← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 91

Sashe 36

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro saura sati uku aure aka kawo lefen Farida kuma gaskiya Rayyan ya yi ƙoƙari sosai.
Farida ta duƙufa da gyaran jiki da shirye-shiryen yadda biki zai kasance.

Yau ana saura kwana goma sha takwas aure, Baffa Musa ya kirata.

"Wani shirme na ke ji za ki yi ranan Alhamis?"

"Baffa friends day za ayi ranan Alhamis tunda ka hana ayi kamu"

"Enemies day za ki yi ba friends day ba. Yanzu ke Farida ba za ki yiwa kan ki faÉ—a ba. Ayi miki walima salamun alaikum a kaiki É—akin ki hankali kwance, sai kin bijiro da wani shirme"

"Baffa a cikin gidan nan fa za'ayi kuma iya mata ne ka san inada jama'a"

"Ungo na ki ke da jama'an na ki"

"Mun gode Baffa"

Taɓe baki yai kawai yana bin ta da kallo. Bakin tan nan yana fata ya zaunar da ita lafiya a gidan ta, ba ya kawo fitina ba.

"Baffa ina ka amince?"

"Ya na iya uwata. Allah ya kaimu lokacin ya kuma kaÉ—e fitina"

"Baffa thank you" ta faÉ—a tana tashi da sauri...

................

Duk yadda ta ke ji gameda auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka kawai sai tsoro ya shigeta gani ta ke kamar za a kuma wani chakwakiyar kamar yadda aka yi lokacin Lukman. Ummi ta zo amma su Nanna sai Alhamis za su shigo. Ranan talata da safe ta wuce Najeeb constructions. Ta fara biya wa office ɗin Sister Munibat ta ba ta katin gayyata tareda cewa idan ba ta zo ba to sun ɓata.

"Sister Aisha kenan, ai indai ina da rai da lafiya to bikin ki da mu za ayi"

Farida ta É—an harareta " kaman da gaske, kin sayi ashobe na kuwa?"

Sister Munibat ta fara sosa kai.

" hmmm ai dama na sani, Dan Allah ki daure ki zo"

"Insha Allah sister Aisha zan zo"

Daga wajen Sister Munibat ta wuce wajen Anas. Ta jima a wajen sa, inda ya ke ba ta labarin sakataren da aka É—auka bayan ta tafi.

"Farida kwanan sa huÉ—u ya ajiye aiki, wai ba zai iya ba"

"Ai Sir Najeeb idan ba jan wuya ba ba mai iyawa da shi"

"Jan wuya kamar ki ba"

"I'in ai mun sha fama da shi"......

Lokacin da ta shiga office É—in sa yana jikin shelf ya na neman wasu files. Ta tsaya tana kallon yadda ya ke ta dibi-dibi a wajen. Da ta na nan yanzu da ita ke wannan aiki.

"Sir Najeeb mai ka ke nema?" Muryan da bai yi zatan jin sa ba ya ji a ta bayan sa. Bai san lokacin da ya sake file ɗin ya faɗo ba. Tsayawa yai yana kallonta, ta wani yi haske tana sheƙi, ga wani ƙanshi mai daɗi da jikinta ke fitarwa.
Tsugunnawa ta yi ta ɗauka file ɗin sannan ta miƙa ma sa. "Ga shi na ma ka aikin ƙarshe"
Bai amsa file É—in ba sai ma juyawa da yai ya je ya zauna a kujerar sa.

"Iko sai Lillahi, daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi. Sir Najeeb ba fa aiki na zo ba da za ka min jan ajin da ka saba"

"Oh really"

"Gashi, dama IV na kawo ma ka" ta yi saurin ajiye file É—in tareda ciro IV ta ajiye ma sa.

"Dan Allah a daure a zo. Duk da ma dai i'm just a secretary"

Ta É—an yi dariya ta ce " was just a secretary"

"Congratulations Miss Salihu"

"Thank you Sir Najeeb"

Ya ɗan kurɓi coffee da ke gaban sa sannan ya ci gaba da latsa laptop.

"Sir Najeeb ina da magana. Dan Allah ka ɗan rage halin kan nan. Ka ga ba kowa bane zai iya jurewa. Ni ma da ƙyar na sha a wajen ka. Allah, watarana idan na koma gida daga office har ƙaramin zazzaɓi na ke saboda stress da zafin kai. Kai ba a maka gwanin ta sannan..."

"Out"

"Ka ga irin halin na ka ko"

"Miss Salihu get out"

Ta yi shiru tana kallon sa sai da ta ga zai sake É—aukan mug É—in coffee É—in sannan ta yi wuff ta É—auke.
Ta kai baki da nufin ta kurɓe duka lokaci guda sai ta ji shi da zafi sosai. Ta ɗan kurɓi kaɗan ta sake kurɓa sannan ta ajiye ma sa.
Dariya ta yi saboda yadda ta ga ya zaro ido.

"Sir Najeeb tsokalar ƙarshe ne fa. Na tafi"

Harta juya sai kuma ta juyo ta ce "Sir Najeeb a yafe mu"...
Sai da ta rufe ƙofa ya ce "devil in a dress" ya jawo wani dogon envelop ya buɗe, hotuna ne guda uku a ciki " happy never marriage Miss Salihu" ya faɗa a fili.

(🙄Sir Najeeb ya dai?)

.......................

Farida na komawa gida ta tarar da Maijiddah ta zo.

"Kai-kai Jiddah mi ki ke ci haka? Kin ganki kuwa"

"Kai Anty Farida"

"Zo zo mu shiga É—aki ki gaya min sirrin"

Sai da su ka zauna ta ce " Jidddah ciki gareki, wannan ƙiban da walakin"

Maijiddah ta rufe ido tana murmushi.

