Sashe 21
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Mmn Afrah* PAGE 1 Sosai Daddy ya yiwa Mummyn Mubarak fa a akan rashin zuwanta duba Mubarak in asibiti yana ganin hakan ba aramin nuna rashin damuwa bane da kuma rashin kulawa.Ita dai tunda ya fara fa an bata tanka asa domin Mummyn mace ce mai matu ar biyayya da kuma kawar da kai.Dan ita duk fa an nashi ma bai ta a mata zuciya ba halin irin rayuwar da ya jefa mata anta yafi damunta amma ta auki hakan a matsayin addara tana kuma addu,a da fatan samun sauyin rayuwar anta. Bayan fitarsa daga sashen nata ,sashen Mubarak in ta nufa ta sameshi shi da Nazeer duk ransu a ace bata dai san me suke tattaunawa ba.Ganinta yasa Nazeer in duk ya kasa sakin jikinsa ita kuma sai bata nuna masa komai ba domin yanzu ta daina ganin laifin Nazeer in ma tafi baiwa Daddyn Mubarak in laifi dan shine yake basu ku i dan haka yanzu daga Mubarak in har Nazeer in duk rayuwarsu abin tausayi ce .Saboda ku i ba aramin taka rawa suke ba wurin ata da kuma lalata yara ba tun daga ananan yara da samari dama wasu manya baki aya dan ku i da mace sune ke canja mutum wala zuwa kyakkyawar rayuwa ko akasin haka.Domin ku in nan idan wasu samarin suna dasu sukan rasa yaya zasuyi dasu wasu daga haka suke afkawa shaye-shaye domin suna ganin suna da ku in da zasu sayi kayan maye,kai har ma su siyawa abokanansu ,wasu wannan ne mafarin kuma sanadin fa awarsu zina saboda suna ganin suna da ku in da zasu baiwa matan dama wasu halaye mararsa kayu. Shisa ake cewa tarbiya daga goda take farawa ,kuma iyaye sune ginshi in rayuwar ansu musamman uwa domin uwa itace gaba aya kaso afi yawa na daga tarbiyar a suke a ashinta.Dan haka uwa ce ya kamata tun yaro na arami ya kamata ta dasa tarbiyarsa akan turba me kyau domin icce tun yana anye ake tan wasashi idan ya bushe in aka tarki tan wasashi karyewa zai yi.Duk da wani lokacin idan akwai addarar mutum babu yadda za kayi wani abin addara ce duk iya bada tarbiyarka da tsawatarwarka sai yaron yayi abun wani kuma ba addara bace in ma da addarar to akwai sakaci ko sangarta laifin uwa ko mahaifi wanda za kiga aya yana tufka aya yana warwarewa.Kamar dai Mubarak Mummynsa tana iya arinta amma Daddynsa yana sangartashi ta sanadin haka gashi ya afka wata rayuwa wacce addu,a da ha uri su ka aine zasu kai ga cimma nasara wajen gyara rayuwarsa. Dan haka yanzu Mummyn ta yanke hukuncin daina nuna musu acin ranta daga Mubarak in har Nazeer in.Za ta ke jansu a jiki ta hakane za su ke an sakin jiki da ita har ta fara kaiwa ga nasara duk da ta san abune mai wahala sai dai idan aka fawwalawa Allah komai tare da mi a al,amura garesa abin zai zo da sau i dan babu abinda ya gagari Ubangiji. Sosai ta saki fuska suka an yi hira ta masa sannu sannan ta an bashi uzurinta na rashin zuwa asibitin dan ta ga yana fushi ,ganin tana ta jansu a jiki sannan bata nunawa Nazeer komai ba ko kuma korarsa sai shoma Mubarak in ya saki jiki suka an ta a hira da Mummyn tana nuna masa kulawa tare da musu nasiha akan abinda sukayi na tarar wani da fa a.Tana kuma nuna musu shifa an adam yana da daraja ko da kuwa talaka ne domin da talaka da mai ku i duk Allah ne ya yisu kuma shi ke azurtawa sannan shi ke talautawa,babu wani wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoronsa da kuma kiyaye dokokinsa.Ta an ga sauyi a tattare dasu kuma da alama maganarta ta ya shigesu duk da basu furta hkn ba amma dai akwai alamar fahimta dan dama tasan sai a hankali komai zai tafi har ya gyaru kafin a kai ga cimma nasara a rayuwa! Washe gari da la,asar lis bayan Zahra ta dawo daga scul Ammi ta sanyata ta shirya har Hauwa,u ranar ba islamiya suka nufi gidansu Mashkur domin ara duba jikinsa,saboda yanzu abin ya zama na gida tunda an gidan awarta ne.Ibrahim ne ya musu kwatancen gidan da dama Ammi ta san unguwar.Sun samu Baba ya fita sai Umma da Mashkur in sai wata ma ociyarsu da ta shigo dubashi tare da jajanta abin da ya faru.Sun gaisa cikin aminci da mutunta juna Umma ta ji da i matu a da zuwansu,Zahra sai sunkuyar da kai take ita dole kunyar Umma ta ke ji. "Zahra ki saki jikinki ni Ummanki ce"Umma tace tana janta a jikinta.Sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsunta. "Umma Yaya fa haka take kunya gareta"Hauwa,u ta ce cikin tsokana.Fakar idon Umma Zahra ta yi ta harari Hauwa,u. "Yaya dan kinga bata gani shine kika harareni?" Hauwa,u tace tana mata gwalo. Wata kunya ce ta ara rufe Zahra,ita dai Ammi murmushi kawai take. "Rabu da ita Hauwa ai ina kallonta ta wutsiyar ido"Umma tace tana dariya.Sunkuyar da kai Zahran