← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 91

Sashe 27

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama duk girman kan Sir Najeeb ya taɓa soyayya? Abun mamaki"

"Kar ki damu da abinda ki ka ga ya yi ɗazu, anjima kaɗan za ki ga ya zo ba da haƙuri"

"Duk da haka Ya Anas, abinda yai bai ma ka adalci ba wallahi"

"Kar ki damu, abinda yai bai kai zuciyar sa ba"

"Wannan sirikin na ka Allah kaÉ—ai ya san yanayin sa. Yau ka gan shi shiru anjima ya fara faÉ—a gobe idan ya fara banbamin bala'i har wani spark bakin sa ya ke yi"

Ai Anas bai san sanda ya fara dariya ba "kai Farida kinada abin dariya ba kaÉ—an ba"

"Allah Ya Anas wani lokacin kaman majnuni ya ke, ka san lokacin da aka kidnapping É—in mu haka mu ka kwana mu ka wuni bai min magana ba daga baya kuma bini-bini sai ya É—aukeni"

"To waya sani ko ke ce ke sa shi haukan"

"Ni Aisha Farida! Rufa min asiri kafin yanzu na ga query letter"

Ta É—an gyara zama ta ce " yawwa, da ma maganar Najdah zan ma ka"

Ya É—ago ya kalleta

"Mi zai hana ka faÉ—a ma ta kana son ta, you never know, sai ka ga an dace. Balle ni ina ganin tana son ka ma"

"Baba na gadi yai a gidan su har ya rasu, karamci na Daddy ne ya sa ya sponsoring karatuna tun daga primary har masters da na yi shi ya sa na zama abinda na zama a yau. Daddy is like my father amma kuma na san indai akan maganar Mustafah ne to zai zaɓeshi ya bar ni, domin Mustafah jinin sa ne"

" tsoro shi zai sa ka rasa masoyiyar ka wallahi. Ba ka taɓa ce ma ta kana son ta ba, ba ka gayawa Najeeb ba balle kuma Daddy, to dan Allah ta ya za su san kana yi balle har a dubi wanne ya fi dacewa da ita tsakanin kai da Mustafah"

"Ki bari kawai Farida. Gara na zauna a matsayina"

"Dan Allah kar ka bani kunya ma na"...

...........

Lokacin da aka dawo daga break ta koma office ɗin ta. Ko da aka zo neman Najeeb ta kira office ɗin sa amma bai ansa ba, ta shiga office ɗin amma baya nan. Har banɗaki sai ta leƙa amma shiru. Numbar sa ta fara kira amma ba ta shiga.
Daga ƙarshe dai ranan har aka tashi ba ta ga Najeeb ba. Haka nan ba ta san inda ya je ba dan da ta fita ƙasa ta tambayi security aka ce ma ta Najeeb ya fita da mota tuntuni.
A zuciyarta ta ce "ai dole ka gudu tunda ka yi abin kunya"...

Tunda ya bar canteen kai tsaye motar sa ya je ya É—auka ya bar kamfanin, ya na shiga gida É—akin sa direct ya wuce ya samu gefen gado ya zauna tare da dafa goshin sa. He cant believe wai shi ne yai wa Anas tsawa. Anas fa, Anas da duk faÉ—in duniyan nan ba shi da aboki kamar sa. Saboda me?
Shi kan sa bai san dalili ba, ya san ba laifin Anas a zaman da Farida ta yi a wajensa. Sai dai ya rasa dalilin da ya sa maimakon ma ya ji haushin Farida sai ya kasance ya fi jin haushin Anas akan ta. Bai san ya za'a yi ya dena jin haushi ba duk lokacin da Farida ta ke tareda Anas.
Ya jima yana tunani a ran sa kafin ya tashi ya fara cire kaya dan ya watsa ruwa.

...............

Samun Anas ta yi akan dan Allah ya kaita gidan su Najeeb ta bashi wa su takardu sannan ta bashi saƙonnin wanda su ka zo ba su sameshi ba tunda wayar sa a kashe ya ke. Yana sauketa a compound ɗin su ya juya ya tafi dan shima bai shirya fuskantar Najeeb ɗin ba, ko da kaɗan ne to ya ji haushin abinda Najeeb yai.

Ranan da su ka zo gidan da dare ba ta lura da gidan ba, saboda dare da kuma hali na gajiya da rashin lafiya. Amma yanzu kam ta ga yadda gidan ya ke da girma da kyau, sai da ta gama yabon kyaun gidan a zuciyar ta kafin ta wuce ciki. Doorbell ta danna tana jira a buÉ—e.

Najdah da Afrah ke cin abinci a dining saboda har yanzu Mom ba ta dawo daga Bahrain ba.

"Adama.... Adama ki zo ki buɗe ƙofa"

Adama ta fito da sauri ta nufi ƙofan.

"Sannu, wa ki ke nema?" Adama ta tambayi Farida da ke tsaye a bakin ƙofa.

"Ni sakatariyar Najeeb ne, na kawo ma sa saƙo yana nan?"

" ki shigo"
Ta matsa ma ta ta shiga.

"Adama waye?"

Kafin ta bada amsa Farida ta ce "Aisha Farida ce"

Sunan ba baƙon suna ba ne a wajen su duka biyun, dan sun san labarinta a Najeeb constructions. Ranan da su ka fara zuwa wajen Najeeb farko-farkon fara aikin Farida. Hana su shiga office ɗin sa ta yi ta sa su ka jira shi a office ɗin ta har sai da ya dawo. Ranan cikin shagwaɓa Najdah ta dinga complain wa Najeeb har da cewa "Big B, your secretary was rude to us". Daga baya Najeeb ya ce wa Farida duk lokacin da ƙanwar sa ta zo yana nan ko baya nan ka da ta hana ta shiga office ɗin sa.

