Sashe 61
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Watarana sun fita supervision aiki wani waje. Tana gefen Najeeb yana magana da wassu sai ga wani mai saida cucumber a wheelbarrow. Wassu ma'aikata su ka nufe shi su na siya. Yadda mai cucumber ke yanka ta yana zuba yajin ƙuli sai ta ji yawun ta ya tsinke.
"Sir Najeeb ina zuwa" ta faɗa tana barin wajen da sauri. Zuwa ta yi aka yanka ma ta cucumber ta ɗari, ga albasa da aka yanka siri-siri da shi abin gwanin sha'awa. Tun a wajen ma ta ke ta haɗiyan miyau. Ta ƙarɓi ledan ta bi bayan Najeeb da ɗan sauri-saurin ta saboda ya nufi wajen da motar sa ta ke. Tana shiga motar ta buɗe ledar, ƙanshin albasa da ƙarago ya cika motar. Maimakon ya tada motar sai ya tsaya yana kallon ta yadda ta ke sa hannu tana cin cucumber.
"Kai! yajin nan ba ƙaramin maggie ya ji ba" ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido.
"Sir Najeeb za ka ci ne?"
"Miss Salihu..." sai kuma yai shiru ya tada motar
"Sir Najeeb ka san ba na iya juran yunwa, ga shi tun É—azu mu ke ta yawo cikin rana"
Bai kulata ba ya maida hankalin sa ga tuƙi da ya ke yi.
"Sir Najeeb Allah ka ci, kasan ance maza su dinga cin cucumber saboda yana ƙara mu su ruwa" ta yi saurin riƙe bakin ta jin abinda bakin ya riga ya faɗa
ÆŠan juyowa da yai ya kalleta ya sa ta ce "Sir Najeeb ka ji mi na ce ne?"
"Wani irin ruwa?" Ya faÉ—a ba tareda ya kalleta ba.
"Nima ban sani ba, kai namiji ne ai ka san irin ruwan ai"
"Ke kuma mace da ki ke ci mi zai ƙara mi ki?" Ya faɗa yana kallon ta.
Basar da zancen ta yi ta ce "tunda ba za ka ci ba shikenan"
Wajen traffic light da su ka tsaya ta cigaba da cin abinta. Hoton da ya É—auka daidai ta kai cucumber baki ne.
Rungume wayan ta yi tana dariya. Wani daɗi takeji a duk ilahirin jikin ta, rabonda ta ji daɗi haka tun ranan da su ka ci gasa. Kai ya ma fi. Hoton ta a wayan Najeeb, duk da ma ta san ya ɗau hoton ne dan ya dinga dariya saboda ga bakinta cike da abu kuma ga shi ta kai hannu tana son ƙara cusa wani cucumber.
"I love you Najeeb, I love you" yanzu kam ta yadda ko ba so bane to Najeeb yana jin wani abu gameda ita...
Wajen message ta shiga tana duba saƙonnin wayan wanda ba su da yawa kaman ɗaya wayar.
Text ɗin da ta ci karo da shi an tura wa wani number da aka saving da *Aysherh* ne ya tsaya ma ta a rai. Duka texts ɗin sai da ta bisu ta karancesu. Ta gane text ɗin amma kanta ne ya ɗaure. Numban Ayshern ta duba wanda ya sa numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan daƙiƙai.
" N-J, Sir Najeeb shi ne N-J" ta faɗa tana dafa ƙirji.
Sai yanzu ta gane shirmenta na baya. Tana ta neman ma su suna da ya fara da N a kamfani bayan ga mai Kamfanin nan da ke da sunan NJ
"N-J, Najeeb Jibo" ta furta tana dariya kaman wata zararriya.
Its true kenan abinda Anas ke faɗa. Najeeb has feelings for her. Zama ta yi tana tuno abubuwan da su ka faru tsakanin su tun daga farkon fara aikin ta da shi har ƙarshen haɗuwar su. Duk wani abu da zai yi hinting feelings ɗin Najeeb sai da ta zaƙulo shi...
