Sashe 57
Sanadin Kishiya Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dabino ya auna da yawa da farar alewa yana sadaka ba dare ba rana sannan ya dinga siyan butoci da makayan ruwa yana kaiwa masallatai sadaka duk akan Allah ya baiwa Zahra lafiya, saboda ita sadaka maganin kowace irin masifa ce.Sannan ya bada sadaka ake sauke qur'ani domin Allah ya warware wannan ulli da aka mata saboda kowa ya da e da gane cewa wani abu aka mata ta samu kan ta a cikin larurar duk da sun yarda cewa Allah ne ya ora mata amma tabbas akwai wani wanda shi ne silar komai. Shi ma kuma karatun qur'ani ba dare ba rana, sai da ya yi kwana shida ban da masallaci ba inda yake zuwa, ranar da zai cika sati guda da daddare ya akko ruwa a wani aramin makayi ya ajiye a kusa da dardumar da yake ibadah sai da ya yi raka'a 12 sannan ya zauna ya ringa azkar ya karance 99 names of Allah sai kuma ya yiwa annabi S.A.W sannan ya aga hannayensa sama ya ce. "Ya ubangiji kai ne mafi ji da gani, kai ke addarawa bayinka komai, sannan kai ke orawa bayinka rashin lafiya kuma ke kake yaye musu.Ya Allah kai ka ce a ro e ka zaka amsa, ya Allah gani a cikin sulusin dare a lokacin da kake sakkowa sama ta aya kana neman wanda zai ro e ka ka biya masa bu atarsa, ya rabbi gani ina mai antar da kai na a gareka ya Allah ina ro on ka ka baiwa Zahra lafiya, ya Allah ka yaye mata jinyar nan ta uraje da makantar da take tare da ita, da duk wata damuwarta da ma musulmi baki aya,ya Allah cikin iko da hikimarka ka warkar da baiwar nan taka cikin gaggawa alfarmar annabinmu manzonka S.A.W" Yana kaiwa arshen addu'ar ya ara rufe addu'ar tashi da salatin annabi S.A.W domin addu'a na saurin kar uwa a yayin da aka bu e ta da salatin annabi S.A.W aka kuma rufeta da salatin annabi S.A.W. Bayan ya kammala ya akko ruwan wannan ya shiga karanta suratul yasin, ayatul kutsiyu, la adja'akum, ulhuwallahu ahad, fala i da nasi yana karantawa yana tofawa a ciki har sai da ya gama sannan ya karanta Allahumma yashfiki sau 100 yana kammalawa ya ure ruwan a cikin gorar suwan a ajiye. Haka ya zauna yana ta lazimi har aka kira sallar asuba, sannan ya sake yin alwala ya wuce masallaci. Zahra ma a nasu angaren suna ta addu'a da neman waraka daga ubangiji, duk da bata san me Mashkur zai yi ba yace mata zai auki sari guda bai zo wajenta ba akwai wani uzuri mai muhimmanci da zai gabatar amma bai fa a mata menene ba.Ita kuma sai ta masa fatan alkairi duk da bata san me zai gabatar ba amma tabbas ta san lallai abu ne mai matu ar muhimmanci tun da har uzurin zai hanashi zuwa wajenta.Hakan yasa ta maida hankali ita ma ga addu'a tare da su Ammi ma gaba ki aya. _WASHE GARI_ Wajen arfe goma na safe ya shirya tsaf cikin farar jallabiya da wandonta farare tas, sai amshi ke tashi daga jikinsa.Wayarsa ya auka ya kunnata dan yau kwannata 7 a rufe dan shi ko wayar ma baya so ya yi saboda kawai kwanakin da ubangijinsa kawai yake so ya gana, gorar nan ya akko mai auke da ruwan addu'ar nan tare da makullin motarsa.Sallama ya yiwa Umma dama Baba baya nan ma ya fita, sa on gaisuwa ta bashi wajen Ammi. Motarsa ya shiga ya mata key ya shiga yin tu i cikin natsuwa, bai zama ko ina ba sai gidan su Zahra.Bayan an masa iso ya shiga suka gaisa da Ammi take tambayarsa Ummarsa ya sanar da ita tana lafiya tana ma gaishe da ita.Hauwa'u ma ta gaishe da shi, sannan ya baiwa Ammi ruwan addu'ar ya mata bayanin yadda za ayi amfani da shi.Ammi kira ta awala Zahra da ke aki dan nauyin Ammi bai sa ta fito ta gaishe da Mashkur in ba. Nan Ammi ta shiga mata bayanin ta je ta shiga wanka Ammin ce ta zuba ruwan wankan tare da zuba rabin gorar ruwan a ciki ta bar rabin a cikin gorar.Ruwan ta mi a mata bayi ita kuma ta je ta shiga wankan dan dama ruwan kawai za a yi wankan da shi banda sabulu. Suna nan zaune Mashkur da Hauwa'u yana nuna mata yadda za ta yi wani assignment na islamiyarsu, Ammi kwa tana an aike aikenta. A lokacin da Zahra ke bayi tana wankan a can gidan malamin da ya yiwa su Zee-zee aiki Zahra ta samu uraje da makanta, yana nan kwance ba lafiya yana cikin wannan halin na rayuwa ko mutuwa kawai sai ya ji tunanin Zahra ya fa o masa akan aikin da ya mata na uraje da kuma mayar da ita makauniya.Duk da ya yiwa mutane da dama aiki amma bai san dakilin da yasa ita ta fa o masa a rai ba yanzu, hakan yasa yana jan ciki ma ya akko wata jakarsa da ke auke da magunguna da abubuwa masu tarin