Sashe 3
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdul na da shekara biyu Alhaji KB ya rasu. Mutuwar da ta gigita Amina da Hajiya Aina'u. Lafiya-lafiya ya tafi Zamfara kawai sai yayan sa Ubaidu ya kira wai Kabiru ya rasu zazzaɓi ya sashi a gaba da dare kafin safiya ya cika.
Amina ba ta shiga tashin hankali ba sai da kwana ishirin kacal da rasuwan Alhaji KB 'yan uwan sa su ka zo su ka koreta a gidan sa. Ƙarshe a gidan su ta ƙare takaba. Kafin wata uku da rasuwar sa su ka saida makarantar sa da gidan sa da mafi yawancin kadarorin sa. Hajiya Aina'u da Amina sun yi ƙoƙarin shigar da ƙara Kotu sai dai tun farko da su ka yi yunkurin hakan aka rufe bakin su. Haka nan Amina wadda 'ya'yanta ke kira da Ummi ta koma gidan jiya sai dai wannan karan tana da ilimi daidai gwargwado da kuma wayewa. Wata makarantar ta nema aiki kuma ta samu da wannan ta ke yin hidimar yaranta da shi. Tsohon mijinta Ibrahim ya nemi ta yi kome saboda yanzu ya rabu da Kubura kuma Alhamdullillah matar sa Hafsatu tanada kirki. Ummi ta ƙi tace ita da aure har abada. Ba yadda Babanta bai yi ba amma ta ƙi ta ce aure huɗu da tayi a baya sun isheta. Yaranta uku na gabanta Farida, Hamza da AbdulMalik. Shi ma Faruƙ ya kan zo hutu wajen Ummin sa lokaci zuwa lokaci har lokacin a Kaduna ya ke. Hajiya Aina'u na ƙoƙarin taimakawa Amina da ɗawainiyar yara daidai gwargwado sai dai fa har yau 'yan uwan KB ba su waiwayeta ba balle su nemi taimakawa yaran marigayi. Gado da ya bari kuma babu batunsa dan tuni sunyi wasan kura da dukiyar sa.
Aisha Farida Salihu yarinya da ta taso da ƙiriniya ga surutu. Ba dai ka faɗa ta yi shiru ba. Kwata-kwata ba ta da tsoro, tana son umminta sosai gashi ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba, idan ka ga suna hira tamkar wa su ƙawaye. Sau tari ma akan ɗauka ya da ƙanwa ne su. Tunda su ka koma gidan su Ummi, Farida ta dena zaman banza ganin dai yanzu ba da bane. Ta koyi kitso da lalle tana yi, ga saida kayan ƙwalama da ta ke yi a school. A haka har ta ƙare secondary school ɗin ta. Jamb ɗin ta na farko ba ta ci ba dan haka ta fara zuwa koyon computer a shagon ƙanin Umminta Ahmad. Ta koyi abubuwa da dama dan Alhamdulillah Allah ya bata ƙwaƙwalwa. Da ta sake Jamb ta tafi Federal polytechnic da ke Bauchi saboda UJ da ba ta samu ba. Business Administration ta karanta a ND da ta zo HND ta koma Marketing. Aisha Farida 'yar kasuwa ce tuƙuru. Dan tana makaranta ba ta zauna haka ba ita ce saida turare, takalma da jakukkuna. Ga shi duk hutu idan ta je Jos za ta saro gwanjuna ma su kyau ta zo tana sayarwa students. Wannan ya sa 'yan ajin su ke kiranta Aisha mai gwanjo.
Yanzu shekarar ta ashirin da uku, tana service a Yola. Tun a camp su ka haɗu da Yasir Sa'ad ɗa ga senator Sa'ad Babagana. A UK Yasir yai karatu. Da farko su na fita daga camp zai relocating zuwa Abuja Inda iyayen sa su ke sai dai soyayyar Farida da ya shigeshi farat ɗaya ya sa ya fasa. Hakan ya sa a Inda aka turata primary assignment ɗin ta shi ma ya je. Duk iya watannin da su ka yi tare Farida ba ta bashi dama ba. Tausayin sa ta ke ji ta girme shi da shekara ɗaya ita kuma tana ganin tsayawa soyayya da shi ɓata lokaci ne. Ga uwa uba kiran da Hajiyar sa ta mata akan ko da wasa kar ta amince da soyayyar Yasir saboda karatu zai yi hakanan akwai alƙawarin aure tsakanin sa da wata. Ita dai Farida ba dan tsoro ta ke baya-baya da shi ba ko kuma ta ƙi son sa ba sai dai bazata bawa kanta ciwon kai a kan Yasir ba. "Yaushe ma ka girma?" Abinda ta ke yawan gaya ma sa kenan.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0ï¸âƒ£0ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
Da dare baƙuwar number ya kirata, da ta ɗauka sai ga muryan Rayyan.
"ÆŠankwassi! a ina ka samu number ta?"
"My Farida kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faÉ—i tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka ba. A hankali a hankali Rayyan ya cigaba da kiran Farida, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cikin sati uku sai da ya san yadda ya ja hankalin Farida har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira.
