← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 91

Sashe 37

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe aka tashi da shirye-shiryen walima. Farida ta kasa magana ta kasa faÉ—an abinda ya faru jiya, ita har lokacin gani ta ke mummunan mafarki ta yi jiya da dare.

Zuwa ƙarfe goma sai ga Baffa ya shigo yana faɗace-faɗace. Kiran Ummi da Nanna da Baaba Sabuwa yai zuwa falon sa. The next thing da akaji sai kukan Ummi. 'Yan gulma su ka yi falon da sauri Baffa musa ya fatattake su.

"Amina ki dena kuka, ni ban yarda da abin da su ka ce ba, kuma koma hakanne dole sai na aurar da 'ya ta gobe. Ba zai yiwu a fasa aurenta har sau biyu ba, sai duniya ta zageni. Ni nawa 'ya'yan ina aurar da su lafiya ita kuma da ta ke amana gareni ake samun matsala duk lokacin bikin ta"

Nanna da ita kaÉ—ai ce ba ta fara kuka ba ta ce "yanzu wa za ta aura?"

"Yakubu, Yakubu zai aureta, ku cigaba da shirye-shirye Allah ya kaimu goben"...

Farida na É—aki har lokacin tana zaune jugum, Maijiddah ta yi tambayar duniyar nan amma ba ta kulata ba.

Ummi ta shigo É—akin tana hawaye. Zuwa ta yi ta tsugunna gaban Farida ta ce "faÉ—a min gaskiya Farida, akwai abinda ke tsakanin ki da Ogan ki?"

Farida ta kalli Ummi da rinannun idanuwan ta ta ce "da gaske ne ko? Da gaske Rayyan ya fasa aurena?. Ummi banida sa'a a rayuwa kenan? Ummi ina son na yi aure, ina son na samu gidan kai na, ina so na haihu na tara 'ya'ya, ina so na samu ladan biyayyar aure, ina so na cika miki burin ki Ummi. Ummi ko dai aure ba ya cikin ƙaddara ta ne?"

Ummi ka sa magana ta yi sai kuka.....

Zuwa ƙarfe shabiyu 'yan gidan su Rayyan su ka zo karɓan kaya. Daga wajen ma su ke cewa aje a kwashe tarkacen da aka jera a gidan ɗan su. Abubuwa dai su ka rinchaɓe a wajen.

Kowa a gidan da abinda ke ran sa, wassu baƙin na shirin komawa amma da su ka ji Baaba Sabuwa ta ce aure ba fashi za ayi, sai su ka tsaya dan su ga ƙarshen Farida.

Farida tun safe ko sau É—aya ba ta fito a É—aki ba, ko wanka ba ta iya yi ba balle abinci kam ba a zancen sa.
Da yamma Yakubu ya dawo daga wajen aiki sai a lokacin ya ke jin labarin abinda ke faruwa. Baaba Sabuwa ce ta ma sa maganar auren Farida da ya koma kan sa. Duk da bai shirya aure yanzu ba sannan bai taɓa kawo auren Farida a ransa ba amma indai dan ya cececi mutuncin 'yar uwar sa ne to zai aureta da gudu ma. Abinda ya ƙara ɗaure ma sa kai baifi yadda aka ce wai 'yan gidan su Rayyan sun ce wai FARIDA karuwar Ogan ta ba ne. Ya san Farida kuma ya san Sir Najeeb, ko da dai chan ƙasar zuciyar sa yana zargin Sir Najeeb na son Farida amma bai kai har ace wai suna neman junan su ba.

Yana cikin wannan tunanin ya ji wayar sa na ringing. Yana dubawa ya ga Farida ai da sauri ga É—auki kiran.

"Dan Allah Yakubu ka sameni a ƙofar gida"

Da sauri ya tashi ya fita.
Lokacin da ya ganta wani tausayinta ne ya kuma shigan sa. Lokaci guda Farida ta chanja ta zama wata iri, fiskanta ya kumbura ga idon ta da su ka ƙanƙance saboda kuka. Tunowa yai da shekara uku da su ka wuce exactly haka ta lalace lokacin da aka raba aurenta da Lukman. Gara lokacin da sauƙi tunda matsalar daga Lukman ne to yanzu fa.

Ya ƙarasa wajenta yana faɗin "Farida dan Allah ki yi haƙuri, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce"

"Ka kaini gidan su Sir Najeeb" abinda ta faÉ—a kenan cikin muryarta da baya fitowa sosai saboda dashewa da yai...

Adama ce ta buɗe ƙofa lokacin da ta danna doorbell ɗin.
"Daddy na nan?"

"Eh ki shigo"

A tsaye ƙiƙam ta tsaya idon ta na kallon ƙasa, kan ta ke sarawa, duk yadda ta ɗaga kan sai ta ji wani raɗaɗi.

Mom ce ta fara saukowa ganin yadda Farida ta ke ya sa tasan yarinyar na cikin damuwa.

" 'yan mata ki zauna mana" ta faÉ—a da Hausanta da bai gama nuna ba.

Farida ba ta ce komai ba sannan ba ta zauna É—in ba. Kitchen Mom ta wuce ganin Farida ba ta cikin hayyacinta.

Minti huÉ—u sai ga Daddy ya sauko.

"Ina wuni Daddy" ta faÉ—a da disashshiyar muryarta.

"A'a Aisha Amarya?"

"Na'am Daddy"

"Lafiya dai ko?, shekaranjiya Baban ki ya kawo min katin biki, ina ce ba wata matsala ba ne ta taso ?"

