Sashe 41
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Anty kuma, ai sai ki sa na ji kunya. Ki kira ni Aisha ko Farida"
"Anty Farida dai"
Farida ta sa dariya.
"Dama na ce daga yanzu ba sai kina gyara É—akin mu ba, zan dinga gyarawa"
"Na gode" Adama ta faÉ—a tana murmushi.
Da rana tareda Adaman su ka yi girkin rana, su na aikin tana ma ta tambayoyi gameda gidan. Su biyu ne ma su aikin ita da Tasallah. Tasallah kuma ta je gida an mu su rasuwa. Ita Adama matar Iliya dreba ne ita kuma Tasallah bazawara ce wanda aƙalla za ta kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar.
Da su ka gama ta haura sama ta duba wayar ta ta ga miss call ɗin Maijiddah da text ɗin ta, inda ta ke sanar da ita ta isa gida lafiya. Kiran Maijiddan ta yi amma ba ta ɗauka ba sai ta kira Ummi. Sosai su ka yi hira da Ummin wanda ta ke ta ƙara ma ta nasiha akan haƙuri...
Ƙarfe uku saura Mom ta dawo, bayan ta kimtsa ta ci abinci ta sa Adama ta kira ma ta Farida.
Farida na bacci ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa kamar daga sama, ta tashi da ƙyar ta zo ta buɗe.
"Anty Farida Hajia na kiran ki"
"Ok tana ina? Tana falon sama"
"Ina zuwa"
Sai da ta wanke fiskarta sannan ta fito.
A É—an kishingiÉ—e ta sameta kan kujera ta yi nisa cikin tunani.
Farida ta É—an yi gyaran murya ta ce " Mom barka da yamma"
Mom ta ɗago kai ta kalleta tareda ƙaƙaro murmushi.
"Sannu da zuwa Aisha"
Sai da Farida ta gyara zama sosai sannan ta ce "you're lucky Aisha, Kin san, Najeeb yana son sunan Aisha sosai"
"Ayya! Amma bai taɓa kirana da shi ba kuwa"
"He likes you. Na san bai gane hakan ba amma nan gaba zai gane"
Farida dai shiru ta yi tana sauraron wannan mata wadda ta ke uwar miji gareta.
Mom ta ɗauki wanni takarda da ke gefen ta ta miƙawa Farida ta ce " na rubuta mi ki abubuwan da ya ke so da wanda ba ya so. Zai taimaka mi ki wajen ganin kun fahimci juna da wuri"
"Na gode Mom"
Ta miƙa ma ta wani ƙaramin jewelry box ta ce "wannan kyauta ne da na ke son bawa duk matar da Najeeb ya aura"
Farida ta ƙarɓi box ɗin tana godiya.
"Open it"
Tana buɗewa ta ga sarƙa ce ta dimond sai walwali ya ke.
"Its pure dimond" Mom ta faɗa tana kallon yadda Farida ke kallon sarƙan
"Mom na gode, Allah ya saka da alkhairi. Haƙiƙa banida ma bakin godiya, this is too much Mom"
"Ba komai, just make him happy"
"Insha Allah zan yi ƙoƙari Mom"...
Farida na shiga ɗaki ta ɗau sarƙan nan ta gwada sawa a wuyan ta, tana duba kan ta a madubi. Wannan duk taron da ta je ta sa ka shi sai ta zama topic of the day. Tana cikin dubawa sai kuma ta ji jikinta yai sanyi tunowa da ta yi wanda aka bata sarƙan domin sa ba wai ya damu da ita ba ne.
Ta maida sarƙan inda ya ke sannan ta ɗauko takardan da Mom ta ba ta, ta fara karantawa.
- ya fi son kala baƙi
- ya na son cin fruits (musamman apple, inabi da lemu)
- ya na son coffee
- ya na son ƙanshi
- ba ya son wari
- ba ya son ƙazanta
- ba ya son hayaniya
- ba ya cin doya
- ya fi son kifi akan nama
- ba ya son jan abu....
Wayar ta da ya fara ringing ne ya sa ta tsaya da karantawa. Ta É—auko wayan sai ta ga Rayyan ke kiran ta. Har wayan ta katse ba ta É—auka ba.
"Mi kuma zai ce min" ta faÉ—a a fili yayinda kiran sa ya sake shigowa. Sai a kira na uku ta É—auka.
"Rayyan lafiya ka ke kirana?"
Daga ɓangaren Rayyan ya ce "My Farida ban san ya zan yi ba, yanzu na ke jin wai hotunan nan haɗa su aka yi, wai Alhaji Jibo ya zo ya samu Baba ya nemi a maida zancen auren mu. I'm sorry dear, ki bani lokaci mu zauna mu yi magana"
"A ina za mu zauna? A saman kwano ko a saman bishiyan mangoro. Look Rayyan, kar ka ƙara kira na, ni matar aure ce"
Ta na kashe wayar ta cillata kan gado ta cigaba da karanta takardar da Mom ta ba ta.
...........................
Kusan ƙarfe biyar wa su baƙi su ka zo Adama ta zo ta kirata ta sauko ƙasa. Su biyu ne, ɗaya ta ganeta domin jiya ta zo, ƙanwar Daddy ce da su ke kira Hajia Fatima. Ɗayar kuma ba ta san ta ba.
Sai da su ka gaisa Hajia Fatima ta gaya ma ta sun zo ƙarɓan sizes ɗin ta ne saboda lefe da za'a haɗa ma ta.
