← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 91

Sashe 76

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu ba ka ji kunyar gaya ma sa ba?" Ta faɗa tana ƙoƙarin cire ma sa riga.

Dariya yai ya ce "wani kunya kuma my Queen"

"Dan Allah ya ka gaya ma sa? Cewa ka yi Dad matata tana da ciki? Ko cewa ka yi Dad Aysherh na da ciki?"

Jawota jikin sa yai ya ce "cewa na yi Dad abubuwan da mu ke yi da wife É—ina an samu sakamako mai kyau kum...."

Toshe bakin sa ta yi ta fara dariya...

.............................

Rintsawar kirki Naomi ba ta yi ba daren ranan. Ta jima tana kallon hotunan Ogan na ta a waya. Ta sani Ogan ta ya ma ta nisa hakanan ga matar san nan da alama masifaffiya ce. Ta tuna ranan da ya fara resuming aiki tana zaune ta hangoshi yana tahowa. Tafiyar sa kaÉ—ai abun kallo ne, balle shigar sa. Ta dulmiya da kallon sa har ya zo ya buÉ—e office ya shiga ba tareda ta iya buÉ—e baki ta gaida shi ba.

Sai da ta ji ya rufe ƙofan ta yi saurin miƙewa tsaye tana sake kallon kan ta a screen ɗin wayarta. Wig ɗin da ke kanta ta sake bazawa da kyau kafin ta ƙara goga janbaki a lips ɗinta sannan ta shiga office ɗin.

"Good morning Sir" ta faÉ—a tana jiran ya amsa.
Bai yi kamar akwai mutum a wajen ba ya cigaba da latsa system É—in da ke gaban sa.

"Oga i'm Naomi Masoyi your new secretary"

"Get back to work then" ya faÉ—a ba tareda ya É—ago ya kalleta ba.
Ranan ba ta tunanin duk shige da ficen da ta ke tsakanin office É—in sa ya É—aga ido ya kalleta.
Washe gari ma cikin ƙananun skirt ɗinta ta zaƙulo ta sa ta tafi office, skirt ɗin rabin cinyar ta ya tsaya. Yadda jiya ta kasance hakan ma ta kasance yau ko sau ɗaya ba su haɗa ido ba. Tana ma sa magana bayan ya ce ta tafi ya daka ma ta tsawa, sosai ta tsorata da shi duk da ma ta samu labarin halinsa sai dai ance tunda yai rashin lafiya ya rage faɗa.

Sati ɗaya da ya fara zuwa aiki gaba ɗaya ta shiga wani hali. Soyayyar Ogan na ta ya ma ta wani mugun kamu. A kullum ta kalleshi ƙara dulmiya ta ke cikin son sa. Ta rasa ya za ta yi da wannan so da ka iya jawo ƙarshen aikinta. Wanda shi ke ciyar da su yanzu. Ta gama service ba aiki, tana manage a wani shago inda ta ke salesgirl kafin mamansu ta yi hatsari...

Mahaifin su Pastor John Masoyi ya jima da mutuwa kusan shekara shabiyar kenan. Shi mutumin Ɓilliri ne da ke jahar Gombe amma matar sa Comfort 'yar Tafawa Ɓalewa ne da ke Bauchi. Sun haɗu a wani church seminar ne da aka yi a Kaduna tun lokacin bai ma zama Pastor ba.
A BUK yai karatu, bayan ya yi service ya samu aiki a wani Kamfani daga baya kuma ya ajiye aikin bayan ya tsunduma cikin harkan Choci. Mrs Comfort 'ya'ya uku ta haifa ma sa. Elizabeth ce babba sai Naomi da ƙanin su Abel.

Kasancewa Pastor John ya mutu ya barta da yara ƙanana ya sa ta nemi aiki ta samu a wani babban Kamfani. Da albashin ta ke ciyar da yaranta ta kuma kula da ɗawainiyar su.
Elizabeth tana dawowa daga makaranta ta yi hatsari ta mutu lokacin ajinta Biyu a Unimaid.
Ya saura Naomi da Abel.

Koran ma'aikata da aka yi a Kamfanin da Mrs Comfort ke aiki ya sa ta rasa aikin ta, kafin daga baya ta samu aiki a Najeeb constructions.

Naomi typical catholic church girl ce until lokacin da ta fara Jami'a ta haɗu da Daniel wanda cikin watanni kaɗan ya rabata da duk wani shiru-shiru da rashin wayewa da ta ke yi. Sun shekara uku su na gurzan junan su wanda har cire ciki ta yi sau biyu. A shekara ta huɗu ne su ka rabu bayan ta kamashi a kan ƙawarta su na abubuwa. Tundaga Daniel ta cire soyayya a ranta amma ganin Najeeb ya sa ta faɗa wani yanayi wanda ko lokacin suna tareda Daniel ba ta ji irin sa ba. Soyayyar Najeeb ce ta ma ta babban kamu.

.............................

Ba ta jima da zama ba su ka shigo hannun su cikin na juna. Ta yi saurin miƙewa tsaye tana gaishe su. Farida ce kawai ta iya amsa ma ta shima ɗin kaman ana roƙonta.

Wassu files Naomi ta kawowa Najeeb dan yai signing, daga ɓangaren Farida ta hango shigar Naomi da kuma yadda ta yi bending tana nunawa Najeeb wani abu a takardar da ke hannun sa. Shirt ne da pencil skirt ta sa. Pencil skirt ɗin ba ƙaramin matseta yai ba, dan tafiya ma da ƙyar ta ke yi, rigan kuma ta buɗe buttons uku na sama har ana ɗan hango bra ɗin ta.

Ba ta ankara ba ta ji an damƙi gashin ta. Sai da ta jita a ƙasa sannan ta ɗaga ido tana kallon angry Farida tsaye da gashin wig a hannun ta.

