← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 91

Sashe 34

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba na tunanin za ta yi haka, CCTV footage ya nuna ta shiga ta duba model É—in har ta É—au hoton su sai ta fita daga nan kuma bai sake aiki ba"

"Who?" Ya faÉ—a wannan karan a hankali.

"Farida, your secretary"

Juyowa yai a hankali yana huci, yadda Anas ya ganshi sai da ya tsorata.

"Najeeb i'm sure ba ita ta faffasa abun nan ba, there's explanation to this"

"Sir Najeeb baƙin sun iso" wani staff ya shigo ya faɗa.

Kawai sai Najeeb ya fashe da dariya, dariya sosai har da ƙyaƙyatawa.

"Najeeb fa za mu yi?"

Cikin dariya ya ce " ya za mu yi? Hhhhhhhh. Dude she won, she succeeded. Abinda ta ke so kenan dama, to make me look stupid. Ka san mi ta yi ranan? Na san ta gaya ma ka ma, but let me tell you again. This crazy bitch puts superglue on my seat, and ...and do you know what she said?"
Ya sake fashewa da dariya " she said *Tsuliyar CEO Najeeb Constructions a waje* the bitch dare say that to my face. Yanzu na san mi ta ke nufi, she wants me to be humiliated, to look stupid"

"Najeeb plz calm down" Anas ya faɗa yana ƙoƙarin dafa abokin na sa.

"Calm down?"

"Za mu nuna mu su 3-D powerpoint ɗin sannan mu ba su haƙuri akan modelling ɗin sai gobe, then kafin goben...."

"If you are stupid i'm not Anas, we've lost this contract"

Ya mangaje Anas ya fita a wajen. Wajen baƙin ya je aka gaggaisa sama-sama. Anas na wajen yana tunanin mi Najeeb zai yi.
Kawai sai ya ce baƙin su biyoshi. Su na zuwa ya nuna mu su modelling ɗin da aka ɓata.

"I'm sorry but a bitch secretary i hired did this"

Nan su ka fara masifa " this is unprofessional, Mr Jibo taya za ka bari mu zo tundaga Abuja only to see a destroyed work"

Anas ya shiga ba su haƙuri yana ƙoƙarin nuna mu su hoton zanen a Tab ɗin sa amma ba su saurare shi ba. "We are highly dissappointed in you Mr Jibo" babban cikin su ya faɗa sannan ya juya su ka tafi. Najeeb bai ce komai ba shi kuwa Anas bin bayan su yai yana ƙara ba su haƙuri amma ba su saurare shi ba...

Najeeb ya jima a ɗakin kafin ya fito, yadda ya ke tafiya kaɗai ka san yana cikin tsananin ɓacin rai.
Yana shiga office É—in ta ya tadda Farida tana waya sai dariya ta ke.

Kallon tsana ya fara ma ta kafin daga baya ya nuna ta da É—an yatsa " i will revenge Miss Salihu, bit by bit"
Tunda ta ga yadda ya shigo fiskarsa ba alamun wasa ko kaÉ—an ta yi saurin kashe waya tana sauraron mi zai ce dan ta É—an tsorata da yanayin sa.

"Ni kuma mi na yi" ta faÉ—a lokacin da faÉ—i kalmar É—aukan fan sa.

Ba a jima ba Anas ya shigo.

"Najeeb mutanen nan sun tafi, we lost the project"

Najeeb bai kulashi ba ya ma rigingina kansa jikin kujera yana kallon sama ya É—an juyawa a jikin kujera a hankali.

"Najeeb lets investigate this issue. Ina da yaƙiƙin ba Farida ba ne ta yi wannan aiki"

"She did it" Najeeb ya faÉ—a a hankali.

Kafin Anas ya fito Yakubu ya zo office ɗin Farida yana ba ta labarin abinda ya faru. Farida ta dafe ƙirji tana faɗin " wayyo Allah, yanzu wahalan Sir Najeeb duk a banza"

"Farida mi ya sa ki ka shiga wajen nan?"

Ta É—an rage murya ta ce " ba dai kana tunanin ni na yi wannan aika-aikan ba"

"Farida camera ya nuna ke ce ki ka shiga wajen nan na ƙarshe and ke yanzu ake zargi"

"Na shiga uku wata sabuwar sharrin da za a min kenan. Ni fa abin ne ya min kyaun na je na ɗau hoton sa. Ga ma hotunan a wayana" ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin buɗo hotunan a wayarta.

Anas ya fito ya same su, the same tambaya ya ma ta akan miya sa za ta shiga É—akin nan, amsar da ta bawa Yakubu shi ta bawa Anas.
Anas ya girgiza kai ya ce " Farida akwai matsala fa, Najeeb yana zargin ki, kuma idan ba'a gano wanda yai wannan abin ba i'm sorry but abinda Najeeb zai iya mi ki ba zai tsaya a kora kaÉ—ai ba"

"Wayyo ni Aisha, yanzu ba za a barni na rabu da Sir Najeeb lafiya ba"

Bayan sun bar office É—in ta ta shiga office É—in Najeeb, har lokacin yana zaune yana kallon sama.

"Sir Najeeb wallahi wallahi ban ruguza ma ka aikin ka ba, hoton abin kawai na É—auka saboda ya birgeni" haka ta dinga zancen ta ita É—aya ba tareda ya tanka ma ta ba, da ta gaji da kan ta ta fita daga office É—in.

Wannan abu ya sa ta manta da batun miliyan biyu da ta gani a account É—in ta da safe.

