← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 91

Sashe 89

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da sassafe ya fita, ruwan tea kawai ya sha ya fita har ya kusa kai wa bakin ƙofa ya dawo ya manna ma ta kiss a goshi ya ce " sai na dawo"

Sai alokacin Farida ta saki ranta ta ce " Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya" ya amsa da amin sannan ya fita...

Shiru- shiru har ƙarfe uku Najeeb bai kira ba bai kuma turo text ba. Ina Kano da Kaduna ace tun bakwai saura da ya tafi bai isa ba. Da farko ta ɗauka ko dan maganar jiya ne amma yanzu kam hankalinta ya tashi dan duk faɗan da su ka yi ko text zai tura ma ta ya ce ya isa.
Ta fara kiran numbar sa switch off, ta kira numbar Abdullahi dreba shima switch off. Nan jikinta ya hau rawa ta shiga kiran Mom. Tambayar Mom ta yi ko Najeeb ya kirata ta ce ma ta a'a.
Cikin kuka ta ce "Mom ki tambayamin Daddy ko sun yi magana da shi"...

Zaune su ke a falon kowa yai jugum saboda rashin sanin halin da Najeeb ya ke, da shi da dreban sa duk wayoyin su a kashe.
Daddy dai baya nan dan ya fita kai report ko zai ji labari ko anyi hatsari hanyar Kano to Kaduna.

Najma na jijjiga É—an ta Bobo da ke kuka wayar Farida ta fara ringing Farida ta yi saurin tashi ta É—au wayar da ke kan centre table. Ganin My Champion ke kira ya sa ta fara murmushi.

"My Champ saura kaÉ—an na mutu yau, ina ka shiga? Are you Ok"

"Yana nan lafiya idan har kun amince da sharuɗɗan mu" muryan wani ƙato ya doki kunnen ta.

"Waye, mi kuka yiwa mijina? Ina mijina?" Tambayoyin da ta fara jerowa kenan.

Jin maganarta ya sa Mom tashi da sauri ta amshi wayar ta sa a speaker tana faÉ—in " ina Najeeb?, mi ku ke so"

Mutumin yai wata mahaukaciyar dariya sannan ya ce " Najeeb Adam Jibo yana nan lafiya until kun fanshi ran sa a wajen mu"

" what do you want?" Mom ta faÉ—a tana danne hawayen ta.

"200million" ya faɗa a taƙaice.

"Ka bawa É—ana mu yi magana"

Mutumin ya sawa Najeeb waya a kunne.

"Mom i'm ok, ku kwantar da hankalin ku." Jin kukan Farida ya sa shi cewa " My Queen dan Allah ki dena kuka"

Mutumin ya ƙarɓe wayan ya ce " kun ji shi dai yana raye, nan da 24hrs idan ba mu ga kuɗi ba za mu aika shi lahira" daga haka ya kashe wayan.

"Hello Hello" Mom ta faÉ—a amma shiru, sake kiran numbar ta yi amma ta ji shi a kashe.

Farida ta dafa kafaÉ—an Mom tana faÉ—in "Kashe shi za su yi ko? Kashe min shi za su yi ko?"

Ƙoƙarin faɗuwa ta ke yi Mom ta riƙota tana kiran sunan ta amma....

*Jirgin SAKATARIYA TA yana shirin sauka jama'a, jirgin ya yi wata É—aya da 'yan kwanaki yana lulawa a sararin samaniya kuma Alhamdulillah yana daf da sauka da daren yau Insha Allah. Da fatan Team Najeeb da Team Farida za su yi cincirindo a filin jirgi su ga saukan mu sannan su bamu masauki mai kyau. Wanda su ka supporting É—ina by paying to read this novel Jazakumullahu khairan. Wanda su ka karanta ta bayan fage kuma...*

Skt 60

Haihuwa ne ya taso wa Farida gadan-gadan bayan sun kaita asibiti wurjanjan. Ba ƙaramin wahala ta sha ba kafin ta haihu dan sau biyu tana suma a wajen. Lokacin da 'yar ta fito gaba ɗaya ta gama galabaita jinin ta ya hau sosai, ga azabar haihuwa ga kuma tashin hankali.

Saboda yadda ta rikice dole sai da su ka ma ta allurar bacci.
Tun a asibiti Mom ta kira Daddy ta sanar da shi halin da ake ciki daurewa yai ya ƙaraso asibitin dan hankalinsa ya mugun tashi.
Lokacin da ya iso Mom na ɗauke da jaririyar da ke kama da uwar ta sak. Ya karɓi jinjirar yana ma ta addu'a...

Bayan an tabbatar ma sa da lafiyar Farida ƙalau sannan ya bar asibitin saboda ya je ya sanar da jami'an tsaro...

Wannan karan waɗanda su ka kama Najeeb da Abdullahi ba ƙananun kidnappers ba ne domin duk yadda ake ƙoƙarin gano inda su ke abin ya faskara. Washe gari Daddy ya je bank aka fara ƙoƙarin cire kuɗi, abu da manyan mutane cikin abinda bai fi awa uku ba aka gama haɗa 200million...

......................

Ummi ce ke zaune gefen Farida tana riƙe da baby tana ɗan shafa bayanta saboda kuka da ta ke yi. Yarinyar ba dai kuka ba, ga shi uwar ta ko ta kan ta ba ta yi, damuwar da ke ranta ya isheta.

"Farida ki karɓe ta ki ba ta nono dan Allah. Ba ta da wani ƙwari fa"

"Ummi idan su ka kashe shi mutuwa zan yi, ba zan iya rayuwa babu shi ba" ta faÉ—a hawaye na bin kumatunta.