yawa a ciki, wani ullin magani ya akko da dodon ko i guda aya ya zuba maganin a cikin dodon ko in ya an jijjiga, sai ya aga dodon ko in ya yi jifa da shi a jikin bango a take ya fashe tare da tarwatsewa wannan shi ne makarin duk wani aiki da ya yiwa mutane to zai karye a yau in nan, amma bai san dalili ba duk ya yi hakan ne saboda Zahra domin itace ta fa o masa har ya karya aikin da ya yiwa mutane baki aya ta dalilinta ni kwa na ce arfin addu'a ne malam.Yana gama tarwatsewa sai ya fara shure shuren mutuwa yana cewa Allah ka yafe min laifukan da na yi, cikin ikon Allah kuma sai ya cika da kalmar shahada. A nan hadisin da ke cikin arba'una hadis ya fito, an adam zai yi ta aiki rin na an wuta sai ya kasance tsakaninsa da ita (wuta) bai fi taku aya ba sai littafinsa ya rinjayeshi sai kuma ya yi aiki irin na an aljanna sai ya shigeta.Wani mutum sai ya rin a yiwa Allah biyayya baya sa a masa tsawon shekaru amma kuma sai yana dab da barin duniya sai a fara wani sa on Allahn da zai mutu yana aikatashi, wanda hakan aikin nashi zai iya sanyawa ya shiga wuta.Wani kuma sai ya yi ta sa on Allah sai ya zo dab da mutuwa idan Allah ya so shi da rahma sai ya shiryu ya cika da kalmar shahada. Duk da cewa ubangiji na gafarta zunubai gaba aya kuma yana gafarta laifin da mutum ya mutu yana aikatawa matsawar dai ba shirka ba ce ma'ana ha a Allah da wani wajen bauta. *Zahra* A lokacin da malam ya fasa dodon ko in nan, ya yi dai dai da gama zuba sauran ragowar ruwan a jikinta, hakan ya sa ta ji fatar jikinta ta yi suwal babu tudu tudun kurarrajin, numfashinta ne ya auke na wucin gadi kafin daga bisani ya dawo ta sha i numfashin da mugun arfi, a hanzarce ta shiga shashshafa jikinta har fuskarta amma ko alamamar urajen bata ji ba. Cikin sauri ta maida kayanta tare da sanya dogon hijabinta, sandarta da je jingine jikin bangon bayin ta auka, ta bu ofar ta fito bakinta auke da addu'ar fitowa daga bayin da sauri take takowa har tuntu e ta ke yi. "Ammi ku zo dan Allah ku gane mini, duk da ba gani nake ba amma na ji kamar babu urajen nan kwata-kwata" Cewar Zahra tun kan ta araso barandar ma Da sauri Hauwa'u da Mashkur suka tunkarota kowa cike da farinciki suna arewa fuskarta da kuma hannayenta da ta fito daga hijabin tana nuna musu. "Ya Zahra wallahi tas jikinki babu alamar uraje ko tabo babu"Hauwa'u ta ce tana doka tsalle ta ane Zahra cike da murna, Mashkur kwa dur usawa yayi ya yi sujada sujudush shukur sannan ya ago yana mai aga hannayensa sama yana godewa Allah. Ammi ma sujadar ta yi har da hawayen farinciki, dan ita ganin Mashkur ya tafi wurin Zahra sai ta yi kawaici ta tsaya a inda take. "Alhamdulillahi!!!"Zahra da Hauwa'u ke ta faman fa a.Gaba aya sun ru e da murna, bayan abin ya lafa sai Mashkur ya ce Ammi ta akko sauran ruwan goran a arasa amfani da shi kamar yadda ya fa a mata. Ammi na akkowa ta zubawa Zahra a tafin hannunta ta ce ta yi bismillah ta wanke fuskarta, haka kuwa akayi tana zuba mata tana yin bismillah tare da wanke fuskar har sai da ruwan ya are tana gama wanka na arshe kawai sai ta ga idanunta ya bu e daga mannewar da ya yi gaba ayan su fosta su ka yi suna jiran ganin ikon ubangiji,aikuwa mannewar na fita idanun ma suka fara washewa a hankali sai ga Zahra ta fara ganin dishi-dishi zaro idanun ta yi cikin mamaki sai kwa ta ga idanun ya washe tas.Akan fuskar Mashkur idanunta suka fara sauka, sannan ta juya tana kallon Ammi da Hauwa'u. "Wallahi duk ina ganinku"Cewar Zahra idanunta na cikowa da walla. Gaba aya kowa ya rikice da murna sai godiya suke yiwa ubangiji akan wannan baiwa da amsar addu'a da ya musu.Bayan sun gama murnar Ammi ta shiga aki ta bar su anan suna ta hira cikin farinciki, Zahra, Mashkur, da Hauwa'u .Duk da cewa bu ewar da idon Zahran ya yi sai take ganin kowa kamar sabon halitta kamar dai yau ta fara ganin su, musamman ma Mashkur da ta ga gaba aya ya canja mata yab ara zama an gayu sannan hutu da wayewa sun ara bayyana a gareshi. Allah ka ai ya san irin tarin farincikin da ke cikin zuciyarta marar misali, sai godiya take yiwa Mashkur akan addu'ar da ya kawo mata wacce ita ce silar samun lafiyarta.Shi kuma yana nuna mata babu godiya tsakanin su.Hauwa'u tun ana hirar da ita da ta ga akalar hirar ta canja zuwa hirar soyayya sai ta tashi ta basu wuri tana musu tsiya. Bai baro gidan su Zahra ba sai wajen arfe aya saura, shi ma dan yana so ya je ya tafi sallar