Hajia Salma da su ka zo tare wadda ta ke amaryar Uncle Sulaiman ne ta É—auko Tab É—in ta ta na rubuta sizes É—in, tundaga na inner wears zuwa general measurement na ta.
Bayan sun gama aka buge da taÉ—i, su na haka sai ga Najeeb ya shigo.
"Yawwa ango dama kai mu ke jira"
"Ni kuma?"
"Yes, mun zo karɓan kuɗin haɗa lefe"
"What's that?"
"Ɗan iska, dan ka yi ƙwacen mata sai ba za ka ma ta kayan lefe ba. To ba zai yiwu ba"
Hajia Salma ta ce " Najeeb bar Hajia Faty da tsokala. Check za ka rubuta ma na za mu haÉ—awa Farida kayan lefe"
Sai da yai kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "how much?"
Hajia Fatima ta ma sa daƙuwa ta ce " ungo na ka da how much ɗin, blank check za ka bamu"
"Hell no, there's no way i'm giving you a blank check. Ki samu daman zuba jari a shagunan ki ko?
"Zan ci ƙaniyar ka Najeeb"
Najeeb ya zauna ya ciro check book na shi ya fara cikatawa Hajia Salma da Hajia Faty idon su ƙyam akan abinda ya ke rubutawa.
Hajia Fatima ta ce "Allah ya sawwaƙa Najeeb, mi wannan zai yi? Ka san ina da ina zamuje kuwa? Kai ka na sa kaya designer ba ka so matar ka ta sa designer ne?"
Farida kam dai kallon su ta ke yi dan ba ta ga nawa ya rubuta ba. Ƙarshe dai dole blank check ɗin ya ba su...
Yana shiga É—aki ya ji wayar Farida da ke kan gado yana ringing haka kawai sai ya tsinci kan sa da É—aukar wayan wanda kafin ta yanke ya ga sunan nan dai da ke tada ma sa hankali *My Ray* tsaki yai ya maida wayar ya ajiye.
Ya na cire kaya amma sai tsaki ya ke shi kaÉ—ai.
Lokacin da ta shigo yana kan gado, ya kunna TV da ke É—akin yana kallon tashar Aljazeera.
"Sannu da dawowa, ya aiki"
" your Ray ya kira ki"
Dam ta ji gaban ta ya buga. Ita wallahi ta manta ba ta goge numbar bane É—azu.
"Sir Najeeb ba wai abinda ka ke tunani ba ne, Allah mantawa na yi ban goge numbar ba"
Bai ce komai ba sai ma remote da ya É—auka ya fara chanja tasha.
Ganin yai shiru ta ce " Sir Najeeb ka yiwa Mom godiya ta min kyautar girma. She gave me a dimond necklace"
"Mrs Jibo" ya faÉ—a da sigar jan hankali.
"Kar ki ƙara yi min maganar matar nan"
Farida ta zaro ido "mahaifiyar ta kan"
"Idan ki na so mu zauna lafiya, to ki dena kawo min zancen ta"
" yau na shiga uku, Sir Najeeb...."
"Shhhhhhh"
Haɗiye maganar ta yi dan yadda ta ga ran sa ya ɓaci.
Zama ta yi a gefen gadon ta ce "Sir Najeeb zan yi aikin, amma sai ka amince za ka bani dama na wanke kai na daga zargin da ka ke min"
" good for you"
..........................
Zuwa yanzu ta gama gane yanayin gidan. Mom ba ta da matsala ko kaɗan hakan ya sa ta rasa gane dalilin da zai sa Najeeb ya dinga ma ta abinda ya ke yi. Najdah kam ƙiri da ƙiri ta ke nuna ba ta son ta. Ita kam ko ajikin ta, dan ba wannan ba ne a gaban ta.
Ranar asabat da ta cika sati É—aya 'yan gidan su su ka zo ma ta gaisuwa. Ta ji daÉ—i sosai kuma ta karrama su, gayya guda su ka zo dan duka matan Baffa Musa ne su ka zo da yaran su kusan su goma. Da za su tafi ta haÉ—a mu su tsaraba...
Anas tun ranan da Najeeb ya ma sa zancen zai dawo da Farida aikin t, ya kira yana ma ta faÉ—a akan miya sa za ta amince da haka, ta nuna ma sa ba komai ita ke son komawa aikin...
"Sir Najeeb wai haihuwa ka ke a banɗakin ne? Tun ɗazu fa" ta cigaba da ƙwanƙwasa banɗakin.
Haƙura ta yi ta je ta zauna tana jiran sa, dama fitsari ne ya matseta.
Yana fitowa ta tashi da sauri ta shiga banÉ—akin.
Tunanin ko lafiyarta lau ya ke. If she's really pressed mi ya sa ba za ta je guest room ba.
Lokacin da ta fito É—aure da towel ya riga ya shirya takalmi kawai ya ke sawa.
"Sir Najeeb ka jirani mu tafi tare dan Allah"
" i'm not your driver"
"Sir Najeeb ya ka ke so na yi, anguwar kun nan ba lallai mutum ya samu abin hawa da wuri ba"
"Akwai mota a gidan"
"Motan tuƙa kan ta za ta yi ne. Ni ban iya tuƙi ba"
Ya miƙe tsaye ya ce "good for you"
Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo ya ce "idan kin je office ki yi aikin ki kamar yadda ki ka saba, cause our relationship is strictly professional"
"Na ji Mr professional"
...........