"Ba na son kina magana kamar wacce ba ta da imani. Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah ya ke kuma zai kuɓutar da mijin ki Insha Allahu. Tashi ma za ki bata nono dan Allah"

Da ƙyar Farida ta iya miƙewa zaune tana jin duk gaɓoɓin jikinta na ma ta ciwo, ta amshi jinjirar daga hannun Ummi ta fara ba ta nono har lokacin ba ta dena zub da hawaye ba.
Ummin ma tausayin 'yartata ne ya cika ta amma dole ne ta dinga ƙarfafawa 'yarta gwiwa saboda halin da ta ke ciki...

A kwana na uku da haihuwar aka sallameta su ka dawo gida. Yau ɗin ne kuma kidnappers ɗin su ka ce za su sake Najeeb dan jiya aka aika mu su da kuɗin su. Ƙarfe goma Mom, Farida da Ummi su ka iso gidan wanda ke cike da 'yan uwa. Kowa a wajen yana jimamin abinda ya faru ne ana kuma jiran dawowar Najeeb...

A hankali Mom ta taimaka ma ta ta zauna a bakin gado, har yanzu ba wai tana da ƙarfin jiki ba ne kawai dai dauriya ta ke yi.

"Mom zan sha ruwa" ta faɗi tana ƙoƙarin kwantawa akan gadon.
Mom ta ce tana zuwa. Ummi ta kwantar da baby a gefen Farida tana faÉ—in "ta ma yi bacci ashe"

Tun safe ake jiran dawowar Najeeb har yamma shiru.
Ihun da gidan ya karaɗe da shi ne ya farkar da Farida da ke bacci. A hankali ta buɗe ido tana maida hankalin ta ga abinda ta ke jiyowa. Jin ana kabbara da faɗin Alhamdulillah ya sa ta miƙe tsaye zumɓur ta fita da gudu duk da kuwa yadda jikin ta ya ke very weak.

Tun daga stairs ta hango shi yana murmushi, an yi cirko-cirko ana kallon shi ana kabbara, gefen sa Daddy ne riƙe da hannun sa ɗaya, shima ɗin fiskar sa ɗauke da murmushi. Tun da ta gan shi ta rage saurin da ta ke yi ta koma saukowa a hankali. Hajiya Fatima ce ta fara kallon ta ta ke cewa " Farida Alhamdulillah kin ga sun sake shi ko"

Tsayawa ta yi tana ƙarewa mijin na ta kallo, kayan jikin sa ne tun na ranan da ya fita, kayan sun ɗan yi bututu, akwai tabon ciwo a goshin sa da gefen bakin sa. Sai duhu da yai da alama bai ga ruwa ba a 'yan kwanakin nan.

Ɗago ido da zai yi ya kalleta tsaye ta zuba ma sa manyan idanun ta. A hankali ya cire hannun sa daga jikin na Daddy ya taka zuwa wajenta yana zuwa ya rungumeta tsam ajikin sa kamar zai shigar da ita ƙirjin sa ne. Sun jima a haka kafin Farida ta iya cewa "it's a girl, your princess is born"

"Alhamdulillah ala kulli Haal" ya furta ya na sauke ajiyar zuciya.

Aƙalla sun yi minti biyu rungume da junan su. Hawayen da ya gani a fiskarta ne ya sa shi sa hannunsa duka biyu yana goge ma ta su yana faɗin "Queen ba na son kuka please" sake shigewa ta yi jikin sa tana murmushi...

.......................

Su na shiga É—aki ta sa key ta kulle. Kafin ma ta gama kullewa ya je wajen gado ya É—au 'yar sa da ke kwance tana bacci. Ya kissing goshin ta yana yi ma ta addu'o'i.

"She's beautiful, just like you"
Ya faɗa yana kallon Farida. Ganin ba shi da niyyar ajiye yarinyar ya sa ta amshi 'yar a hannunsa ta ce mu je na ma ka wanka. Ta maida yarinyar kan gado kafin ta ja hannunsa su ka shiga banɗaki. Ita ta sa hannu ta cire ma sa duk kayan jikin sa wanda ta san daga yau sun gama aiki dan ƙona su za ayi. Yana tsaye yana binta da kallo ta fara murza ma sa shower cream a jikin sa tana dirje dukkan jikin sa da shi. Da ta gama ta kunna shower ya wanke duk kumfan. Ta tsiyayi shampoo ta sawa gashin sa tana dirza ma sa especially scalp ɗin sa, ɗan rankwafowa yai da kan saboda ta samu daman wankewa da kyau cause ya fi ta tsayi. Sai da ta wanke shi sau biyu a bakin shower kafin ta tara ma sa ruwan zafi a bathtube ta ce ya shiga ciki. Ya ji daɗin ruwan zafin da ya shiga dan dama jikin sa na ma sa ciwo.

"I'm sorry my Queen" ya faÉ—a ganin hawaye da ta ke yi.

"Ni ce zan ba ka haƙuri miji na. I'm sorry you are married to a crazy woman"

Dariya ya fara yi yana faÉ—in "and i love my crazy wife"

Dariya itama ta yi tana cigaba da yiwa kafaÉ—un sa massage...

..........................

Duk ƙoƙarin 'yan sanda ganin an kama wanɗanda su ka kidnapping Najeeb abin ya ci tura. Kidnappers dai sun tafi da miliyan ɗari biyu wanda biya kam sai dai a lahira.

Ranan suna anyi ƙasaitacciyar walima, duk da anyi shagali amma bai kai lokacin sunan Yaman ba. Ko dan saboda abinda ya faru, oho.
Yarinya dai ta ci sunan Mom, an raÉ—a ma ta *Nabeelah Zafreen*

Wannan karon a gidan Daddy aka yi suna, infact sai da aka yi sati uku da sunan ma kafin su ka koma gidan su.

.........................
Chapter 89 · 0% Book details