"Ke karuwa ce? Ko kwartuwa ce? Wannene a ciki?" Ta faÉ—a da tsawa.

"I'm sorry Madam, I'm sorry"

"Dan uban ki miyasa za ki bar nonuwan ki a waje? Nan hotel ne? Ko aiki ki ke a hotel?"

Naomi ta birkice tana ta bada haƙuri.

"Albarkacin Mrs Comfort ki ke aiki anan, idan ba za ki kama kan ki ba, za ki yi gaba dan ba zan yi aiki da karuwa ba"

Ta cilla ma ta gashin wig É—in ta ce " ki je ki sake reviewing dresscode na wannan kamfani. The next time ki ka sake shigan banzan nan za ki gane kuren ki. Now get out"

Naomi ta É—au gashinta ta yi waje da gudu.

Najeeb na kallon su bai ce komai ba, Farida ta juyo tana huci.

Najeeb ya taso ya kama hannunta, sai da ya zaunar da ita a kan kujerar sa sannan ya ce "My Queen kin san fa yanzu ba ke É—aya ba ce. You have to take things easy"

"Take it easy? bayan ga sakatariyar ka tana girgiza ma za nonuwanta"

Najeeb ya fashe da dariya ya ce " My Queen anya ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba"

"Wallahi sai na zo. Da ba na nan fa inaga sai dai ka É—aga ido ka ga ta buÉ—e ma ka rugujajjun nonuwanta"

Najeeb mi zai yi banda dariya...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣0️⃣

Tun daga wannan rana Naomi ta risina, tsoron Farida ta ke sosai. Ko office ɗin ta ta shiga za ta ma ta wani aiki ko za ta ba ta saƙo haka za ka ga jikin ta na rawa. Farida kam tana lura da yanayin Naomin sosai dan ta ga alama kaman tana yiwa Najeeb kallon so. Sai dai ganin ta dena shigar banza da kuma rawar ƙafa idan tana office ɗin sa ya sa ta ɗan ɗaga ma ta ƙafa. Ita ba dan tausayin Mrs Comfort da ta ke yi ba da tuni ta kori Naomi...

Tana zaune a falon ƙasa su na hira da Faruƙ wanda yazo hutu sai ga Najeeb ya sauko. Yau weekend ba su je aiki ba, sai da ya mannawa matar sa kiss a kumatu kafin ya mu su sallama akan zai je ya gaida Daddy wanda ke fama da ciwon ƙafa. Farida ta tashi ta raka Najeeb zuwa wajen mota.
Tana rungume jikin sa ta ce "za mu je gida anjima ni da FaruÆ™"

"Kar ku daÉ—e plz kin san nima ba zan jima ba zan dawo"

Ta manna ma sa light kiss a lips É—in sa. Shi kuwa ya rankwafo ya kissing cikin ta yana faÉ—in "baby, Daddy zai je gaida granny dont disturb your mom"

Farida ta yi dariya...

Kamar kowani zuwanta, yau ma maganar auren Ummi ta kuma yi wa Baffa Musa, wannan karan hatta FaruÆ™ sai da ya sa baki, shima ya nuna goyon bayan sa É—ari bisa É—ari.

"Baba idan ba ka amince ba Allah zan je Toro na É—auko Abdul da Hamza su zo mu taru mu yi ta ma ka kuka har sai ka amince"

Baffa Musa yai murmushi ya ce "kin zama babbar banza kenan tunda yara na karatu za ki je ki É—auko su"

Ta ɗan shagwaɓe fiska ta ce "Baba to ai duk cikin so ne"

Tafiyar su Farida ya sa Baffa Musa dogon tunani. Amina ta sha wahala da yaranta tun bayan rasuwan mijinta na ƙarshe. Da tana tareda iyayenta ne to yanzu kuma dukkan su biyu sun rasu, ita ɗaya za ta yi rayuwarta sai dai zama da yayyenta da matan yayyen. Yaranta ma ba sa kusa. Farida na nan Kano, Faruƙ na Kaduna. Sauran biyun suna boarding school a Toro sai hutu su ke zuwa gida.
Zai taimaka ma ta wajen haɗa kan yaran idan ya aureta. Kuma hankalinta zai kwanta idan tana kusa da 'ya'yan ta. Da wannan tunani ya yanke shawaran tuntuɓar Aminan ya ji mi za ta ce.

Ranan Asabat ya je yai aski, ya zauna aka ma sa gyaran fiska. Ɗan tsoho mai shekara hamsin da takwas ya fito fes da shi. Ranan Lahdi da sassafe ya ɗau hanyar Jos. Yana tuƙi yana jin wani nishaɗi. Sabon kaya ya saka wanda cikin ɗinkin shi na sallah ne da bai sa ba. Shadda ce ash da ta sha aikin hannu mai kyau, ya ɗaura hular Zanna a kan sa wanda ya shiga da kayan...

Da ke Ummi ba ta san da zuwan sa ba, ta ma fita barkan suna chan ƙasan layin su lokacin da ya zo, Aliyu babban yayan su wanda shima ke zaune da iyalin sa a gidan ya kirata akan ga Baffan Farida ya zo. Sai da ta ji wani jim a ranta, ta dai amsa ma sa da cewa tana zuwa yanzu.

Baffa Musa kam tuni ya bayyanawa Aliyu buƙatar sa na son auren Amina. Yaya Aliyu ya nuna ba su da matsala da wannan infact su na murna da wannan haɗin. Kawai dai ita Aminan ne sai a hankali dan tun rasuwan Alhaji Kabiru ta ƙi aure fau-fau bayan kuma har yanzu da sauran ƙuruciyar ta...
Chapter 76 · 0% Book details