← Book details Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 62

Sashe 53

Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi a cikin tashin hankali jin cewar an saki Zahransa abin da ya ata masa rai ma shi ne auren ko shekara uku bai yi ba amma aka saketa, shi da yake da burin idan ya aureta sai ko mutuwa ce za ta raba su amma yanzu ga wani banza can ya ci moriyar ganga ya yada korenta. Lokacin yana busy dan haka bai samu damar zuwa Zariyar ba, domin yanzu kasuwa ta cigaba sai albarka ke aruwa dan shi yanzu ma ba ya jin ko aikin gwabnati ya samu zai yi saboda sabo da kasuwanci.Tun da aka fa a masa an saki Zahra yake jin abubuwa guda biyu abu na farko haushin sakin da aka mata abu na biyu kuma wani abu mai kamar farinciki dan tun sanda Umma ta sanar masa ya ji duk wani nauyi da ya da e a zuciyarsa ya sauka, yana jin kamar ya zama tsuntsu yaje ya ga Zahra, domin itace ka ai a zuciyarsa dan ko a Kano ya ha u da an mata da yawa wandansu da kan su suke cewa suna son sa ya aure su amma wani abi sai dai yayi murmushi kawai dan baya jin akwai wata mace da zai iya bata gurbi a a cikin zuciyrshi.Tashin hankalinsa aya jin larurorin dake tare da ita. Amma kuma wani abin mamakin Umma tun tana sa ran ganinshi har dai ta cire rai abin ya aure mata kai sai dai babi yadda za tayi ne, har dai ta fara tunanin ko dai dan Zahran ta ta a aure ne amma kuma a iya saninta Mashkur ba zai fasa son Zahra ba dan kawai ta ta a aure tun da dama ko bayan auren Zahran ta san har yau bai daina aunar Zahra ba rashinta ne ma yake hanashi zuwa garin. Bata tunanin wata mace za ta auke masa hankali aka soyayayar Zahra duk da an adam na canjawa ako yaushe kuma a kowane lokaci, musammman ma da ake cewa ku i da kuma mace na canja namiji a kowane lokacin amma dai tana yiwa Mashkur in kyakkyawan zato akan soyayyar da yake yiwa Zahra. Ko Zariyar ma ba ya maganar zuwa ko gida ma da ya siyawa su Ummar Ibrahim kawai ya aikowa ku in aka siya musu har suka tare a gidan amma bai zo ba itama kuma Ummar ko da sun yi magana a waya bata sake masa magana akan Zahra ba ta barshi ne ta ga iya gudun ruwansa duk da bata san dalilinsa ba kuma bata so ta sani, amma ita a tunaninta a ranar da ta fa a masa zai iya yiwa Zariya tsinkaye a washe garin ranar in ma bai shigo a ranar ba. Wasa - wasa sai da aka kwashe watanni uku amma babu Mashkur babu labarinsa babu alamar zuwansa garin Zariya. Zahra ma tun da aka saketa take sanya ran zuwa Mashkur garin ko dan ya zo ya dubata dan ta san dai Umma ba za ta kasa sanar masa halin da take ciki, duk da ta san ba lallai ne ya zo dubata ba sanda tana gidan aure akwai kuma igiyar wani akanta amma kuma yanzu ai bata da aure.Kullum kunnuwanta a bu e suke hankalinta akan ofa tana sauraren da wanda zai shigo gidan domin har kullum cike take da begen jin muryar Mashkur in tun da ta san yanzu dai bata da idon ganinsa. Amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, tun tana sauraron ringtone in wayarta in an kirata ko za ta ji ance Mashkur ne tun da ita ba gani take ba amma sai dai ta ji shiru babu kira ko da a waya ne.Hatta Ammi ta san Zahran na cikin damuwa duk da bata fa a mata damuwarta ba amma ta san tabbas akwai lauje cikin na i, kuma itama Ammi a nata angaren tana mamakin rashin zuwan Mashkur in duba Zahra ko da ace ya canja she a ma'ana ya samu wata wacce ya canja ra'ayi ta auka zai zo ya duba Zahra ko dan zumuncin su da mahifiyarsa amma shiru. Zahra ita har ta dangana da zuwansa ta sanyawa ranta ha uri da dangana dama Mashkur ne take sanya rai akan sa cewa duk runtsi duk wuya ba zai ta a rabuwa da ita ba, duk lalurar da ta sameya zai iya zama da ita ashe dai ba haja bane tun da gashi wata uku da sakinta amma bai ma tuna inda take ba bare ma ya tako ya zo inda take.Hakan yasa ta cire rai da wata aba soyayya bare auna dan dama yawanci mutane suna son mutum ne saboda wasu abubuwan zarar ya rasa abubuwan to su kwa sun daina marmari son sa bare har su auna ce shi hakan yasa ta sanya a ranta cewa tun da ta samu lalurar uraje da makanta to dole ta sanya a ranta cewa babu wani da zai auna ce ta musamman da Mashkur ya manta da ita haka ta ringa baiwa ranta da zuciyarta ha uri akan hakan. Allah sarki kowa yana da udurinsa hakan yasa ake so kar ka yankewa mutum hukunci ba tare