"Daddy kai uba ne na gari amma É—an ka bai É—auko hali na gari ba. Najeeb ya min sharri, ya raba ni da farin ciki na. Ya sa min tabo a rayuwata wanda ban san ranan da wannan tabo zai gogu ba. Ni marainiya ce, ba ni da gatan da ya wuce Allah, kuma na haÉ—a Najeeb da Allah. A kamfanin sa ban tsira ba, na bar aiki da shi ma ban tsira ba. Allah zai saka min" ta fashe da kuka ta fice daga gidan da gudu. Daddy yana kiran ta amma ba ta tsaya ba. Daddy kan shi ya É—aure dan bai gane ina maganganun Farida su ka dosa ba.

Tana fitowa ta tsaya ta goge hawaye sannan ta fara tafiya duk da kuwa ba ta da ƙwari a jikinta. Ta kusa isowa wajen Yakubu da ke jiran ta jiri ya ɗebeta ta faɗi ta suma. Yakubu ya yiwo kan ta da gudu...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣2️⃣3️⃣

Maigadi da dreba da su ke zaune a benchi su ka taso da gudu.
Ce ma sa su ka yi ya kai ta mota yayinda Iliya dreba yai sauri ya shiga gidan don ya faÉ—awa Daddy.
Daddy na falo har lokacin yana waya da Anas.

Ya na ma sa bayani Daddy ya ce muje-muje.

Daddy na gaba Yakubu na baya É—auke da Farida wanda har lokacin ba ta farfaÉ—o ba duk da kuwa sun yayyafa ma ta ruwa. Kafin su isa asibitin ta farfaÉ—o amma ba ta san inda ta ke ba....

Chan gida kuma Baffa ne ya ke ta faÉ—a kan miyasa za'a bar Farida ta fita a wannan halin. Maijiddah ne ta ce tare su ka fita da Yakubu. Sai a sannan yai shiru ya zaro wayar sa a aljihu ya fara kiran numbar Yakubun amma bai É—auka ba.

"Shima É—an gatan'wa, ko ina ya shiga oho"...

Ruwa aka É—aura ma ta aka ma ta alluran bacci dan sun ce jinin ta ne ya hau. Sai da ta fara bacci tukunna Yakubu ya samu damar kiran gida ya faÉ—a mu su.

Daddy ya dubi Yakubu ya ce " mi ya ke faruwa ne? mi Najeeb ya ma ta?"

Da kaman ba zai faɗa ma sa ba,sai dai girman Daddy da kwarjininsa ya fi gaban ya ƙi ma sa magana. Duk abinda ake ciki ya tsirge mi shi tundaga farko har ƙarshe.

Da ya gama bashi labarin Daddy ya É—auko waya ya kira wata number.

"Anas ka na ina ne?"

Yakubu bai ji mi ake ciki ba ya dai ji ya ce "muna room 18 a sama"

Ba'a jima ba sai ga Anas ya shigo. Ganin Farida a kwance ya sa shi mamakin mi ya faru.

"Yakubu ya jikinta?, mi ya sameta?"

Da sauƙi kawai Yakubu ya iya ce masa.

"Ina É—an banzan nan ya ke?"

Daddy ya tambayi Anas.

Ya gane Najeeb ya ke nema dan haka yai saurin cewa yana office nima daga office É—in na ke.

"Har da kai ake rusa rayuwar mutane ko?"

Anas ya zaro ido ya ce "A'a Daddy"

Daddy ya miƙe ya ce "Yakubu Allah ya bata lafiya, ina nan dawowa anjima"

Yana Fita daga É—akin Anas ga bi bayanshi da sauri.
A motan Anas É—in su ka wuce Najeeb constructions.

Ya jima yana tunanin ko wani hali ta ke ciki. Wani ɓangare na zuciyar sa na faɗa ma sa bai kyauta ba wani ɓangaren na nuna ma sa ya yi dai-dai.
"She deserve it" ya furta a fili.
Yana ƙoƙarin duba wasu takardu da aka submitting ma sa tun da safe amma ya kasa fahimtar komai. Haka kawai zuciyar sa ke ma sa ƙunci....

A hanya Daddy ke sanar da Anas abinda Najeeb yai, Anas ya kaman salati yana salallami.

"Daddy ban san Najeeb zai iya yin haka ba especially saboda zargin da na ke masa akan yana son Faridan"

"Dan uban sa dan yana son ta sai ya mata sharri"

Anas dai shiru yai yayinda Daddy ke ta surfa ma sa masifa kaman wanda shi yai laifin.

Da ke an riga an tashi wajen shiru ka ke ji. Daddy da Anas su ka haura third floor.

Ya kifa kan sa akan kujera saboda wani zazzaɓi da ya rufeshi lokaci guda, ya rasa mi ya sa shi shiga wannan yanayi. He supposed to be happy ya rama kaɗan daga cikin asaran da Miss Salihu ta sa ya yi. But instead his sad.

Buɗe ƙofar office na shi da aka yi ya sa ya ɗago kan sa da sauri.
Ganin Daddy da Anas sai ya miƙe. "Dad " kaɗai ya iya faɗa kafin saukan mari ya sa ya haɗiye koma mi ya ke shirin faɗa.
A karo na biyu Daddy ya kuma marin sa, ji ka ke taas. Anas na gefe ya sha jinin jikin sa dan faÉ—an uba da É—a sai Allah.

"I'm ashamed to call you my son"

"Dad" Najeeb ya faÉ—a a hankali

"Ashe tarin shekarun ne kawai akan ka ba hankali. Mahaukacin banza Mahaumacin wofi. Sai ka samu me idan ka hanata auren? Tukunna ma, miye dalilin yi ma ta sharri? Miye dalili? "

"she deserve it Dad, she wanted to ruin me. Na rasa big contract saboda ita saboda haka 2 project da mu ka fara su ka soke contract da mu. She tarnished my image and the repeatition of my company"
Chapter 37 · 0% Book details