Ranan da su ka yi passing out ɗin su sai ga shi a Yola. Ta ji mamaki hakanan kuma ya ɗan samu matsayi a zuciyarta. Saboda Yasir ya haƙura da ita ya sa ta introducing Rayyan a matsayin saurayin ta. Yasir kamar ya haɗiyi ran sa saboda baƙin ciki haka su ka rabu da shi baran- baran. Ko sallama babu.
Rayyan Abdullahi ɗan Kano ne kuma ma'aikaci a Zenith bank. Ya je Bauchi ta'aziyar 'yar yayarsa da ta rasu su ka haɗu da Farida. Sosai ya ke jin Farida a ransa, tsiwarta da masifarta yana burgeshi matuƙa. Ya ɗau ɗamaran koyawa Farida son sa musamman da ya gane ba ta da wani tsayayyen saurayi. To ina za ta yi saurayi bayan masifarta kaɗai ya isa ya sa samarin su dinga gudun ta.
..................................
Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye É—akin sa ya wuce dan ya san Daddy ba ya nan balle ya je ya gaida shi. Ya na shiga ya danna SHS zuwa Main kitchen "lemon tea in 10minutes" ya faÉ—i tareda zama ya fara cire socks na shi daga nan ya cire gaba É—aya kayan jikin sa sannan ya shiga toilet.
Adama ta zo haurawa ɗauke da tea ɗin Najeeb ta haɗu da Afrah da ke shirin haurawa saman. Ta duƙar da kai ta gaisheta, Afrah ta amsa a gatsine.
"A Ya Najeeb za ki kai wa?"
Adama ta amsa da "eh"
"Kawo zan kai masa" ta ƙarɓi tray ɗin daga hannun Adaman.
Ta cigaba da hawa stairs ɗin tana tafiya ƙarar takalminta na ba da sautin ƙas- ƙas- ƙas...
Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a É—aki na" Ya daka ma ta tsawa
Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.
Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Joseph sabon sakatarin sa ya turo ma sa. Yana dubawa yana sipping tea ɗin sa a hankali. Ba laifi Joseph yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sati biyu da Joseph ɗin ya fara ma sa aiki kenan.
..........................
A hankali soyayyar Rayyan da Aisha Farida ta fara nisa, domin har ya je Jos ya gaida Ummi...
"Farida ba magana na ke mi ki ba"
"Ummi dan Allah ki haƙura da wannan zancen, zan dai dinga zuwa mu su akai-akai yanzu tunda na gama bautar ƙasa"
"Kin sani sarai har yau Alhaji Musa ni yake É—aurawa laifi akan na raba ki da dangin Baban ki. Sun fi ni iko da ke Farida"
"Ni kan Ummi ki yi haƙuri, ba zan je ba, albarkacin Inna na ke zuwa mu su dama, kuma ta rasu shikenan"
"Ki yi yadda ki ke so Farida" Ummi ta faÉ—i tareda barin É—akin.
Ita ta rasa dalilin da zai sa sai yanzu Baffa Musa zai takura wai ta koma wajen sa da zama. Ita yaushe ma za ta juri zafin Kano balle uwa uba rashin kunyar yaran sa. Dama dalilin Inna ke kaita Kano kuma tunda ba ta nan kowa ya riƙe kan sa. Da wannan tunani ta janyo purse ɗin ta tana irga kuɗin da ke ciki a karo na biyar kenan tun safiyar yau.
Sosai Ummi ta nuna ɓacin ranta akan ƙin zuwa Kano da ta yi, ko gaisuwarta yau da safe ba ta amsa ba.
"Nanna dan Allah ki cewa Ummi ta bar ni na yi zamana anan. Wallahi ba jin daÉ—in zaman Kano na ke yi ba"
Nanna da ke shan kunu da ƙosai ta ce " kin dai san da daɗewa Ummin ki tai alƙawarin za ki koma Kano da zaran kin gama makarantar ki. Alhaji Musa da kan shi ya kirata jiya ya ke cewa ya ji shiru. Ke idan ba ke bama ba saurayin ki ɗan Kano bane, idan ki ka je chan sai ku saita kan ku, kinga ba sai an sha wahala ba daga nan sai dai mu je bikin ki chan Kanon"
Ta turo baki tana faÉ—in "Allah dama kun gaji dani. Ni dai ba zan je Kano ba"
"Ah to, sai ki kira Baffan na ki ki gaya ma sa ai"
Farida ta zumbura ba ki ta fice a É—akin....
Cikin kwana biyar ta gama shirin ta tsaf, ba wai tana son zuwa Kano bane, sai dai tunda abinda Ummi ke so kenan dole ta yi shi. Ranan asabat ta wuce Kanon tsabar haushi ko kiran Baffa Musan ba ta yi ba balle ta sanar ma sa da zuwan ta.
A ƙofar gida ta haɗu da su Kamal yaran Baffan su na wasa, da gudu su ka zo su ka tareta sannan su ka tayata ɗaukan kayan ta.