Sashe 30
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iya Bose ke mu su girki, amma tana kwana uku da zuwa ta fara shiga kitchen tana taya Iya Bose sarrafa abinci duk da kuwa Iya Bosen ba ƙarya ta iya girki sosai. A wajen ta ta san favourite na mijinta ta kuma koyi yadda ake sarrafa su. Shi ba bayarabe ba amma yana son cin amala da sakwara, dan haka ta dage tana koyon su a wajen Iya Bose. Miya kam ta ga ikon Allah, domin ita dai a gidan su idan ba kuka, kuɓewa, ko alayyaho ba to ba wani special miya da ake yi. Akan yi miyar egusi wani lokacin saboda Baffa na so amma a wajen Iya Bose sai ta ga miyar egusin ma ba kala ɗaya ba ce. Haka ta dinga ɗaukan darasin girki a wajen 'yar tsohuwar matar nan.
Daren Jumma'a da ya cika sati uku da auren su sai ga Aneesa ta zo.
Suna zaune su na kallo da yara a falo ta shigo, yaran suna ganinta su ka fara ihun mommy mommy.
A hankali Maijiddah ta fara satan kallon Aneesan duk da kuwa ta taɓa ganin hoton ta, amma ganinta a fili sai ta ga ta ƙara zama ma ta wata Madam. A ƙalla Aneesa za ta kai 36yrs ko 37yrs, amma jin daɗi da kuma samun mayuka ma su tsada sai ya ɓoye shekarun ta.
Sai da ta raba su Baby da Alizah a jikinta sannan ta kalli inda Maijiddah ke zaune sanye da doguwar riga ta atampa É—inkin ya amshi É—an jikinta É—as-É—as da ita.
Sai da Aneesa ta ƙare ma ta kallo sannan ta ja tsaki ta ce "ashe househelp Sweetheart ya kawo min"
"Sannu da zuwa" Maijiddah ta ce da ita.
"Nonye, Nonye" Aneesa ta fara ƙwalla sunan nannyn su Alizah.
Matar ta fito da sauri.
"Welcome ma"
"Je ki gyara min É—akin Seeetheart, na san by now it most be stinking of filth"
Nonye ta haura sama É—akin AbdulWahab. Dama ita ke gyarawa sai dai zuwan Maijiddan ne ta hanata ta ce ta dinga gyara É—akin yaran kawai da sauran wajen.
Kallon kirki Maijiddah ba ta samu daga wajen Aneesa ba. Aneesa ta haura sama don ta je ta shirya kafin AbdulWahab ya dawo.
Maijiddah kam sai duk jikinta yai sanyi. Tsoron Aneesan ne ya kamata ganin wannan kallo da ta ke ma ta. Ta na da ƙuruciya amma Aneesa ta fita wayewa da komai. Ba za ta iya haɗa kan ta da ita ba.
Ƙarfe tara saura sai ga AbdulWahab ya dawo daga office. Yaran su ka fara sanar da shi gameda zuwan Aneesa. Bai yi mamaki ba dan rabon sa da magana da ita tun ranan da aka ɗaura aurensa da Maijiddah.
Maijiddah ba ta yi yunkurin raka shi É—aki ba kamar yadda ta saba tunda Aneesa ta dawo.
ÆŠakin sa ya je ya cire kaya ya watsa ruwa sannan ya fito bayan ya sa kayan gida.
"Hauwerh yau na yi laifi ne ko ya hanya ba a min ba?"
Rasa mi za ta ce ma sa ta yi dan gaba É—aya zuwan Aneesa ya birkita ma ta lissafi.
Sai da ya zauna sannan ta fara serving na shi dama yara sun riga sun ci abinci, ita É—in ma saboda zuwan Aneesa ta ci abincin tareda yaran dan ba ta son hayaniya.
Da ta gama ta juya za ta tafi ya riƙe hannunta " gimbiya ta zauna"
Ba ta musa ba ta zauna amma hankalinta ba a kwance ya ke ba. Ƙanshin turarukan Aneesa shi ya sanar da su isowanta falon. Irin kayayyakin da Farida ta bata a matsayin gudunmawa, irin sa ke jikin Aneesa yanzu. Wata arniyan riga ce ta saka wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyar ta, rigan ba ta da hannu, rabin nonuwan ta a waje. Tana catwalking har ta iso wajen su.
Kai tsaye ta mannawa AbdulWahab kiss a kumatu tana faÉ—in " Sweetheart sannu da zuwa. Shine har ka fara cin abincin ban da ni"
Da ƙyar Maijiddah ta sauke wani wahallen numfashi sannan ta tashi ta bar wajen. Ashe rashin ganin Aneesa a kusa ne ya sa take ganin kaman ita ba ta da kishi.
Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta ja ƙofa ta sa key. Maimakon bacci ya ɗauketa kamar yadda ta so sai bacci ya ma ta ƙaura. Ta ga yadda idon AbdulWahab ya chanja lokacin da ya ga Aneesa, to irin wannan shiga ai ko ita da ta ke mace ma ta yaba. Sai dai anya ita Maijiddah za ta iya saka irin waɗannan kaya kamar yadda Farida ta yi ta ja ma ta kunne?...
...............