"Masha Allah, Allah ya raba lafiya. Ina kishiyar ki? Har yanzu tana Abuja?"

"E, amma yanzu sau biyu ta ke zuwa a wata"

" 'yar kusun'wa, za ta ma ajiye aikin ta dawo gidan ta, ko kuma ta ji ta a silencer dan mune ma su gidan yanzu"

"Na gode Anty. Kayan da ki ka bani sun min rana"

"Zauna a wajen, ai mazan yanzu sai da shigar bariki. Nima na je Jos na kwaso nawa suna nan jingim"....

Biki na matsowa jikin Farida na ƙara sanyi kullun ta yi bacci sai ta yi mafarkin an fasa aurenta. Abin ya dameta ta gayawa Ummi, Ummi ta ce ta dinga addu'a. Itama ɗin Ummin Allah-Allah ta ke ayi bikin lafiya ba tareda wata matsala ba.
Ranan Alhamis aka je aka yiwa Farida jere a gidan Rayyan. Rayyan ya gina 3-bedroom flat mai kyau. Baffa yai ƙoƙari dan ya kashe kuɗi sosai wajen sayen ma ta kaya, 'yan uwan Ummi ma sun yi ƙoƙari gaskiya...

........... ..........

Ya na zuwa ƙofar gidan ya sa yaro ya kira ma sa maigidan. Da yaron ya fito ya ce yana zuwa...

Musabaha su ka yi da dattijon sannan su ka gaisa.

"Yi haƙuri ban ganeka ba"

Ya miƙa masa envelop sannan ya ce " ɗan ka zai yi aure ranan Asabat ɗin nan ko?"

"Insha Allahu"

"Matar da zai aura ba matar aure ba ce"

"Ban gane ba"

"Ka dubi cikin envelop É—in nan za ka ga zahiri" daga haka ya juya ya tafi.

.....................

Anyi friends day lafiya kuma ba laifi ƙawayen ta na Jos sun zozzo, anci an sha kuma an girgije.

Ƙarfe goma sha ɗaya na dare lokacin ba ta fi 'yan mituna kaɗan da kwantawa ba kiran Rayyan ya tashe ta. Tana ɗauka ya ce ta fito waje yana ƙofan gidan su.

"My Ray lafiya ka zo da daddaren nan?"

"Ki fito Farida akwai saƙon da zan ba ki ne"

Maganar saƙo da ya ce sai ta ji zuciyar ta ya buga. Ta tashi ta sa hijabi ta fito.
Akwai wa su baƙi da ke kwance a barandar tsakar gidan su na hira, da ke ba su jima da tattara tsakar gidan ba.

"Amarya ina zuwa haka?"

"Ƙofar gida zan je an kawo min saƙo"

"Samarin zamani dai, angon ne ya ka sa hakuri haka"

Ita dai ba ta sauraresu ba ta fita.

Wajen motar sa ta je ya buÉ—e ta shiga.

"My Ray minene, hankalina ya mugun tashi fa"

Da ke dare ne ba iya kallon fiskarsa ta yi sosai ba balle ta ga yanayin sa.

"Farida ashe za ki iya cin amana ta"

Dum ta ji ƙirjin ta ya yi.

"Wallahi ban É—auka za ki min haka ba"

"Na shiga uku ni Farida ba dai za a kuma ba. Rayyan mi na yi?"

"Ashe soyayya ku ke da Ogan ki. Ashe duk yadda ki ke zagin sa a gabana iya fatar baki ta tsaya"

"Rayyan dan Allah kar ka sa zuciyata ta buga yanzu. Idan ma wasa ka ke ka dena please "

"Da kan sa ya je gida ya ce wa Baba ke karuwarsa ce"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun, Lahaula wala ƙuwwata illa billah. Sir Najeeb ne ya faɗi hakan?"

Miƙa ma ta wayarsa yai ya ce ga hotunan da ya kawo. Ina tunanin ma waɗannan lokacin da ku ka je Lagos tarene ku ka yi holewarku achan.
Ta amshi wayar ta fara kallon hotunan. Hoton farko tana zaune kan cinyar Najeeb ta sa hannayen ta a kafaÉ—un sa tana murmushi, É—aya kuma suna tsaye ya rungumeta ta baya, lips É—in sa a daidai wuyan ta. Ta swipping na gaba wanda tana kallo hawaye na É—iga a jikin wayar. Suna rungume da juna bakinsu a haÉ—e kamar suna kissing.

"Ba ni bane, wallahi ba ni bane. Wannan sharri ne. Rayyan ka yarda da ni"

"Dama na zo na faÉ—a miki ne da kaina kafin gobe a zo gida a faÉ—a. Na fasa auren ki Farida, ina son ki amma ba zan iya auren ki ba. Najeeb yana da kyau yana da kuÉ—i, ko bayan mun yi aure idan ya neme ki za ki amince da shi. Ba zan iya aure da zargi a ciki ba"

Bakin ta ne ya fara rawa, tana so ta yi magana amma ko me ya taho zai fito sai ya maƙale a wuyan ta. *"Na fasa auren ki Farida"* shine maganar da ke ta maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.

"Gobe za su zo su karɓi sadaki da lefe, sauran abubuwan na yafe. Na gode da Allah ya tona asirin ki kafin ma ayi auren, dama Umma ta sha faɗamin ba ta yarda da ke ba dan 'yan Jos ɗin nan yawancin ku 'yan iska ne"...

Ba ta san ya akayi ta buɗe ƙofa ba, ba ta san kuma ya akayi ta shiga gida ba. Zuwa ta yi ta zauna a bakin gado hawayen da ta ke yi ma ya tsaya. So take ta gane mafarki ta ke yi ko gaske ne. Bacci kam ranan ba bu shi a idon Farida.
Chapter 36 · 0% Book details