tayi tana sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta. "Ammi sannu da zuwa ina wuni"Mashkur yace lokacin da ya fito daga akinsa ya tsugunna kansa a asa . "Lafiya kalaw Mashkur,ya jikin naka" "Da sau i sosai Ammi" "To Allah ara afuwa"Ammi tace tana masa kallon tausayi gaba aya ya fita hayyacinsa duk jikinsa tabon dukana sosai ya daku a hannun an sandan nan sai dai ace Allah masa sakayya. "Amin ya Allah"Yace har lokacin kansa a sunkuye dan haka kawai idan ya kalli Zahra sai ya dinga jin fa uwar gaba,gani yake kamar zai rasata jiya kwata-kwata kasa sukuni yayi barci bai ga idanunsa ba yana sa e-sa e akan abinda idanunsa suka gane masa jiya na irin kallon da Mubarak in ke jifan Zahra dashi tabbas idan har son Zahra yake to ya san shi da auren Zahra sai dai wani iko na Allah.Duk ya san Ammi ba zata hanashi auren Zahra ba amma yana tsoron ya rasata tunda mahaifin Mubarak yana aiki da arfin dukiyarsa ya yiwa ansa abin yake so shi kuma talaka ne amma dai haka kawai yake jin wani iri a ransa dan ya san tabbas idan ya rasa Zahra to tabbas rayuwarsa tana cikin matsala domin zuciyarsa ta dale da yin nutso cikin kogin sonta. "Kake kiyayewa Mashkur duk da nasan halinka amma ka daina shiga irin wannan duk da kana da gaskiya amma yanzu ku i sun danne gaskiya ta fannoni da dama.Dan haka komai aka maka ka kauda kai kaga yanzu kalli yadda aka illataka sakayuar sai dai a iyama kuma duk akan gaskiyarka"Ammi ta ce cikin tausaya masa. "Insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba wannan ma tsautsayi ne" "Allah kiyaye gaba ya baka lfy" "Amin "Yace cikin sanyin murya ,ya tashi daga wurin yana tsokanar Hauwa,u da take masa sannu tana ta jimanta abinda aka masa dan ya daku sosai. Bayan shigarshi akinsa sai Umma ta ce da Zahra ta tashi ta je ta masa sannu, domin akwai maganar da Umma take so su tattauna.Jim Zahra ta yi tana an jin nauyi har sai da Ammi ta sake maimaita mata sannan ta bi bayan Hauwa,u da har ta kai ofar akin.Da sallama suka shiga akin amsa musu yayi suka aga labulen suka shiga,zaune yake a bakin katifarsa ya kifa kansa akan gwiwa.Har suka samu wuri akan kujuru na plastic suka zauna,amma bai ago ba. "Umm Yaya ni bari inji gidansu awata ar islamiyarmu bayan nan layin ne naga Yaya Mashkur in kunyata yake ji"Hauwa ,u tace cikin tsokana kafin Zahran ta bata amsa ta fice daga akin.Tana fitowa ta tambayi Ammi aikuwa bata hanata ba Umma ma tasan gidan har tace ta gaishe da matar gidan da to ta amsa tasa kai ta fice abunta. A can cikin akin kwa Zahra tun tana ari- ari dan wannan shine karo na farko da ta shiga akin wani a namiji.Wannan ma tasan Ammi ta kyaleta kasancewar akin a cikin gidan yake kuma ma inda su Ammi suke zaune kusa da akin ne. Shirun da ta ji yayi yawa ne kuma har lokacin Mahskur bai ago kansa ba.Kallon yanayinsa take tana ta sake -sake a ranta dan ko jiya da ya kirata a waya da daddare data auka shiru yayi tayi ta magana amma shi babu abinda yake cewa haka ku insa yake ta tafiya.Idan ta gaji ta kashe sai ya ara kira haka yayi tayi har dai da ya gaji ya daina kiran.Da safe ma kafin ta tafi scul ta kirashi ta masa sannu amma daga amsa gaisuwarta da kuma tambayar jikinsa da tayi tun daga haka bai sake cewa komai ba,haka ta gaji da magana ta katse.A scul ma ta kasa sukuni sai da ta sake kiransa amma hkn bai canja ba.Duk da a ranta tana tunanin hkn baya rasa nasaba da cewar da wannan wanda ta ji ana kira da suna Mashkur a police station yace saboda ita ya janye case in tana tunanin wannan ne dalilin daya sanya Mashkur in yin fushi. "Ya sau in jikin?" Ta ce cikin sanyin murya.Shiru yayi bai amsa ba bai kuma ago ba. "Ya Mashkur dan Allah kace wani abu wallahi bama jin da in yadda kake min daga jiya zuwa yau" A hankali ya ago da kansa ,dan shima ba a son ransa yake mata abinda yake matan ba,dan ko jiya da yake jin muryarta a waya kawai hawaye ne suke kwaranya a idanunsa.Duk lokacin da yaji muryarta ta daki dodon kunnensa sai ya ji wani bala,in son ta ara ninkuwa a zuciyarsa a gefe aya kuma yana hango wani abu da ba kowa zai fahimta ba,dan tunda ya ga kallon da Mubarak ya mata har ya sanya hannu ya mari wata wacce da alama budurwarsa ce ya mareta saboda Zahra tabbas tun daga lokacin ya fara tunanin akwai lauje cikin na A razane ta kalleshi ganin hawaye akan kyakkyar fuskar masoyinta, tabbas koma menene wannan abu ne mai girma wanda ita ta kasa fahimtar hakan dan ba aramin abu bane zai sanya Mashkur in damuwa har da zubar hawaye. "Ya salam, me kuma ya faru?"Ta fa a itama nata idanun na ciccikowa da walla. " Zahra