da ka ji ta bakinsa ba, yin hakan zai sa ka munanawa wani zato akan kuma yana da kyakkyawan uduri a zuciyarsa domin Allah ka ai ya san abin da ke cikin zukatan mutane! A ranar da Zahra ta cika wata uku da kwana aya ana washe garin gama idar ta, da misalin arfe biyar da rabi na yamma, yammaci ne mai cike da tarin ni'ima babu zafi sannan babu sanyi sai dai yanayin ya dace da yadda kowa zai ji hakan ya masa da i.Dan dama ace zafi yayi yawa ko ana sanyi mai shiga ga i shine za ka ga an samu banbancin ra'ayi na yanayin wani yace zafi, yafi wani kuma yace sanyi ya fiye masa. La'asar ce sakaliyya tafe yake a cikin motarsa da bai da e da siyanta ba, a hankali yake tu i sai dai jin ransa yake kamar ana sanya masa ara saboda wani sanyi da ke ratsa ran nasa da kuma tarin farincikin da ke cikin zuciyarsa.Ga kuma karatun qur'anin da yake suararo daga sudais shi ne ke ara sanyaya zuciyarsa yana kuma sanya mishi nutsuwa. A dai -dai ofar gidan ya tsaida motar a hankali ya ago kansa tare da sauke akan gidan kallon gidan yake tamkar a yai ne ya fara ganin gidan, rabon da ya biyo layin nan ma tun ranar da zai koma garin Kano da zama, tun daga wannan ranar ko da wasa bai yarda ya biyo layin ba amma a yau sai gashi bayan lokaci mai tsawo ya dawo ba ma layin ka ai ba har gidan zai shiga ji yake kamar a wancan lokacin da yake tsaka da zuwa gidan a kowacce rana domin yin tozali da kyakkyawa kuma tauraruwar zuciyarsa. Cikin natsuwa ga bu ofar ya fito, sanye yake cikin dark blue in shadda inkin tazarce babu hula a kansa dai dai gashin kansa da yake kwance luf a kan nasa domin bai kasance mai tara gashi ba, sai sajen fuskar da ta matukar yiwa kyakkywar fuskarsa awanya ga girarsa mai yalwa da ba i da gashin idanunsa masu tsawo, sai sajensa wanda ya zagaye har bakinsa sai dai babu gemu a ha arsa. Fatar jikinsa da tayi matu ar yin kyau sai she i take farinsa ya ara bayyana idan ba wansa ya san Mashkur sani na ha a ba idan ya ganshi ba zai shaidashi ba dan gaba aya ya sauya ga hutu da ya ara bayyana a tattare dashi sai amshi turaruka da ke tashi daga jikinsa masu matu amshi. ofar ya maida ya rufe tare da sanya key ya rufe ofar, gidan ya durfafa cike da shau i marar misaltuwa. Zahra ita ka ai ce cikin gidan Ammi da Hauwa'u sun fita za su je gidan suna a can ciki anguwar, dan haka ita ka aice a gidan, tashi ta yi tana so za ta shiga bayi sandarta ta lalimo a hankali ta shiga dafa bango tana lalumawa ha e da neman ofa da sandarta ta.Sai dai Ammi tace Hauwa'u ta zauna amma Zahran tace su je tare tunda ita Hauwa'u awarta ce me haihu ita Ammi maman yarinyar ce suke zumunci.Dan haka ma Zahra tace su je babu komai za ta zauna ita ka ai duk dama ba wani da wuri suka fita ba sai bayan la'asar. A haka har ta je wurin ajiye butoci ta au butar ta nufi hanyar bayi. "Assalamu Alaikum!!!" Wani bugawa gaban Zahra yayi da mugun arfi, jin muryar da ta daki dodon kunnenta Mashkur kwa jin ba a amsa ba yasa ya ara yin sallamar a karo na biyu, Zahra bata san lokacin da ta saki butar hannunta ba tsabar yanayin da ta tsinci kanta a ciki wanda ta kasa gane farinciki ne ko akasin haka. Mashkur kwa jin ba a amsa masa sallama ba dama daga cikin zauren ofar gdn yake hakan yasa ya ara sallama a karo na uku a niyyarsa idan ba a amsa ba zai koma ne ya sake dawowa duk da ya san cewa akwai mutane a gdn tun da gdn a bu e yake. "Wa alaikumus salam"Zahra ta tattaro gaba aya arfin gwiwarta ta amsa masa sallamar cikin sanyin muryarta. "Ya salam"Mashkur ya ambata a cikin zuciyarsa jin muryarta cikin dodon kunnensa hakan ya sa ya fara tunanin ko dai a mafarki ne tazo masa kamar yadda ta sake zuwa masa a mafarki.Hannu yasa ya murje idanunsa jin idanunsa biyu ba a mafarki bane hakan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ya fara takowa cikin gidan a ransa yana ayyana cewa yau sai dai Ammi ta kauda idonta domin ba zai nuna kara ko kawaici ba akan Zahra yadda yake ji a cikin zuciyarsa yayi kewarta wacce bata da kwatankwaci ko misali, kewace da zai iya cewa bai ta a yin irinta ba a tsawon rayuwarsa bai ta a kewar wani abi ba sama da Zahrarsa. Yana shigowa da ita ya fara tozali a hanyar bayi tana tsaye ri e da sanda a hannunta sai buta dake yashe a asa wacce har murfin ya bu e ruwan ya zube da alama
Chapter 53 · 0% Book details