Sashe 48
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji ya yi an banko ofar da arfi, Daddy ne ya shigo a fusace yace "Wai Mubarak me yasa baka da hankali ne, ya zaka bar yarinyar mutane da lalura kana gudunta maimakon ace yanzu kana neman yadda za a yi a nemo mata magani ko ta samu lafiya amma sai kuma kake wasu abubuwa kamar mai ta in hankali"Daddy ya arasa fa a cikin acin rai. Mubarak sanyaya muryarsa ya yi saboda Daddy yaji tausayinsa yace "Dan Allah Daddy ka yi ha uri nifa ba wai gudunta nake ba ya za ayi na guji matata, amma Daddy ka duba yadda jikinta yake wlh Daddy idan na tsaya zan iya suma kasan dai can dama tun ina yaro ina da tsoro abu ani yana firgitani bare kuma wannan kana ganinta kasan mutum idan yana kallonta ka ai zai iya yin mafarki"Yace yana langa ar da kai gefe. Wani tausayin Mubarak ne ya kama Daddy, sosai yaji tausayin an nasa na shigarsa a take yaji yafi tausayin ansa akan Zahra dan Allah ka ai ya san me ta yiwa Allah ya jarabceta da hakan.Amma ansa bai jiba bai gani ba azo ana bashi tsoro tabbas da sake. Fara takawa yayi a hankali ya arasa gaban Mubarak in tare da janyoshi jikinsa ya rungumeshi yana jin aunar an nasa na ratsa dukkan sassan jikinsa. "Ka kwantar da hankalinka babu mai takuraka kaje inda take, dan babu yadda za ayi na za i wata a kanka amma dai za a nema mata magani a matsayinta na matarka" "Godiya nake Daddy" "Ka fi arfin komai, jeka ka shiga wankan kaji" "To Daddy" Yace tare da janyewa daga jikin Daddy yana an murmushin samun nasara. Yana shiga bayi Daddy ya fito daga part in, ya koma part in Zahra, ganin suna kuka ita da su Hannatu ya dakatar da su tare da cewa su shirya za su tafi asibiti.Ita dai Mummy da to kawai ta bishi dan ita ta ma rasa a ma'aunin da za ta saka abin da ya samu Zahra. Sun shirya tafiya Mummy tace Hannatu ta zauna ta yi girki su je su dawo.Haka kwa akayi sai da suka fito Mummy tace Hauwa'u taje ta kirawo Mubarak su tafi, amma Daddy yace wai zazza i ya rufeshi ba sai an je dashi ba, ita dai Mummy mamaki ya hanata magana kuma bata so ta cika Daddy da tambaya a gaban su Zahra dan hakan zai iya kawo raini dan ta san maganar ba haka take ba. Daddy ne je jan motar dan dama ru ewar tunanin halin da Mubarak yake yasa ko direba basu taho dashi ba, Mummy a gaba sai su Zahra a baya. A wani katafaren private hospital Daddy yayi parking.Asibiti ne da ya amsa sunansa domin akwai wararrun likitoci wanda suka san aikinsu da warewa, hakan yasa asibitin ya zama mai matu ar tsada sai dai akwai biyan bu ata domin komai ana yinsa ne cikin warewa. Office in babban dector in wanda asibitin yake mallakinsa ne suka nufa, su Mummy sun samu wurin sun zauna shi kuma Daddy yayi nocking ofar office in, izinin shiga aka bashi bayan sun gaisa da Doc in dama sunsan juna anan Daddy ya shiga fa a masa abin da ke tafe dashi bai yi mamaki ba dan sun saba da irin wa an nan dan indai abin da ya shafi fata ne suna da skin Doc wanda gaba aya yayi karatunsa ne akan fata dan haka , shi ma kuma mai asibitin ya san abin da ya shafi angaren fata dan shi ma karatu ya yi na angarori da dama sai dai akwai inda yafi warewa. A nan aka tafi da Zahra wani akin gwaje -gwaje domin duba menene ainihin mafarin ciwon nata, da kuma yadda za a magancesa.Abin mamaki duk na'urar da aka gwada domin gane cutar Zahra babu abin da na'urar ke nunawa, abin ya baiwa likitocin mamaki dan dama tun lokacin da suka yi tozali da jikin Zahra suka yi mamaki tare da jinjina irin urajen nata. Ganin dai babu wata na'ura data nuna cutar jikin Zahra kowacce aka ora sai ta nuna babu komai alalmar babu wata cutar amma kuma a zahiri ga shi nan ana gani.Jin bayanin da Doc ya yiwa Daddy sai hankalinsu duka ya tashi musamman ma Mummy da Hauwa'u ita kwa Zahra sunkuyar da kanta a asa sunayen Allah kawai take ambato.Dan Doc yace babu yadda za su yi, su san abin da za su yi wurin orata akan magunguna har sai sun san cutarta kuma gashi na'ura ta i nuna cutar.Dan haka sai dai su yi ha uri su koma gida idan an an shafi kwanaki sannan cutar ta auki kwanaki a jikinta, tunda ance yau ne abin ya fito mata, sai su dawo a gwada ko na'urar zata nuna cutar.Haka suka baro asibitin. Bayan wannan asibitin sai da suka je asibiti ulu amma gaba aya sakamakon guda aya ne wato babu wani abu da ke jikinta bayan gashi nan urajen a jikinta babu masakar tsinke.Haka