Zuwa rana duk Farida ta shiga damuwa, wannan ya shigo ya ma ta Allah wadai da halin ta wannan ya shigo yana son yi tsaigumi da gulma. Tun tana mu su masifa har ta gaji ta haƙura, idan mutum ya zo har ya tafi ba ta tanka ma sa. Ranan fa gaba ɗaya kamfanin ya rikice. Rashin samun wannan contract zai jawo mu su asara sannan sunan Kamfanin su zai samu mummunan shaida a gari da ƙasar ma gaba ɗaya.

Lokacin da aka tashi Farida da ƙyar ta tashi ta tafi bayan ta leƙa Sir Najeeb wanda har lokacin ke zaune a kujera.

"Sir na san inada rigima amma wallahi ba zan yi abinda na san zai janyo wa kamfanin ka asara ba, tunda na san dukkan mu nan muna ci a ƙarƙashin ka" abin da ta faɗa kenan lokacin da za ta fita.

Ko da ta je gida ka sa taɓuka abin kirki ta yi. Jira kawai ta ke Yakubu ya dawo ta ji mi ke faruwa. Sai dai Yakubu bai dawo ba har chan dare lokacin ita kuma ta yi bacci.

Washe gari da sanyin jiki ta shirya ta tafi wajen aiki.
Ta fara zuwa office É—in Yakubu amma ba ya nan. Haka ta wuce office É—in ta tana fargaban mi za ta tarar.

Tana zuwa ta leƙa office ɗin Sir Najeeb amma ba ya ciki. Ta koma na ta office ɗin ta yi jugum. Ƙarfe tara saura Anas ya shigo, fiskar sa ba yabo ba fallasa.

"Yaya na ya aka yi?"

"Akwai babban matsala Farida. Kina cikin matsala, za'ayi board meeting a kan ki anjima. A ina ki ka san kamfanin VESTAC Farida?"

"VESTAC kuma?"

"Account details É—in ki ya nuna kamfanin sun turo mi ki kuÉ—i miliyan biyu jiya"

Sai lokacin ta tuno da maganar kuÉ—i.
"Yaya ni ban san su ba, jiya nima na ga alert, abinda ya faru jiya ne ma ya sa ban yi maganar ba"

"Farida.." shigowar Najeeb ya sa ya katse maganar ya tashi ya bi bayan Najeeb É—in.

"Allah ga ni gareka ni 'yar marainiyar nan. Wanda ya nufeni da sharri ka mayar ma sa ya Allah. Ya Rabbil Alaamin ka ceceni" ta faÉ—a a fili

Ba a jima ba Najeeb da Anas su ka fito, daga baya kuma Yakubu ya zo ya kirata.
"Farida ki yi ta addu'a kawai" abinda ya iya faÉ—a ma ta kenan lokacin da su ka baro office É—in na ta.

Da Bismillah ta shiga hall É—in.

Su kusan tara ne ko goma a wajen kowa yana zaune Najeeb na tsakiyar su.
Nu na ma ta kujeran da ke tsakiyar wajen aka yi ta je ta zauna. Kowa ya zuba ma ta ido. Ba ma kaman Najeeb da ke ma ta kallon tsana.

"Miss Aisha Farida Salihu, bincike ya nuna ma na ke ki ka lalata modelling da aka yi, ki ka sa aka sace takardun zanen. Mi za ki ce gameda wannan?"

"Ni ba abinda na yi, kawai dan na shiga na É—au hoto. Ni ba abin da na yi"

Wani a gefe ya ce " Miss Salihu binciken mu ya nuna kin haÉ—a hannu da Kamfanin VESTAC domin ki lalata sunan kamfanin nan ta hanyar sace takardun zane da kuma faffasa modelling É—in da aka haÉ—a"

"Ni ban san su waye VESTAC ba, jiya su ka turomin kuɗi batareda na taɓa sanin su ba"

"Ƙarya ki ke Miss Salihu, kin je bid ɗin da aka yi a Lagos tareda Mr Najeeb kuma kamfani VESTAC na ɗaya daga cikin wanda su ka je wannan bid ɗin, su na neman a basu wannan project"

" Allah ya isa na"

"Miss Salihu ga details na account É—in ki, miliyan biyu sun shigo mi ki jiya daga Kamfanin VESTAC, mi za ki ce gameda haka? " wani acikin su ya kuma faÉ—i.

"Ni kam kun sani a gaba da tambaya kamar wanda na kai ziyara ƙabari. Ni ban san VESTAC ba balle na san dalilin da za su turomin kuɗi"

Wani daga cikin su ya É—au waya yai kira ya ce " ku ce ya shigo"

Wani tsoho ne ya shigo, masinja ne a kamfanin tun farko-farkon buɗeshi, da ke a first floor ya ke aiki Farida ba za ta ce ta san shi ba sai dai kaman ta taɓa ganin sa.

Ce wa aka yi ya shigo yai bayani.

Ya zo ya tsaya gefen Farida saboda kujera É—aya ne a wajen ya ce " Ranka shi daÉ—e. Sakatariyar Oga Najeeb ta zo ta sameni akan an ba ta aiki amma ba ta san ya za ta aiwatar ba dan za a iya ganeta. Ta sanar da ni kamfanin Vekta"

"VESTAC" wani aciki ya gyara ma sa.

"Yawwa kamfani VESTAC sun ce ta lalata aikin da aka yi ta kuma sace takardun zane saboda ba sa so kamfanin nan ta samu wannan aiki. Sun ce za su ba ta miliyan biyu. Ni kuma ta min alkawarin za ta bani dubu É—ari biyar aciki idan na yi wannan aiki"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Tsohon banza ka ji tsoron Allah. Ni yaushe ma na taɓa magana da kai"
Chapter 34 · 0% Book details