← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 62

Sashe 51

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

afafunta ta sakko asa ta tafi makunnar fitilar akin ta kunna, har aran makunnar fitilar ta ji alamar kunnuwar fitilar amma cikin iko da hikimar ubangiji ba ta ga haske ba.Mamaki ne ya cika mata zuciya dan ta san dai ko da ace babu fitila dole dai za ta ga an alamun haske ko wanda ya ratso ta window ne dan lokacin tana jiyo karatun sallah a nasallatai kennan ko hasken alfijir ta an gani,amma dilim take gani babu wani abu da take gani. A hankali ta kai hannayenta ta ta o idanun nata amma abin mamaki a bu e suke amma bata gani, cikin fa uwar gaba ta shiga murza idanun amma babu wani abu da ya canja daga ganin nata. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya rabb taimakon ka nake nema ka dafa mini cikin ni'imarka ka min jagora a al'amurana.Ya Allah kar ka ora min abin da ba zan iya ba duk da na san baka orawa rai face abin da zata iya, ubangiji kanji anci lamurana kasa ba idanuna na rasa ba"Cikin zuciyarta take karanto addu'ar. A hankali ta juya daga wurin makunnar fitilar ta laluma ta koma wajen gadon, jin ta araso yasa ta juya domin ta zauna aikuwa ashe bata kai kan gadon ba ji kake tim!Ta fa i a asa mazaunanta dake cike da urajen nan masu zafi da ra i, ya bugu a kan tiles a take taji wani mugun ra i ya ziyarceta, shiru ta an yi tana jin saukar ruwan hawayenta a kumatun ta, godiya ta yiwa ubangiji domin shi dama bawa anaso a kowane hali ya tsinci kansa ya godewa Allah. Mazaunanta ta mi a za ta zauna a bakin gadon amma ashe bata gama arasawa kan gadon ba dan haka sai jinta tayi tim ta fa i a asan tiles, wani zafi da ra urajen da suka mata awanya a mazaunata ne ya ziyarceta nan take! Wani hawayen ne ya cigaba da waranyo mata tabbas idan bawa bai mutu ba to lallai ba a gama masa halitta ba, kuma ba a gama jarabtarsa ba.Cikin arfin hali ta ara mi ewa tsaye sai da taji ta dafa gadon sannan ta zauna a kai. Hannu ta kai kan Hauwa'u da ke ta minshari tana baccinta hankali kwance, bata san meke wakana ba ta shiga bubbugata tana kiran sunanta da yake Hauwa'u akwai nauyin bacci sai data mata tashi hu u sannan ta tashi.Idanunta ta shiga murzawa tana yatina fuska irin a wanda bai ji a da tashi daga bacci ba. "Ya Zahra har arfe aya da rabin tayi?Gaskiya yau daman mun bari sai arfe uku muyi nafilar nan wallahi bacci ne a idanuna sosai"Ta ce tana kallon ar uwarta ta. "Wa yace miki tsakiyar dare ne yanzu ai har an fito daga masallacin asuba ma"Zahran ta fa a tana sauraron arwarta ta. "Ikon Allah lallai yau nasha bacci, kice har kinyi taki sallar dan nasan ba zaki kai yanzu baki yi sallah ba, matar da sai tayi raka'a tainil fajr sannan ta dinga azkar har sai an shiga sallah sannan ta gabatar da sallar farillah"Hauwa'u tace cikin zolaya Shiru Zahra tayi tana jin zuciyarta na neman karyewa so take ta sanar da ar uwarta halin data ara samun kan ta a ciki a yau, amma bata so hankalin Hauwa'u ya tashi tafi so ta sanar da ita cikin hikima. "Nima ban yi sallar ba"Ta fa a cikin sanyin murya tana jin kamar idan Hauwa'u ta tambayeta rashin yin sallarta ta da wuri kuka zai wace mata. "Ikon Allah yau in kuma jar da su kaza a cin dan o,ki ce yau makarar bani ka ai ba amma garin yaya hakan ta faru?"Ta ce cikin tsokana tana so taga murmushin Yayarta ta ganin tun da ta tashi sai tsokanarta take amma bata murmusa ba. "Hauwa'u bana ganinki!!!" Shine abin da kawai ya iya fitowa daga bakin Zahra. "Kamar ya ?Yau kema kin zama ni kenan tsokana za kiyi gwara dai mu fara sallar tukunna"Hauwa'u tace ta arin sakkowa daga gadon tana dariya. Hannh Zahra ta mi a ta ri o doguwar rigar baccin da ke jikin Hauwa'u, waiwayowa Hauwa'un tayi cikin mamaki dan ta san dai Zahra ta tsani taga ana wasa da lokacin sallah, amma kuma gashi yau tana neman tayi wasa da lokacin sallah da kan ta. anwata bana ganinki fa ki yarda dani, babu abin da nake gani sai tsananin duhu"Zahran tace zuciyarta na karyewa hawaye na saurin sakkowa kamar jira suke. Da farko Hauwa'u tayi zaton ko wasa ne Zahran keyi amma ganin hawaye ya tabbatar mata da gaske Yayarta ta take, cikin muguwar razana Hauwa'u ta kamo kafa un Zahra tare da jijjiga Zahran da arfi tace "Ya Zahra kika ce bakya gani na!!!? Dan Allah da gaske kike dan Allah duhu kike gani ko haske ?Ki bani amsa amma banaso ki ce duhu kike gani"Hauwa'u take fa a da arfi tana kuka wiwi jin wata addarar ta dirarwa Yayarta ta bayan bata