suka dawo gida sun zo suka iske Ammi a gidan dan Hannatu ta kirata a waya ta fa a mata shine suka taho da Ummar Mashkur dan gaba aya hankulansu a tashe suke. Dawowar su Zahra shi ya ara tayar musu da hankali ganin yadda jikinta ya koma ga kuma urajen da mugun tauri da zafi ga suna saka mata zafin jiki, haka suka sha kukan tausayin Zahran babu mai lallashin wani.Babban tashin hankalin ma guda aya shine da akace babu abin da aka gani a asibiti.Mummy ta jajanta musu daga arshe suka musu sallama suka tafi gida ita da Daddy sun ce shi Mubarak bai da lafiya. Su Ammin sun jinjina musu tare da musu godiya ganin irin awainiyar kaita asibiti da suka yi ko neman Ammin ba su yi ba, amma Mummy ta nuna musu babu godiya tsakanin su ai itama arta ce kuma jinya tana kan kowa.Su Ammi dama basu sa ran ganin Mubarak ba dan ba kowane namiji bane zai iya zuwa kusa da matarsa idan tana cikin wannan halin ba. Ammi ce ta samu ruwa ta karanta addu'o in tsari tare da na waraka a ciki tace Zahra taje ta yi wanka da ruwan dan gaba aya sun tsorata da yanayin duk da sun fawwalawa Allah komai kuma sun yarda Allah ne ya ora mata amma kana ganin yanayin abin kasan akwai sihiri. *Mubarak* Wajen arfe biyar ya ara fesa wankansa ya sha kwalliya abinsa sai amshi yake, key in mota ya auka da wayarsa, yana ganin missed call in Nazeer amma ya i kiransa saboda ba ya so ya katse masa hanzari.Ko inda part in Zahra yake bai kalla ba ya wuce abinsa ya shiga motarsa mai gadi ya wangale masa get ya kama hanyar Hotel in da su kayi za su ha u shi da Zee-zee SANADIN KISHIYA NE NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS ERITER'S ASSO... PAGE 3 A harabar Hotel in ya samu Zee-zee na jiran zuwansa, sanye take da wasu kaya da suka kama jikinta, tun da ta ga Mubarak duk ta saki jiki tana wani narke masa Shima sai zumu in ganinta yake an jima ba a ha u ba. aki ya kama musu inda suka shiga she e ayarsu wa'iyazu billah, ba su suka tashi baro Hotel in ba sai arfe tara na dare, ta shiga motarta ta tafi shima ya shiga tashi motar ya nufi gida ban dan ransu ya so ba suka rabu dan in san samu ne su kwana tare. Horn yayi mai gadi ya bu e masa get ya shigo yayi parking, door bell ya shiga dannawa yana jiran azo a bu e masa,Zahra tana jin aran door bell in ta san shine saboda taji sanda ya tashi motarsa kuma ko lokacin da mai gadi ya mi o sa o a ajiyewa Mubarak in mai gadin ya tabbatar mata tun yamma ya fita.Wani ululun acin rai ne ya tsaya mata a ma oshi ta san dai ba wani wurin abin arzi i ya tafi ba kawai saboda ta tsinci kan ta cikin addara hakan ya nuna bata da wani amfani a wurinsa ita ba ma wannan ne damuwarta ba damuwarta ace shine mijinta kuma wataran zai zama uban anta amma kwata-kwata cikin halayensa babu na auka. Ajiyar zuciya ta sauke ta juya ta kalli Hauwa'u da ke linke kaya tace mata taje ta bu e masa ofar, dan su Ammi da zasu tafi tace Hauwa'u ta zauna tun da sunyi hutun makaranta sai take an taimaka mata, kuma Mummy Mubarak in ma ta dawo da magriba ta duba jikinta nata duk da yanayin jikin nata da sau i dan tun da tayi wanka da ruwan addu,ar da Ammi ta mata sai taji sau in ra in da urajen ke mata sannan zafin jikin nata ma ya an ragu sai dan abin da ke zuba daga jikinta ne dai bai daina zuba ba kuma bai ragu ba. Hauwa'u sai da ta tura baki gaba sannan ta tafi bu e masa ofar dan bala,'in haushin sa take ji yadda yayi biris ya nuna halin ko in kula da yayarta, dan ko lokacin da Mummynsa ta zo tana tambayrsa saboda ta ga part insa a rufe cewa Hauwa'un tayi ya fita masallaci ita kwa Zahra shiru tayi dan bata son aryata ar uwarta tun da bata san dalilinta na yin hakan ba. Tana bu e masa ofar ya shigo yake binta da kallo Hauwa'u kwa ta ha e rai suke kallon -kallo, ta e baki yayi ya ra a ta gefenta ya wuce, rufe ofar tayi itama ta ta e nata bakin tana ara jin haushin sa dan ita ko magana bata masa ba bare ta gaishe da shi tana kallonsa ko inda part in yayarta yake bai kalla ba ya wuce part insa wafa tayi ta koma part in Zahra cike da takaicinsa. Mubarak kwa jinsa yake a sama sai wani annashuwa yake yana jin ba ya shi, a'uzubillahi mutumin da yayi zina amma yake jin farinciki a ransa babu jin ba inciki da takaici da kuma nadama da ya aikata sa on Allah.Zaunawa yayi akan kujera ya jingina bayansa tare da rufe idanunsa yana jin da i sosai a cikin ransa babban abin