Sashe 49
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ke sashi nisha i yadda ya ara samun kansa a matsayin namiji dan da har ya yanke cewar matu ar suka ha u da Zee-zee bai ta uka komai ba a matsayinsa na namiji to dole zai sanar da Mummy halin da ya tsinci kansa ayi saurin aukan mataki.Amma abin mamaki sai gashi bai tsinci kansa a halin da ya tsinci kansa ba da suka kasance da Zahra hakan ya tabbatar masa da cewa Zahra ce tayi wani abin dan kar ya kusanceta saboda bata son sa. Wani haushinta yaji a ransa ya doka wani uban tsaki, kafin ya tashi domin yin wanka. aure da towel ya shiga bayin sai kuma ya shiga she awa kansa ruwa kamar yadda ya saba yin wankan tsarkinsa idan ya dawo daga yawon she e ayarsa.Sai bayan ya gama jagwalgwalawa sai kuma tunanin Mummyn sa ya fa o masa da ta koya masa wankan tsarkin dama can takan zauna ta tarki koya masa ita a tunaninta matsayinsa na musulmi baligi dole ya iya wankan tsarki ko dan mafarki ma dn ita bata kawo cewa yana neman mata, amma baya saurarenta saboda sangarta. Alwala ya sake ai wato maimakon alwalar sallah da ake wanke ga i sau uku-uku na wanka kuma sau ai - ai haka yayi kamar yadda Mummyn ta koya masa.Ruwan ya ako ya shiga wanke kansa zuwa fuskarsa har sai da yayi hakan sau uku, sannan ya wanke arin jikinsa na dama sau aya sannan sai ya wanke na hagu shima sau aya sai kuma ya ha e jikinsa gaba aya da ruwan yana mai cuccu a ko ina. Da har zai fita yayi sallan a hakan kamar yadda Mummyn tace masa idan mutum yayi wankan tsarki yana iya yin sallah a haka indai a lokacin ne ba tare da ya sake alwala ba alwalar da mutum yayi a farkon wankan ta wadatar.Amma kawai sai yaji a ransa gwara dai yayi alwalarsa hakan yayi alwalar ya fito ya shirya ya gabatar da sallah.Dama sun ci abincinsu shi da Zee-zee acan Hotel in dan haka baya bu atar wani abinci, dan dama so yake zuwa gobe a kawo masa kuku daga gidansu domin yake masa abinci, dan baya jin ko da abinci daga part in Zahra ya fito, ba ita ta girka ba zai iya ci ba saboda yaminta da yake ji. Zahra haka suka kwana basu rintsa ba saboda cikin dare sai urajen suka shiga mata zugi da sukarta, addu'a suka shiga yi ita da Hauwa'u dan tsabar tausayin Zahra da Hauwa'u hawayen tausayin ar uwarta ne kawai ke kwaranyar mata sai Zahran ce ta shiga lallashinta tare da nuna mata cewa ba komai bane jarabawa ce ita ko fatan ta Allah bata ikon cin jarabawarta ta.Hakan yasa ita ma Hauwa'u daurewa suka dinga addu'a har asuba haka suka kwana basu rintsa ba. _BAYAN SATI GUDA_ Mubarak da Zee-zee sosai sai abubuwan da suka yi gaba dan yanzu burinsu bai wuce su mallaki kansu ba a matsayin ma'aurata dan gaba aya Mubarak in haukacewa yayi akanta.Baya ma batun Zahra dan tun washe garin kawota har yau bai ara sanyata a idanunaa ba, dan bai ara kallon ko da hanyar part inta ba bare kuma har yayi sha'awar shigar.Ko Mummy idan ta zo dubata in ta tambaya yana shigowa sukan ce mata eh dan Ammi ta garga esu akan su guji fa awa mahaifiyrsa cewa ga abin da yake mata dan bata so su shiga tsakanin uwa da Zahra kwa bata damu da halin ko in kula da yake nuna mata ba, idan ya fice yawonsa sai lokacin da ya ga dama yake dawowa.Bare yanzu an kawo kuku da ke yin girki da kuma mata guda biyu matashiyar budurwa da kuma wata dattijuwa saboda aikin gida. A ranar alhamis ne misalin takwas da rabi na dare Mubarak ya shirya tsaf domin zuwa gidansu domin gabatarwa da Daddynsa maganar son arin aurensa shi da Zee-zee saboda ta nuna masa acin ranta da kuma cewa matsawar ba zai gabatar da maganar aurensu ba a gaban iyayensa.Shima dama yana son hakan dan ko da ya tuntu i abokinsa Nazeer shima cewa yayi ya ma fi son ya auri Zee-zee wayayya kuma ta san komai yadda za ta tafikar da shi, kuma su ma har sa ke zuwa gidansa a matsayinsu na abokansa amma wannan yarinyar da aka kawo ga ance ta zama aljana shi yasa basa son zuwa gidansa. A part i Daddy ya same su har Mummy bayan ya gaishe su suka shiga tambayarsa jikin matar tasa, ya amsa musu da sau i sosai.Bayan sun an ta a hira sai kuma ya shiga gabatar da abin da ke tafe dashi.Mamaki ne ya hana Mummy magana yaron da sati guda kenan da tarewarsa da matarsa amma yanzu zai zo da batun arin aure. "Ita yarinyar ar gidan waye?"Mummg ta tsinci muryar Daddy na tambayar Mubarak dama ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Kallonsu kawai take Mubarak in na yiwa Daddy bayanin shi kuma Daddy na gya a kai