gama fita daga wata ba bare kuma rashin ido ai mutuwar tsaye ce makanta da yarintar ta da komai. "Ya Allah ka dubi maraicinmu ka fitar da baiwar nan taka daga halin da take ciki, ya Allah kai ke ora cuta kuma kai ke warkarwa ya rabbi ka warkar min da Yayata daga dukkan ciwukan nan da ta tsinci kan ta a ciki"Hauwa'u ta sake fa a tana ame Zahra ganin Zahran ta kasa magana sai kuka take mai cin rai da shiga zuciyar mai sauraro.Lallai Allah gagara misali ga dai idanun a bu e suna iftawa amma kuma babu abin da suke gani! MMm afrah SANADIN KISHIYA NE NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE3 ```Mashkur``` Rayuwa tayi kyau sosai domin kawunsa ya bashi jari mai tsoka tare da nuna masa kasuwanci, yanzu ba ma ya samun lokacin kansa kullum idan ya fita tun safe sai ko gabanin magrib yake dawowa.Dan haka yanzu bai fiya yawan tunane -tunane ba dan gaba aya hankalinsa yana kan kasuwanci, dama yawancin damuwa tana samun gurbine a zukatan mutane da zarar mutum ya ka aice amma idan kana tare da mutane ko kuma kana yin wasu abubuwan to ita kanta damuwarka za tayi sau Idan ba dare bane yayi in yazo kwanciya tunanin Zahra ke son addabar zuciyarsa, yana arin yakicewa amma saboda zuciya wani abun ko bakaso sai kayi.Yanzu ya sake layikan waya har ma da wayar yana waya da su Umma amma bai ta a tambayar labarin Zahra ba ita ma kuma Umma ko da wasa bata ta a yin urin sanar dashi halin da ake ciki ba duk da cewa shi a nashi angaren zuciyarsa na azalzalarsa akan yana son ya san halin da Zahran ke ciki amma yana tursasa zuciyarsa akan mantar da tambayar domin yanzu ya san ta zama mallakin wani kuma ma baya so yaji labarin Zahran na cikin damuwa.Sai dai ya san ko da ya san hakan babu wani abu da zai iya yi. _Zahra_ Ta fawwalawa Allah damuwarta yanzu bata wani sanya komai a ranta domin kuwa ta yarda a ranta cewa haka Allah yake son ya ganta, sai dai suna dagewa da addu'a daga ita har Ammi da Hauwa'u akan idan da rabon ta sake gani watarana Allah zai bata lafiya idan kuma bata warke ba to dama haka Ubangiji ya addara. Duk da yanzu cikin iko da hikimar ubangiji abin da ke zuba a jikinta ya auke, tun yana zuba ka an -ka an har dai ya dawo sai ayi kwana biyu uku ma bai zuba ba.Hakan kuma ya faru ne ta dalilin tsayuwa tsayin daka da addu'a da suka yi. *Mummy* Ta shiga tashin hankali da jin makantar da ta samu Zahra, hakan ya sa, ta tausaya mata sosai dan haka a kullum sai taje dubata sau biyu.Sai dai babban tashin hankalinta bai wuce yadda Daddy ya takura akan cewa sai Mubarak ya sawwa ewa Zahra, dan tun da ta makance yake cewa yarinyar mai farar afa ce dan haka baya so masifu su zo su afkawa ansa ta sanadinta dan ya ga abin ya dara wuce maka i da rawa.Amma Mummy ta yi fito ana fito da Daddy ta nuna masa matsanancin acin ranta akan hakan dan a ganinta hakan rashin adalci ne kuma ma zalinci ne ace saboda larura ta sameta ace an saketa, duk da Mubarak in ba wani shiga shirginta yake ba dan ko da aka ce masa ta ara samun wata larurar ta makanta cewa yayi babu ruwansa da er ma Mummy ta sanyashi a gaba yaje ya dubata dan shi tun ranar da ya baro part inta bai ara komawa ba bama ya tunota mantawa yake da ita. _Zee-zee_ Rayuwa ta samu duniya sabuwa ga burinta ya cika na makantar Zahra ga kuma ciki da take auke dashi Mubarak sai ji da ita yake yana ririta ta kamar ya ha iyeta dan murna yana bala'in son cikin jikinta dan shi fatanshi ta haifa masa an biyu.Yanzu bata da wata damuwa duk da damuwarta aya shine idan Mubarak ya fita zuwa wani wurin sai zuciyarta ta ringa mata sa a da kuma zargin ko yana can tare da wata suna aikata masha'a wannan abin ke damunta amma in bayanshi bata da wata damuwa ku i ne gasu nan Daddy kullum kamar bai san ciwonsu hakan zai ta auka yana hanka a musu acc. _Baffa Abdullahi_ Tun da Zahra ta fara jinya da suka je sau aya suka dubata bai ara bi takansu ba, dama yana zaton idan Zahra tana gidan zai ke samun ku e tun da tana auren mai ku i amma ganin mijin ma baya tata ga kuma ma ta makance ko ina sai da sanda hakan yasa yace dama ku i ne ya farfa o da zumuncin yanzu ko tunda babu ku i to dole zumunci ya nemi gado ya kwanta yayi bacci.Hakan yasa ya auke afarsa daga shiga harkarsu su ma kuma basa ta tashi tun da ma can sun saba da rashin sa a cikin rayuwarsu.Ko gidan da aka baiwa Ammi bai san dashi ba iyakarta idan ya ji aljihunsa babu ku i yaje wurin Daddy ya lan wasar da kai da murya a bashi masu gidan rana ya kama
Chapter 51 · 0% Book details