Tana cikin mota ma sai murmushi ta ke wani lokaci kuma sai ta yi dariya. Hatta Dreban ta Abdullahi sai da ya tsargu ko Madam ɗin na sa ƙalau ta ke yau ɗin.
"Hajiya amma dai lafiya?"
"Lafiya Malam Abdullahi" ta amsa tana sake duba hoton da Najeeb ya É—auketa.
Ba su yi nisa da gida ba Daddy ya kirata akan ta zo gidan Hajiya Mama. Ta so ta ƙarasa asibiti ta ga mijinta ko da na minti ɗaya ne amma dole ta bari ta gama da komai dan ƙilan idan ta je wajen sa ba za ta iya barin gefen sa ba yau.
Cewa ta yi Abdullahi ya kai ta gidan Hajia Mama...
Ta san Hajia Mama ba lafiya tun kwanaki to amma kusan sati kenan da aka sallamota daga asibiti. Rabonta da 'yar tsohuwan ma kusan kwana takwas, tun tana asibiti rabon ta da ita.
Gaskiya 'Yar tsohuwa na jin jiki dan yadda ta ganta ba ƙaramin bushewa ta yi ba. Tana kwance akan gado su Mom, Daddy, Uncle Sulaiman da Hajia Fatima su na kewaye da ita.
Har ƙasa ta tsugunna ta gaida su, kafin Daddy ya ce "Mama ga Aishatun na ki ta zo"
Hajia Mama ta ɗan miƙa hannu tana yiwa Farida alamar ta zo. Farida ta ƙaraso ta tsugunna a bakin gadon tana riƙe hannun Hajia Maman.
"Aishatu ce ko?"
Hajia Fatima ta ce "e ita ce, ba kin ce a kira mi ki matar Najeeb ba"
"Najeebullahin ya tashi ne?"
Farida da idon ta ya ciko da hawaye ta ce "zai farfaÉ—o Insha Allahu Hajia"
Hajia Mama ta É—an yi murmushi, ta san Allah bai bata haihuwa ba amma ya bata 'ya'ya da jikokin da za su tuna da ita bayan rai yai halin sa.
Akwai wani awarwaro kaman bangle na zallan azurfa da ke hannun Hajia Mama. Ko su Daddy da shi su ka tashi su ka gan ta. Ba su taɓa gani ta cireshi ba.
Hajia Mama ta sa hannunta ta cire awarwaron azurfan ta miƙawa Farida.
"Mutane dayawa sun nemi na bar mu su wannan awarwaron amma na ƙi, kin san miyasa na baki?"
Farida ta girgiza hawaye na zubowa a idon ta.
"Na yiwa Najeebullahi alƙawarin zan bawa matar sa awarwaron nan..."
Tari ne ya ƙwace ma ta. Ta jima tana yi kafin ta cigaba.
"Kyautar budurci ne, tundaga ran da Alhaji ya sa mi ni a hannuna ban taɓa cire shi ba sai yau. Ki riƙe shi da daraja"
"Insha Allah Hajia" ta faÉ—a tana sa awarwaron a hannun ta.
"Allah Sarki Najeebu na. Allah ya tashe ka"
Kowa a wajen sai hawaye.
Mom ta taso ta durƙusa gefen Farida da ke sheshsheƙar kuka.
"Hajiya" Mom ta faÉ—a cikin raunatacciyar murya
"Nabilatu ce"
Mom ta gyaÉ—a kai.