Satin da Farida ta ce za ta yi shi ta yi duk da kuwa Yakubu ya kira ya ce Sir Najeeb ya yi faɗa akan wanda su ka ƙara hutu. Ita kam ba damuwarta ba ne.
Ranan da ta resuming aiki Najeeb bai yi faɗa ba, kodan ta ga kamar hankalinsa na kan wani aiki da aka damƙawa kamfanin na su satin da ba ta nan. Sati biyu bayan sallah aka kawo sadakin Farida sannan aka sa rana uku ga watan december wanda yai dai-dai da wata uku ma su zuwa.
Farida ta so Baffa ya sa bikin irin wata biyar É—in nan, dan ta samu ta haÉ—a wasu kuÉ—aÉ—e wanda za ta yi hidiman biki da su.
Sai da aka tashi daga aiki ta shigo office É—in sa, lokacin ma shi duba wasu zane da aka submitting ma sa ya ke.
"Sir ga goron sa ranan aurena da akayi, na kawo ma"
Ɗago ido yai ya ga baƙar ledar da ta ajiye akan table.
Ƙura ma ta ido yai yana son gano wani abu a tattare da ita. She was excited as she talked to him.
"Sir idan ka ɗan ƙara haƙuri da ni, nan da wata uku zan bar aiki da kai"
Still bai ce komai ba
"Ka san anguwan da zan zauna É—an karan nisa ne da kamfanin nan, ga kuma aikin ku 8am-4pm. Ina matan aure kam ba zan iya ba"
Duk maganganunta ba wanda ya tanka a ciki a dole da ta ga ba shi da niyyan yin magana ta haƙura ta ce "Sir Najeeb tunda ko fatan alkhairi ba za ka min ba. Sai da safe" ta gyara zaman jakarta ta fita daga office ɗin.
Certainly Anas ya ce ma sa Farida is engaged tuntuni, amma shi bai É—auki abin serious ba. Tukunna ma wani mahaukacin za ta aura da zai iya zama da ita. Ya kalli ledar da ta ajiye ya ji wani takaici ya shigeshi. Haka kawai ya tashi ya É—au ledar ya je ya jefa a dustbin da ya gama ya shiga banÉ—aki ya wanke hannun sa. Da ya dawo ya zauna, ran sa ya riga ya dagule, aikin da ya ke son yi ma kasa yi yai dole sai tattarawa yai ya bar office É—in shima.
.........
Its like tunda Farida ta yi maganan sa ranan ta sai Najeeb ya rasa kan sa. Mafiya lokuta idan Farida ta zo sai ya ji wanni haushin ta fiye da da, haka nan kuma ba shi da abinda zai ma ta. A da tana É—an tsoron masifar sa amma yanzu kam kamar ma ta maida shi kakanta ne.
Yau ya dawo a gajiye ya tarar da Mom ta dawo. Kamar ko yaushe bai kulata ba, ita ne ta ma sa sannu da zuwa amma bai kula ta ba.
"Sabreen asked about you"
Tsayawa yai da tafiya ya juyo ya kalli mahaifiyar ta sa.
"Dont you dare, kar ki ƙara min maganar ta"
Juyawa yai ya wuce É—akin sa. Yana cikin banÉ—aki ya kunna shower ruwa na zubo ma sa ya fara tuno rayuwar sa da Sabreen.
Sabreen ta kasance 'yar uwar sa ce, Mahaifinta da Mahaifiyar sa cousins ne. Ita ɗaya ce a wajen iyayen ta kuma mahaifinta yana da mahaukacin kuɗi. Shekara uku ya bata amma tun suna raya su ka shaƙu, duk lokacin da su ka je hutu ƙasar Bahrain to su na tare. Ko lokacin da ya ke fama da matsalar rasuwan Aisha, Sabreen ta kasance macen da ya ke son kasancewa da ita a wannan lokacin. Duk da alaƙarsa da Mom ya ruguje hakan bai hana shaƙuwar sa da Sabreen ya lalace ba. Shaƙuwa ce tun da ga yarinta ta girma ta zama soyayya. Saboda Najeeb Sabreen ta dawo America da zama wanda ya zamo musabbabin komai.
Sabreen tana da kyau kuma tana ji da kan ta. Bayan ta yi karatu a Newyork Film Academy ta nuna sha'awarta na acting film maimakon directing da ta ce za ta yi da farko. Sun riga sun tsara yadda rayuwar su za ta kasance idan sun yi aure. Matsayin mai bada umurni da ta ce za ta zama, Najeeb bai da ja akan haka, kuma tun kafin a sa ranan auren su ta riga ta fara aiki da Hollywood inda ta zama assistant director a wani romantic film da yai tashe a lokacin.
Shirye-shiryen biki ake yi wanda iyayen biyu ke ta sake kuÉ—i kamar ba su san wahalan neman sa ba. Mom a wannan lokaci tana so ta yi abin gwaninta ko Najeeb zai yafe ma ta amma kash abu bai yiwu ba.
Saura sati biyu a ɗaura aure Najeeb ya koma Bahrain saboda anan za a fara hidima kafin daga baya a wuce Dubai daga Dubai kuma a wuce Italy sannan a ƙare hidiman a Singapore.