← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 62

Sashe 47

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

sara masa sai wani farinciki da ya mamaye masa zuciyarsa saboda muryarta da ya tsinkaya. "Kiyi ha uri ban manta da ke ba, ni kaina bansan mai ya aukeni ba na kasa tunawa da ke sai yanzu da naga kiranki a take naji wata sabuwar soyayyarki ta sokeni a zuciyata" Yace yana jin wani nisha i da jin muryar Zee-zee. "Ba wani nan bayan kayi aurenka kana can da amaryarka ka manta dani" "Ke dalla wa yake ta amarya, amarya ko jidali" "Kamar ya?" "Ki bari kawai Baby, ai ni wannan auren nayi da na sanin yinsa" Wani mugun da i ne ya rufe Zee-zee jin kalaman Mubarak sun tabbatar mata da komai ya tafi kamar yadda Malam ya tsara kasancewarsa, domin alamu sun nuna cewa babu wani abu daya faru tsakanin Mubarak in da Zahra, sannan kuma ta fahimci cewa son Zahra da ke cikin zuciyar Mubarak in ya dan are wanda hkn duk cikin aikin Malam ne.Ga kuma uwa uba yace bai manta da ita ba lallai komai yayi dai -dai sai aure kawai ya rage tsakanin su. "Da na sani kuma" "Eh ke dai bari kawai" "Amma na jajanta maka ha en guy kamar ka amma yake da na sanin yin aure" "Bar maganar nan, ki shirya zan shigo da la,asar mu fita mu an huta" Wani irin ihu Zee-zee ta saki jin abin da Mubarak yace, sannan ta maida wayar kunnen ta tace "Ina jiran zuwanka" "Ok bye"Yace tare da kashe wayar, shi ma yana kashewa ya mi e tsaye tare da naushin iska yace ."Yess"
Chapter 47 · 0% Book details