"Ehen, duk haÉ—uwar ku na office bai isa ba sai kin biyoshi gida" Afrah ta faÉ—a tana huhhura hanci.

"Idan aiki na ya tsone mi ki ido, kya iya zuwa ki ƙarɓa"

"Mtsww" Afrah ta ja tsaki

"Mi ki ka zo yi?" Najdah ta faÉ—a ita É—in ma fiskan ba yabo ba fallasa.

"Na kawo wa Sir Najeeb wa su files ne, sannan na zo neman bayanai gameda masoyina Anas kasancewa kin fini sanin shi"

"Masoyin ki Anas?" Najdah ta maimaita

"Wanni Anas tukunna?" Afrah ta saka baki.

"Abokin yayanki ma na, ko kin san wani Anas É—in bayan shi?"

Najdah ba ta ce komai ba sai haurawa da ta yi sama da gudu fuuuu itama Afran ta bi bayanta tana kiran ta.

Ganin su duka biyun sun bar wajen ya sa Adama ta je wajen SHS É—in falon ta danna 6 muryarta na rawa ta ce "Ranka shi daÉ—e ga Sakatariyar ka ta zo neman ka"

Shiru kusan minti É—aya ba a ce komai ba, har Adama ta fidda rai sai ga muryar sa ya na cewa " send her to my room"

"Ina ne É—akin?" Farida ta tambaya

"Idan kin haura sama shine ɗaki na ƙarshe a ɓangaren hagu"

Ok kawai ta ce ta haura saman. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta yi lokacin da ta iso. Ta tsaya na aƙalla minti biyu kafin aka buɗe ƙofar.

Sanye ya ke da jallabiya na 'yan Morocco kalar toka.

"What do you want?" Ya faÉ—i fiskar sa tamau.

"Ya Allah, wai haka gidan ma su kuÉ—i su ke ne, daga ka zo sai a fara tambayarka mi ka zo yi. To ni ba maula na zo yi ba ziyara na kawo"

Ƙofar ya jawo zai rufe ta yi saurin sa hannu ta ce " yi haƙuri Sir Najeeb saƙo na kawo"

Ya dakata da rufe ƙofar yana kallonta. Ta fito da wani file ta miƙa ma sa sannan ta ce " Sir MD na Hafzal suites ya zo neman ka ya ce da ka ji saƙon nan ka kira shi akwai magana mai muhimmanci da za ku yi sannan dan Allah ka bawa Ya Anas haƙuri abinda ka..." baam ya rufe ƙofar sa.

" Mr Egocentric" ta faÉ—a kafin ta juya ta fita.

A falo ta haɗu da Daddy shi ma ya shigo gidan kenan, har ƙasa ta rusunna ta gaida shi.

"Kaman na san fiskar nan"

"Yallaɓai ai ni ce sakatariyar Sir Najeeb wanda aka sace mu kwanaki"

"Oh Aisha ko?"

"E"

"Sannu ya Baban na ki"

"Ya na lafiya"

"Ki gaida min shi ko"

"Insha Allah zai ji"

"Gida za ki je ne?"

Ta amsa da E

"To to, Adama ki fita ki ce Iliya ya kaita gida ko"

"Na gode Daddy"

Ya fito da kuɗi a Aljihu ba tareda ya irga ba ya miƙa ma ta ya ce ta sha ruwa a hanya.

"Daddy ka barshi na gode"

"Idan ki ka yi haka ba ki É—auke ni Daddy ba kenan"

Ai tuni Farida ta karɓa tana ƙara faɗaɗa murmushinta lokacin da ta ji kaurin kuɗin zai iya kaiwa dubu goma.

Ita kam bajau É—in ta, ta tafi gida a mota mai kyau ga AC ga dubu takwas da Daddy ya bata...

Ai ba ta gama zama ba Anas ya kira ta.

" 'yar uwa mi ki ka faɗawa Najdah ne? Ta kira ni wai muna soyayya da ke kuma na ɓoye ma ta bla bla bla..."

Sai da Farida ta yi dariya mai isar ta sannan ta ce " Yaya na kenan, idan akwai kishi to akwai so. Najdah na son ka, ka saurari plan É—ina ka ji..."

............

Su na cin breakfast a dining Najdah ta ce " Big B wai ashe Ya Anas da sakatariyar ka soyayya su ke"

Tea É—in da Najeeb ya kai baki ya furzar da sauri.

"Anas ya gaya mi ki?"

"Jiya da sakatariyar ka ta zo ta ke gaya min. Big B, Ya Anas ya rasa wanda zai nema sai masifaffiyar yarinyar nan, that girl fa ba za ta rasa mu'amala da ƙwaya ba"

Miƙewa Najeeb yai bai ce komai ba ya bar dining ɗin.

Ranan da Anas da Farida ban san wanda ya fi shan masifar Najeeb ba. Abu kaɗan masifa, lokaci guda Najeeb ya dawo wa Farida Najeeb ɗin da ta sani farkon zuwan ta. " get out, fuct you, stupid, nonsense" waɗannan kalmomi da su na tsiro da sun tsiro a jikin Farida saboda tsabar yadda ta ji su a wajen Najeeb. Idan ta kawo takarda ya signing kuwa yana gamawa zai wurgeta da shi ba zai miƙa ma ta da hannu kamar yadda ya saba ba.

Anas ma ya ɗauka da Najeeb ya zo zai ba shi haƙuri a wuce wajen sai ya ga saɓanin haka. Yana tambayar sa abu maimakon yai magana sai ya fara ma sa tsawa...
Chapter 27 · 0% Book details