yaron da ya samu an mutane ya maida masa fuska kamar mota ta masa dameji,kuma ni a ganina wanda zashi sama ya taka leda ai yaci arfin tafiya" Shima ayan police in ya fa a yana an rubuce rubuce a wani littafi. "Dan Allah kuyi hakuri mu dai ganinsa muka zo ,sannan ma mun taho harda ku in belin insa"Cewar Ibrahim kuma ya sako maganar ku in beli ne dan ya san wasu ann sandan da son ku i kamar me. us sukayi a tsakaninsu,jin zancen ku i sai kuma ayan yake ra awa ayan cewa wannan mutanen basu da ku in da alhajin nan mahaifin yaron nan zai basu,kuma ko jiya dubu ari ya bada kuma zai kawo wasu.Hakan ya yasa suka ce ai su Ibrahim in ba zasu samu damar ganin Mashkur in bare har aje ga basu belin insa dan lefin da yayo mai girma wata ila ma abin ya kai ga kotu ayi shari,a in ma ta kama har gidan kaso sai an kaishi. Wannan batu da suka ji ya matu ar tadawa Umma hankali duk da suma su Baban sun razana da jin hakn dan aun san yanzu asar sai a hankali kana da gaskiya sai a baiwa maiku i gaskiya kai kuma ko oho "Shikenan babu komai mu zamu tafi amma ku sani Allah yana bayan mai gaskiya kuma duk nisan jifa asa zai fa o sannan idan baku anta ba lokacinda za a aukeku aikin nan sai da kukayi rantsuwa akan cewa zaku yi gaskiya!"Baba yace yana kallon Umma dake share hawaye. "To munji wlh bamda ma kaci sa,ar furfura da kaima sai mun ha aka da an naka mun kulle ,kuma ka sani dan gobe ake wankan dare,tunda dai yanzu an naka bai zo hannunka bare kace za ka fa i magana son ranka" an sandan yace yana buga kantar wurin da hannunsa. "Dallah yalesu gayyar tsiya arna a idi,ai wlh cin abimcin kishiya ramako ne,kuma dan tuwon gobe ake wankin tukunya sannan harbi ga wutiya yafi kuskure" aya an sandan ma ya fa "Ibrahimu ku zo mu tafi"Baba yace cikin sanyin jiki yana juyawa su Umma suka take masa baya.Haka suka koma gida Ibrahim ya musu sallama ya tafi,haka sukayi ta jajanta maganar ga damuwa a ransu,yaro ya fita nema amma a kawo machine insa goda ace shi kuma yana hannun an sanda tabbas akwai tashin hankali! Mubarak kwa tunda aka je asibitin nan ,ya ara