← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 91

Sashe 29

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"An dai ji kunya" ta faÉ—a sannan ta bar wajen. Da sauri Anas ya bi bayanta yana kiran sunan ta.
Ta shiga lifter amma kafin ƙofar ta rufe Anas yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga lifter ɗin shi ma.

"Najdah wai miya faru ne?"

"Dont pretend kamar ba ka san abinda ya faru ba. Sakatariyar Big B fa ka ke so. Sakatariyar sa"

A wannan dama da Allah ya bashi yau, dole ya cire tsoro kamar yadda Farida ta ce.
A hankali ya furta " to miye a ciki? Ita sakatariyar Najeeb ba mutum ba ce?"

Wannan karan kaman za ta yi kuka ta ce "Yaya yanzu duk faÉ—in garin nan ka rasa wanda za ka so sai ita, that cheap girl"

Ƙwarai ya gane kishi ta ke amma bashida 100% assurance cewa kishin sa ta ke, sai dai dole ne ya tabbatar wa kan sa domin shi ta ke kishin.

"Najdah wa ki ke so na so? Wa ki ke ga zai so É—an Maigadi"

"Yaya you know we love you, ka riga ka zama É—an uwan mu yanzu"

Matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya ya ce "so idan ɗan Maigadi ya nemi 'yar masu gida za ta amince?"

Jikinta yai sanyi haka nan kuma kusancin su da hannunta da ya riƙe ya sa ta fara jin wani baƙon yanayi ajikinta, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri.

Zuciyar sa ce ta ce 'Anas is now or never'

A hankali ya kai bakin sa dai-dai kunnenta ya ce "i love you Najdah, only you"

Maganar yai dai-dai da tsayuwar lifter dan haka ta wafce hannunta ta fita da gudu. Bai bita ba, sai ma murmushi da ya fara yi saboda jarumta da yai yau, finally he said it...

Farida na zuwa office É—in Najeeb ta tadda ya chanja kaya.

"Manyan mutane kenan, Allah ya ja zamanin ka CEO"

Fiskar nan ba fara'a ko kaÉ—an ya É—ago ya kalleta ya ce "your two weeks suspension starts now, Miss Salihu"

"Suspension"

Sai kuma ta yi shiru.

"Two weeks suspension is not all, bayan kin dawo za ki serving punishment na ki"

"Hutarere wallahi. Hutun sati biyu ai gaba ta kaini, ka ga zan fara azumi a gida kenan dan Jos zan wuce. Na gode Sir Najeeb Allah ya ƙara daraja"

"Leave" ya faɗi da ƙarfi

"Sir Najeeb ina da magana" ba ta jira ya ce komai ba ta ce "tsakani da Allah abinda ka yiwa Ya Anas bai dace ba, ka san yadda mutumin nan ke ganin girma da darajarka amma ka walaƙantashi. Irin walaƙancin kun nan na ma su kuɗi ya sa ya kasa furtawa ƙanwar ka kalmar so, kaima kuma da ke ba ka damu da shi ba, sai ba ka gano son da ya ke yiwa ƙanwar ka ba"

ÆŠago ido yai yana mamakin maganganun ta.

"A rage girman kai Sir Najeeb. Shi girman kai rawanin tsiya ne"...

Bai san lokacin da ta fita daga office ɗin ba saboda ƙwaƙwalwarsa da ta tafi duniyar tunani.

Anas na son Najdah, how when,why?. Kenan ba Aysherh ya ke so ba?

Da sauri ya miƙe ya bar office ɗin...

Wasu takardu Anas ke dubawa lokacin da Najeeb ya shigo, da ka gan shi ka san yana cikin farin ciki.

"You love my sister?" Ya tambayeshi lokacin da ya shigo.

"Najeeb..."

"Idan har kana son Najdah, why Miss Salihu again"

Dariya yai ya ce "tsaya Najeeb, waya gaya ma ka akwai abu tsakanina da Farida? I love your sister, ita kaÉ—ai na ke so"

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja sannan ya bar office ɗin.

Nan zuciyar Anas ta É—auko kan zan cen.

"Najeeb kishi ya ke da ni. Haba, dole biri yai kama da mutum ai. I suspected this tuntuni, Najeeb is inlove"

Murmushi ya biyo bayan maganar da yai wa kan sa, duk wani abinda Najeeb É—in ya ma sa sai ya ga ya washe ko kaÉ—an baya jin haushin sa. The fact that Najeeb has feelings for someone else bayan Sabreen ai abun farin ciki ne. After 8yrs of loneliness.

Cikin kwana biyun nan abubuwa sun chanja. Najeeb ya koma yana jin kunyar Anas saboda abinda ya ma sa duk da kuwa Anas É—in ya nuna komai ya wuce. Shi kan sa Najeeb ba zai iya faÉ—an dalili É—aya da ya sa yai ma sa haka ba domin haushinsa ya ke for no reason amma kuma yanzu ya washe.