"Ki yafe min dan Allah. Najeeb ya yi gaskiya ni ba uwa ta gari ba ce, ranan da Aisha za ta rasu ta kira ni sau biyar, kuma daga jin yadda take nishi na san tana jin jiki amma kishi ya rufe min ido ban je na taimaketa ba, ban kuma kira an je an taimaketa ba har ta haihu ita kaÉ—ai ta rasu ba kowa a wajen ta. Ki yafemin"
"Allah Sarki Najeebu ashe dai dalilin da ya sa ya ke gudun ki kenan. Na yafe miki, ai dama sababin mutuwar Aisha rubutacce ne tun kafin ta zo duniya. Allah ya yafe mu gaba É—aya. Na yafe wa kowa"
..................
Duk wani É—okin zuwa asibiti da ta ke sai ta ji ya fita a ranta. Tana so ta tsaya da tsohuwar nan wanda ta ke cike da tarin barkwanci.
Ranan ba ta bar gidan ba sai taran dare. Da ta je ma kuka ta dinga yiwa Najeeb tana nuna ma sa awarwaron da Hajia Mama ta bata...
Da asuba bayan ta yi sallah ta yi azkar ta ɗau alƙur'ani ta zo saitin kunnen Najeeb tana karanta ma sa kamar yadda ta saba. Da ke asabar ne ba za ta je aiki ba. Kusan ƙarfe shida da rabi sai ga kiran Mom akan Allah ya yiwa Hajia Mama rasuwa tsakar daren jiya, tun daga wajen ta fara hawaye...
Tareda ita aka yi karɓan gaisuwa har na kwana uku. Cikin kwanaki ukun nan sau ɗaya ta ke zuwa duba Najeeb...
7days later
Daren ranan jummu'a tana zaune akan kujera tana karatun ƙur'ani bacci ya sace ta. Tana bacci ta yi mafarki Najeeb ya farka yana kiran sunan ta. Da murmushi ta buɗe ido lokacin da ta farka. Haka kawai sai ta tsinci kan ta da zuwa dubashi ko dai da gaske mafarkin ta zai zama gaskiya.
Ƙura ma sa ido ta yi, kaman a mafarkin sai ta ga gashin idon sa yana ɗan rawa, chan kuma sai idon ya buɗe, ido ta zaro ganin idon sa ya buɗe. Sake rufe idon yai ya sake buɗewa a karo na biyu a karo na uku kam da ya buɗe bai sake rufewa ba.
Farida da ta yi suman tsaye na ɗan daƙiƙai ka sa yarda da abinda idon ta ga gani ta yi ta fara murza idon ko dai har yanzu bacci ne a idon ta. Ganin idon sa a buɗe ta mari kumatun ta da ƙarfi dan ta tabbatar dai ba mafarki ta ke ba. Bakin sa ta ga yana motsawa kamar zai yi magana amma bakin ya ma sa nauyi. A hankali ta ƙarasa wajen sa hannun ta na rawa ta kai yatsar ta kaman za ta sa a idon sa sai ta ga ya fara ƙyafƙyafta idon.
"Sir Naj..." maganar bai ƙarasa fitowa ba ta faɗi wajen a sume...
*Team Najeeb ku sha rawan shoki wannan page na ku ne*
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0ï¸âƒ£3ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
Yana son ɗaga hannun sa amma hannun ya mai nauyi banda yatsun sa da su ke motsi ya kasa ɗaga hannun sama. Da farko baƙi ya ke gani daga baya kuma ya ci karo da idon mutum. Ba zai iya cewa ya san mai idon ba hakanan kuma ji ya ke kaman ya jima yana kallon mai idon. Ƙaran na'ura da kuma abubuwan da ya ga an jona ma sa a ƙirji ya tabbatar ma sa a asibiti ya ke. Ƙoƙarin tuno dalilin da zai kawo shi asibiti ya ke amma ya kasa. A hankali ya fara ƙoƙarin tursasa ma ƙwaƙwalwar sa domin ta gano abinda ya kawo shi asibiti. Yana so yai magana amma ya kasa, haka ya cigaba da kallon sama still yana ƙoƙarin gano miya faru da shi da kuma inda ya ke.