Sashe 17
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wanka da ruwa mai zafi ta yi, ta gasa jikinta sosai, ta jima a banÉ—akin dan kwana biyu kenan ba wanka. Tana fitowa Ummi ta sa ta a gaba da abinci. Allah na gani bacci ne yanzu a idonta ba abinci ba amma da Ummi ta takura dole ta zauna za ta ci.
Ummi ta ƙarɓa cokali ta fara ba ta abincin a baki. Hakan ya sa Farida ta tuno lokacin da Sir Najeeb ke ba ta abinci, haka kawai sai ta tsinci kan ta da murmushi.
*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0ï¸âƒ£1ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
Tana tsaye jikin balcony na gidan tana kallon mai yankan flower wanda ke faman gyara flowers ɗin gidan, ya saƙalo hannunsa ta ƙugunta sannan ya manna ma ta kiss a wuya ya ce "do you like it?"
"Gidan yai kyau sosai. Its perfect" ta amsa ma sa
Juyo da ita yai ya ce"This is our home Aysherh"
Murmushi ta yi ta manna ma sa light kiss sannan ta ce "our home is beautiful my love"....
A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe shaɗaya na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, ya taking hot shower ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar maghrib da Isha, kaman yana azkar bacci ya tafi da shi. To wa ya maidashi kan gado? Ya janye tunanin ta hanyar tashi ya shiga banɗaki...
Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Mom tana haurawa sama.
"Son ya jiki?" Ta faÉ—a a hankali
" lafiya Justice" ya faÉ—a ba tareda ya kalleta ba.
Mom ta bishi da ido tana haÉ—iye wani abu mai É—aci da ya taso ma ta tun daga wuya.
Adama ya samu tana goge-goge a falo.
"Hey ina baby?"
"Sir ta tafi makaranta"
"Dad fa"
"Yana waje"
Fita yai daga falon dan ya san inda zai samu Dad É—in.
A wajen gazebo da ke garden ya samu Dad, yana zaune yana karatun littafi.
"Come here son" Dad ya faɗi lokacin da Najeeb ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Dad, Dad ya manna ma sa peck a goshi ya ce "Allah ya ma ka albarka"
Najeeb ya amsa da Amin
"Ya jikin na ka?"
"I'm fine Dad"
"Allah ya ƙara sauƙi"
Dad ya ajiye littafin ya fara bayani
"Ka ga irin abinda na ke gaya ma ka ko. Joseph ya ce korarsa da ka yi shi ya sa shi ɗaukan wannan mummunan mataki a kan ka. Ɗa na, ka dinga danne zuciyarka kana haƙuri da mutane, Allah ya baka ɗaukaka da daraja ne domin ya jarrabaka. Su wanda su ke ƙasa da kai akwai haƙƙin su akan ka kuma Allah zai tambayeka ranar gobe"
Ƙaran wayan Dad ne ya katse hirar ta su. Yana ɗauka ya ce " to muna shigowa"
"Najeeb, Hajiya ce ta zo. Mu shiga ciki"
Ba mu su ya tashi su ka jera da Dad É—in.
Hajiya Mama da kan ta ta yiwa Najeeb girki ta kawo, wai dole sai ya cinye dan ta san bai ci abinci ba a chan. Haka ta tisa shi a gaba yana cin abinci tana tambayarsa gameda kwana biyun da yai a hannun su Joseph. Mom na gefe tana kallon su, kwaÉ—ayin wannan dama da ta rasa ta ke yi, hira tsakanin uwa da É—a.
Ko sai yaushe Najeeb zai ba ta dama ta gyara kura-kurenta na baya?...
........................
Da yamma Yakubu ya kawowa Farida wayarta wanda aka samu a gidan da aka tsaresu duk da kuwa an yarda sim É—in ciki.
"Anas ya ce zai zo ya gaishe ki bayan sallar isha"
"Allah ya kawoshi lafiya" ta faÉ—i tana cin farfesun kayan cikin da Ummi ta haÉ—a ma ta...
Tana sallar Isha aka kira wayar Maijiddah. Maijiddah ta duba numbar ta ja tsaki ta ajiye wayar gefe.
Kwana biyu kenan Aneesa matar AbdulWahab tana damunta da kira da texts, ranan da ta fara kira ba irin É—ibar albarkar da ba ta ma ta ba. Gashi ita ba mai iya maida magana bane, haka ta gama zagin ta kashe wayar. Lokacin jimamin rashin Farida ya sa ba ta wani damu da abinda Aneesar ke ma ta ba.
"Matar AbdulWahab ce ta kira ki ko?"
Maijiddah ta gyaÉ—a kai.
"Ban wayar na bata amsar maganganunta"
Maijiddah ta langwaɓe kai ta ce " Anty dan Allah ki barta. Idan ta gaji za ta bari"
"Hmmm a tarihin rayuwata ba na gani in ƙyale dan haka bani wayar kawai"
Maijiddah ta miƙo wayar dan ba yadda ta iya.
Bugun farko ba a É—auka ba sai a na biyu.
"Assalamu Alaikum Uwargida ran gida, da fatan kina ta shirye-shiryen zuwan amarya?"
Daga ɓangaren Aneesa ta ce " who's this?" Dan muryan bai yi kama da na Maijiddah ba wacce ranan farko da ta kirata haƙuri ta dinga ba ta.