alamar gamsuwa. "Insha Allah jibi zan je nema maka aurenta"Daddy ya fa a cikin farinciki. "Wai lafiyarka kwa Daddyn Mubarak!?Ya za ayi ace yaron da sati guda kenan da tarewarsa ace za a nema masa wani auren" "Dakata! Shin me kikeso in yi ne?Yaron ya zo min da maganar airen sunna kina maganar satinsa da tarewa, shin so kike ya fa a a halaka bakya ganin yadda ita matar tasa ta gidan ke auke da larura a hakan da take ma yake zaune da ita inaga ai yayi jihadi"Cewar Daddy yana kafe Mummy da ido kamar zai kai mata duka. "Ni bance ba kuma ba haka nake nufi ba amma mutane zasu zagemu ake ganin dan yarinya ta ha u da larura an mata kishiya kuma iyayenta ma ba za su ji... "Ya isheki, ke kike lissafin mutane ni babi ruwana da mutane zan yiwa ana duk abin da yake so bare aure sunnar ma'aiki S.A.W kuma ma tun da dai sakinta akayi ba sunna ce kawai za a abba a"Daddy ya katse mata hanzari. "Shikenan"Mummy tace tare da tashi ta bar falon. Haka suka shiga tattaunawa kafin daga bisani Mubarak in ya yiwa Daddy sallama ya bar gidan.Yana dawowa ya kira Zee-zee ya fa a mata abin da Daddy yace.Tayi murna sosai akan labarin nan mai da i da Mubarak ya sanar mata na batun zuwa neman aurenta ranar sun sha murna ita da Aunty sosai suna ganin aikin Malam yayi daga arshe ta kira Neesa ta bata labari sosai tasha mata kirari wai matar Mubarak. Bayan kwana biyu su Daddy suka je neman auren Zee-zee aka yanke rana sati aya domin angon yace yana son komai a kusa ne.Babu wanda ya sanar da Zahra halin da ake ciki dama Mummy ita kwa nauyinsu take ji daga ita har Ammin ta yaya za ta tunkareta da maganar wannan bayan tana ganin halin da yarinyar take ciki.Kuma ita ma Ammin kanaganinta kasan tana cikin damuwa dan duk bayan kwana biyu sai ta zo gidan ta duba jikin Zahran wani lokaci kuma su zo ita da Ummar Mashkur, shi dama Baffa Abdullahi ba a maganarsa dan zuwansa aya shi da matarsa suna can sun tare a sabon gida suna cin duniyarsu da tsinke arzi i gashin hanci MAMAN AFRAH SANADIN KISHIYA NE NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS ERITER'S ASSO... PAGE 3 An sha shagalin biki sosai aka kashe ku i iya ku i, ku i da ya amsa suna ku i ba muna ku i ba, sati guda aka kwashe ana bidirin bikin Zee-zee da Mubarak.Zahra kwa ko da Ammi da Ummar Mashkur suka sameta da maganar arin auren Mubarak in ba ta wani damu ba duk da sun mata nasiha tare da nuna mata cewa, ta yarda da hakan rubutacciyar addararta ce.Itama Ammin Mummy ce taje takanas har gida ta sanar da ita dan bata son su samu labarin a gari gwara dai koma menene ace an fa a musu domin hakan kulawa ce. Ammin ta nunawa Mummy babu komai kuma zata samu Zahra da maganar ita da take ta kanta babu wani abu, haka Ammi ta yiwa bikin ftn alkairi tare da addu'ar samun zaman lafiya mai orewa.Sosai Mummy taji da in yadda Ammin ta nuna mata duk ta san da ciwo ace za a yiwa arka kishiya bare ma ar da ita ma ba wani da ewa aka yi da yin aurenta ba, ga kuma lalura da ta ha u da ita. Bayan tattaunawar da Mummyn da Ammin su ka yi sai kuma Mummyn ta fito da takardun gida da makullai, ta baiwa Ammi wannan kyauta ce daga gareta, sosai Ammi ta nuna mata jin da inta da kuma mata godiya da mata addu'a ta dacewa mai tarin yawa, Mummy taji da i sosai ganin ta farantawa Ammi, haka ta tafi bayan ta fa a mata in suka shirya zuwa ganin gidan kafin su tashi tarewa za ta sa direba yazo ya kai su. Bayan tafiyar Mummy Ammi ta ajiye takardun gidan da makullan a gefe ta shiga jimamin labarin da Mummyn tazo da shi sosai ta shiga rudani fisabilllahi daga yin aure ace har an yiwa Zahra kishiya ina ma lafiya bare kuma wayo na zama da kishiya, wallar tausayin artata ne ya shiga zubo mata tasa hannu ta goge tana sawa a ranta cewa su Allah suka ri a da kuma addu'a tabbas kwa tasan ba zasu ta a ta ewa ba. Amarya Zee-zee an tare a gidan Mubarak amma abin da ya bata haushi yadda duk kyau da tsaruwar gidan amma ace akwai wata a ciki, watan ma azamar yarinya marar galihu yarinyar da ta sanya hannu ta mari fuskarta da sannu za ta nuna mata shayi ruwa ne.Tun a ranar da ta tare ta ke jin kanta ita wata ce, part inta yana a can ciki ne sai ma an wuce na Mubarak sannan nata.Abin da ke faranta mata bai wuce irin zarrar da kayan akinta ya yiwa na Zahra da kuma lefenta da irin dukiyar da aka narkar a bikinta sai kuma uwa uba da Mubarak ya zamana mallakinta ita ka ai dan ba za a ma sanya Zahra a layin matarsa ba, tun da ko