Sashe 78
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"I'm sorry" Farida ta faÉ—a cike da tausayin shi.
"No dont be. Allah ba ya taɓa ɗaurawa bawa jarrabawar da ta fi ƙarfin sa"
Farida ta ce hakane.
"Amma ba ka sake nema ba ne ko ya?"
Lukman ya nisa ya fara ba ta labarin yadda yai sanadin musuluntar da wata colleage na shi Dr Jennifer, har sun tsara za su yi aure ta amince da shi duk da ya gaya ma ta matsayin shi. Ƙwatsam wani abokin aikin su wanda ya ke da mata biyu fa Dr Faisal ya shiga nemanta yai ta hure ma ta kunne da ma ta burga da asalin sa yana kushe Lukman a matsayin sa na shege. Ƙarshe dai Dr Faisal ta aura.
"Kai duniya, yanzu musulmi É—an uwan musulmi amma sai ya ha'inci É—an uwan sa. Shi da ke da mata biyu amma ba su ishe shi ba sai sun hanaka samun mata?"
Lukman yai dariya mai ciwo ya ce " mi za ta yi da shege bayan ga cikakken namiji mai asali"
Jikin Farida yai sanyi. Yadda ta tsara anya zai yadda da shawaranta kuwa? Dama so ta ke ta ma sa maganar Sabreen. Sabreen tana buƙatar aure sannan tana buƙatar auren mai addini wanda zai kula da ita. To kuma Lukman shi ne candidate ɗin da ta ke ganin ya dace ya auri Sabreen dan ya ƙara gyara ma ta rayuwar ta...
Shigar Dr Lukman office ɗin Farida ya sa Naomi ta sa do not disturb tag a jikin ƙofa tana addu'ar Allah ya sa Najeeb ya dawo da wuri.
Tana zaune kuwa sai ga Najeeb, as usual ko kallon ta bai yi ba ya zo zai shige office sai ya ga tag É—in da ta sa.
Ya juyo a fusace yana tambayar dalilin saka tag É—in.
"Sorry Sir, Madam ce ta ce na sa dan ta yi baƙo. Tun tafiyar ka su ke tare"
Najeeb bai kawo komai a ransa ba ya buÉ—e office ya shiga. Ta glass É—in da ya raba office É—in sa dana Farida ya hango Farida da Lukman su na zaune. Zahiri ba wai su na wani abu ba ne. Magana ce su ke yi amma fiskan Farida É—auke da murmushi.
SheÉ—an ne ya tunzura shi a wannan lokaci. Har zai buÉ—e office É—in ya shiga sai kuma ya juya ya fita, Kan sa ke wani irin ciwo. Idon sa ya yi ja zir.
Yana fitowa ransa a ɓace zai tafi Naomi ta kira shi.
"Sir"
Ya juyo a fusace ya kalleta. Naomi ta fara ƙyafƙyafta ido, ta taso ta zo gaban shi har lokacin bai iya janye idon sa daga na ta ba. "dear ka yi haƙuri. Ka kwantar da hankalin ka, ina tareda kai"...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0ï¸âƒ£5ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Naomi ta sa hannu ta fara shafa ƙirjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daɗi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.
"Sweetheart ka yi haƙuri ka ji"
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaÉ—a ma ta kai...
Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada yaƙinin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.
"Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa"
Ta É—au waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an É—auka ba.
Duk da gabanta ya faÉ—i da hakan amma ba ta nuna ba.
Ta yi murmushi ta ce "ƙila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu ɗan hira shi"
Lukman ya miƙe tsaye ya ce "Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni"
"Insha Allahu wannan karan za a dace"
A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.
Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haɗu ta ko'ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a ɓangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye...
Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu É—aya ya É—auka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
"Gida kuma?" Farida ta faÉ—a cikin rashin fahimta.
"Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida" ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai É—auka ba.
Jakarta ta É—auka ta fito.
"Ma, za ki fita ne?" Naomi ta faÉ—a tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo ta ce "Naomi miji na ya zo ne?"
Naomi ta yi saurin cewa "No ma"
Farida ta fita cike da tunani a ranta...
............................
Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa É—auka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga É—aki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Duƙawa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ƙarasa dai-dai kan sa tana faɗin " miji na lafiya? Are you Ok?"
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya ɓaci ko kuma he's stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba ɗaya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai ɓata ma sa rai.
"My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya ɓata maka rai?"
" ba na son surutu" ya faÉ—a a hankali
"Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daÉ—in baccin"
Mirginawa yai ɗaya ɓangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.
ÆŠakin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki...
Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Baƙin riga da wando ya sa sai ya ɗaura farin blazer a kai.
"My Champ fita za ka yi ne?"
"My Champ...My Champ" ta cigaba da kira har lokacin da ƙofar ta rufu. Baki tasake tana bin ƙofar da kallo. Ya kalleta sun ma haɗa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.
Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ƙarfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.
Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.
"My Champ, My Champ" da sauri ya dinga taka stairs ɗin har ya ƙule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ƙarfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taɓa wuce ƙarfe tara a waje ba...
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banɗaki lokacin da ta shigo. Itama banɗakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka ko za su shirya daga nan amma ta ji banɗakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banɗaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah ɗakinta na ƙasa.
Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai É—an shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a ɗakin ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce "My Champion dan Allah ka yi haƙuri, idan ma wani laifin na maka ka yi haƙuri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina" tana maganan ne kaman za ta yi kuka
"Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma É—akin ki"
Kan ta ya ɗaure. Najeeb ba zai taɓa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar ɗakin.
"Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba"
tsaki yai ya tashi ya É—au pillow ya koma kan kujera ya kwanta.