"Aisha Farida ce, yayar Amarya Hauwa Maijiddah. Na kira ne in gaya mi ki kar ki kuskura ki sake kiran ƙanwata saboda naga alama ƙwaƙwalwar kifi ce a kwanyar ki"
"Ke! ƙaramar karuwa ki kiyayi bakin ki. Ki kuma ja wa ƙanwar ki kunne karta yadda ta shigo gidana"
"Ashe ke Jaka ce, daƙiƙiya, Tinkiya mai kamar Aladu. Har kin isa ki hana Jidda zuwa gidan ki. Idan ba kwartonci ba, mijinki na Lagos kin maƙale a Abuja wai ke sarkin aiki. To tunda ke bakisan yadda ake riƙe miji a tarairayeshi ba, shi ya samu wacce za ta zauna kusa da shi ta kula da shi. Kuma wallahi wallahi ki ja girman ki ki dena kiran ƙanwata ko kuma mazaunanki su yi tsami"
Yadda Farida ke magana da faɗa-faɗa ya ƙara tunzura Aneesa.
"Ke matsa chan jahila mai kama da...."
Farida ba ta bari ta ƙarisa ba ta amsa da cewa " ke ce jahilar ai. Kwartuwa mai bin gindin maza, Allah ya wadai da halin ki. Tir da ke Aneesa mai ƙaton baki. Hooooo ashewo....Hoooo ashewo" (ashewo- karuwa)
Aneesa ta yi saurin kashe wayar saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Wannan wace irin yarinya ce haka, lallai kuwa Maijiddah za ta ci ubanta idan ta shigo ma ta gida. Sai da ta gama banbamin bala'i sannan ta dubi screen É—in wayarta ta sa hannu ta shafa lips É—in ta.
"Ko wa yace ma ta ina da babban baki? Ba dai AbdulWahab ba"...
Farida na jin an kashe wayar ta sa dariya ta ce " ƙaramar 'yar iska, da ki tsaya ma na"
Ta kalli Maijiddah da ta yi zuru-zuru da ido
"Ke kuma ki cigaba da yin shiru-shiru har wannan matar ta sa mi ki ciwon zuciya. Gara ki É—aure É—amara dan wannan matar da alama 'yar tasha ce"
"Sannu Malama Farida, expert a ɓangaren rashin mutunci"
"Kai Yakubu ba na son iskanci fa"
"Ki fito Anas na jiran ki a waje"
Gyale kawai ta yafa ta fita bayan ta gayawa Ummi. Gaishe shi ta yi lokacin da ta shiga motar na shi.
" 'yar uwa ya jiki"
"Da sauƙi yaya na"
" ashe ba ƙaramin jin jiki ku ka yi ba. 'Yar uwa ya abin ya faru ne? Najeeb ya ƙi ya bani labari"
Dama abinda ta ke jira kenan ta fara karanto ma sa yadda abin ya faru. Labarin da tun safe ta ke faɗawa 'yan gidan su da maƙota da ke zuwa gaisuwa.
Abu ɗaya ta ƙi faɗa wanda ita kanta duk yawar maganarta ta rasa dalilin ƙin faɗar da ta yi. Ta ƙi faɗin cewa Joseph ya tofa wa Najeeb miyau.
Sai da ta gama ba da labarin Anas ya ba ta wani envelope ya ce "wannan daga Najeeb constructions ne. KuÉ—in magani"
ya miƙa ma ta wani envelop ɗin ya ce " wannan kuma Dad ne ya baki, kuma ya ce na gaishe ki da jiki"
"Kai na gode sosai, ka miƙa godiyata wajen Daddy dan Allah. Najeeb constructions kuma sai mun zo mu ku sallama"
"A'a, 'yar uwa sallama kuma. Ba dai aikin za ki bari ba"
"Eh yayana, zan ajiye aiki da ku"
"Gaskiya ban yarda ba. Ai hutu kawai za ki yi na sati zuwa kwana goma ki dawo bakin aikin ki"
"Ya Anas Ummi na ba ta so, ta ce na ajiye aikin"
"No Farida, Najeeb needs you. Ki ba wa Ummi haƙuri ta barki ki dawo dan Allah"
" to bari mu ga ni dai. Na gode Yaya"
Sai da za ta fita daga motar ta ce " Ya Anas ya jikin Sir Najeeb?"
" da sauƙi ƙanwata" ya faɗi yana murmushi...
Ita ɗin ma da ta shiga gida sai ta ji kamar ba za ta iya haƙura da aikin ba. Musamman idan ta tuna bikinta da Rayyan zai iya kaiwa wata shida ma su zuwa...
Washe gari su ka wuce Jos ita da Ummi bayan ta yi welcome back É—in layinta.
.....................
Yana zaune a kujerar sa yana duba wasu files amma hankalin sa na kan wayar sa, jira ya ke ya ga ko an turo ma sa saƙo. Sai yanzu yai da na sanin ƙin bin Anas da yai ranan. Ko ba komai da ya ganta ya tabbatar lafiyar ta ƙalau.
Duk da ya san ba ta da numbar da ya tura saƙon. Ya ja dogon tsaki ganin har awa ɗaya kenan da tura saƙon na shi amma ba amsa, saboda ka da ta gano shi ma ya sa ya ke rubuta saƙonnin da Hausa. Da ya gama duba files da takardun da ke gaban sa ya tashi ya fita a office ɗin. Ganin kujerarta wayam ba kowa ya sa shi jin wani abu a zuciyar sa, ba dai da gaske barin aiki za ta yi ba. Kai tsaye office ɗin Anas ya wuce wanda ba nisa da na shi office ɗin.