"Yau zan fara zuwa hira officially, sirikina ka gaya min tips wanni irin kaya Najdah ta fiso namiji ya sa"
Najeeb ya dundeshi ya ce "É—an iska, ta fi son gwanjo"
Kalmar gwanjo da ya faÉ—i ya sa sunan Aysherh ya zo ma sa, kwana uku kenan da ba ta nan.

" abokina dan Allah kar ka manta a shigemin gaba wajen Daddy"

"Fuck you, Daddyn ne sai ni ne zan ma sa magana, kai ma ai É—an sa ne you can talk to him about it"

"Ni ba marar kunya bane irinka ai"...

Anas na fita daga office É—in sa ya tura wa Farida text akan an janye suspension É—in ta resuming aiki gobe. Lokacin da text É—in ya shigo Farida na bacci so ba ta gani ba.

Shigowar Khalidah office É—in ne ya sa shi deleting É—in text É—in da ya ke shirin tura wa Farida ta É—aya layinsa.

"Kwana na biyu da dawowa banga sakatariyar ka 'yar gold ba. Ko ka koreta ne?"

" get out"

"Maida wuƙar Najeeb. Na zo maganar project da ake yi a Kaduna ne"

Ya nuna ma ta kujera akan ta zauna...

Farida na ganin text É—in Najeeb ta yi tsaki ta tura ma sa reply kamar haka

*Sir Najeeb ni ba zan dawo ba sai sati biyu sun cika, kana gani za a fara azumi nanda kwana biyu ka ce na dawo, gaskiya sorry*

Lokacin da ya gama karanta text ɗin yai ƙaramar tsaki.

...................

Sati biyun dai ba ta yi shi ba, sati É—aya ta yi ta dawo saboda yadda Anas da Yakubu su ka takura akan ta dawo.
Duk da an rage awa É—aya cikin lokacin aiki, hakan bai sa ta jin haushin aikin ba yanzu saboda watan azumi da aka shiga.
8-3pm ba wasa ba ne a wajen Farida ga ɗan karen zafi da ake yi a garin na Kano, ga ruwan sama ma dai har lokacin da azumi ya kai goma ba wani alamunsa sosai dan sau ɗaya aka yi ruwa. Daga ƙarfe shabiyu za ka ga Farida ta yi laushi. Da ƙyar ta ke kaiwa lokacin tashi.

Yau ma wani aikin da za ta yi Najeeb ke ma ta bayani.
Burping ta fara yi akai akai har sai da Najeeb ya fusata ya ce " Miss Salihu will stop sounding like a frog"

(Burping kaman ƙwanafi kenan, ban san Hausa word na shi ba. Irin dai abinda ma su ulcer su ke yi ɗin nan ko kuma idan mutum ya cika cikinsa da abinci dayawa za ka ga daga maƙoƙoron ka kana fitar da sautin irgh irgh irgh )

"Sir Najeeb ba fa da gangan na ke ba, ulcer na ne ya tashi..." ba ta ƙare maganan ba ta kuma yi ya ce "Gosh! Miss Salihu get out"

Ba ta musa ba ta fita dan dama a gajiye ta ke...

Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga office ɗin sa sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci in his office a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali and there he sees her. Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da macaroni.

"Since when did my office become your dining room?"

ÆŠago ido ta yi ta kalleshi hannunta É—auke da sokali totse da abinci.

"Ni ban É—auka za ka dawo yanzu ba"

"Miss Salihu"

"Dan Allah Sir Najeeb ka barni, ka ga office ɗina kowa na shigowa ƙarangatsau, na ka office ɗin akwai privacy"

Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan ya ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan ba amma ita ya san zuwa anjima kaɗan za ta take shi.

Wata rana ana azumi goman ƙarshe, ranan anyi tsananin rana. Ƙarfe biyun rana sun je wani site Farida tana tsaye tana jin maganganun su har ta koma ba ta jin komai sai yijib ta faɗi ta suma. Najeeb da mutanen da ke wajen su ka yi kan ta.
Wanni Emmanuel na shirin kai hannu zai taɓa ta Najeeb ya daka mi shi tsawa "dont touch her"....

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣1️⃣7️⃣

Bayan ta farfaÉ—o ya sa aka kawo ma ta ruwa, maltina da madara akan ta karya azumi.

"Kai za ka biyamin ai idan na karya" abinda ta faɗa kenan lokacin da ya miƙa ma ta maltinan.

Ranan daga wajen ma ya maida ita gida ba tareda sun koma kamfani ba.

Haka dai a dararance ta cigaba da azumi har aka ƙare. Ana gobe Sallah aka ba su hutun kwana uku akan rana ta ukun sallah za a dawo. Farida kam cewa ta yi ba ta san zance ba sati ɗaya za ta yi. Ta wuce Jos ta yi sallan ta achan, duk da Kano za ta ga hawan sallah amma wannan baya gaban ta ta fiso ta ji ta jikin Umminta. Ƙila ma daga wannan sallah ita da sallah a Jos sai ta Allah.

.................

Lagos

Sati uku Maijiddah da angonta su na kwasan amarci, ba ta da matsala dan yaransa ba ma su hayaniya sosai bane.
Chapter 29 · 0% Book details